Hakade yayi ta ɗaura ta keken ɓera,amma fa duk da haka baji a zuciyar cewan zata hakura da haɗa Ahmad da ɗiyarta Fauza aure ba,wannan burin da ɗeɗɗen burine dake dankare cikin ranta.

****
Da ɗaya hannun yana riƙe da ƙugunta ɗaya kuma yana shafan fuskanta a hankali ya sauƙe babban yatsan sa yana zagaye tattausan lip's ɗinta dashi,lumsh idonta tayi sai hawaye dake sauka saman kyakkyawar fuskanta masu ɗumi yana sauka saman hannun sa.

Lumshe idon sa yayi yana kai bakin sa a hankali kunnen ta lip ɗinsa masu taushi ya gogi fatan kunneta haɗe da numfashin sa mai ɗumi daya sata rintse idonta da karfi"kina bukata na baki ko in karɓa da kaina?tsigan da yayi maganan dashi kaman bashi ba,batasan sanda ta bude idon tarrr ,bata sauke kallon ta ko ina ba sai a saman fuskan sa,kallon cikin idon sa tayi abunda ta gani ɗin yasa tayi sauri tana ɗauke idon ta daga barin kallon sa,sake kai bakin sa yayi saitin kunnenta yasake cewa"yanzu zaki bani ko sai anjima kode ni zankarɓi abata anjima?

Jikin tane ya ɗauki rawa karkarkar ai batasan sanda wani karfine yazo mata ba,bata kuma san sanda ta ture shi tayi gaba da ɗan gudun ta ba,saide ba inda taje ya cabkota yana sake haɗe ta da jikin sa yayi mata kyakkyawan masauki saman faffaɗan kirjinsa ya sake kai bakin sa yayi kunneta ya furta"saurin me kike ai basai ta kaimu ga zuwa can ɗin ba?ai ko anan kika bani zankaɓa,amaryata ta wucin gadi ya kare maganan cikin zolaya.

Kicin kicin din kwatan kanta ta fara yaƙi bata daman haka saima wasu abubuwa da yafara mata wanda taji kaman ƙafafunta baxasu iya ɗaukan ta ba,jin sabon yanayi data sinci kanta ciki shi kansa jinsa yake wani irin kasancewa dukkan su su biyun daga shidin har ita sabin shigane.

"turesa tayi cikin kuka ta xame ta zauna a waje tasaki wani irin marayan kuka tasake,jikinta yana wani irin tsuma,komawa yayi ya zauna saman kugera yana daidaita nutsuwar sa,saida yaji sa ya koma daidai ya bude bakin sa ahankali yana cewa"ashe dama ke matsoraciya ce haka ban sani ba,tsiwa fal cikin ki amma ɗan wannan abun da bekai ya kawo ba,kin wani zube kina ɓarnatarmun da hawayenki masu tsada amma dakin adanasu zasuyi miki amfani zuwa ranan da zan karɓa idan kin bani ko baki bani ba idan na buƙata zan karɓane.

Jin irin maganganu dake fita daga bakin sa,wanda tayi imanin sun girmi tunanin ta dama shekarunta baki ɗaya ai batasan sanda kukan ta yatsaya cak ba,tana murguɗa masa baki ta miƙe ta faɗa ɗakin da gudu tana maida ƙofan tana rufewa harda murza key,murmushin gefen baki yayi yana cewa lalle akwai aiki jaa a gabana gata da tsuwa da tsoro hmmm.

Yana nan zaune sai ga kiran Faisal saida yayi koƙari dan ganin ya daidaita yanayin sa kafin ya ɗauki wayan,yanayin yanda yayi salla kaɗai saida yasa Faisal tutsurewa da dariya yana cewa"me yasamu muryanka?

Saida ya shaƙa sannan  yafesar yana sake kame muryar sa dabata fitowa da kyau yace"idan dama ka kirane dan kamun wannan tambayar ne ka ajiye waya dan ina da abunyi,ya faɗa murya a shaƙe.

Ai Faisal besan sanda yafashe da wani irin dariya ba haryana riƙe cikin sa"ƙwafa Ahmad yayi yana kashe wayan yayi wani dogon tsaki mtssss yanajin haushin kansa daya kasa riƙe kansa kan ƙaramar yarinya karfa ta raina masa hankali gashi yanzu har takai Faisal yanason yimasa sharri.

Yana nan zaune wayan tasoma burarin neman agaji,kaman baze dauka ba ganin mai kiran nasa haka ya daure ya dauka dan yasan kiran dole tana da mahimmanci.

"Idan kasan rashin M zakamun pls Officer ka kashe wayan,abunda yace dashi kenan sanda ya ɗaga kiran"ok ok yace yana danne dariya dake zuwar masa dan yasan muddin yabari yakashe masa wayan karo na biyu ba lallene yakuma samun Ahmad ɗin  yauɗin ba.

Ka zauna cikin shiri karfe biyu dare Alhaji na Allah xe fita kayi kokarin dan gani kabisa a baya"ok kawai yace a takaice hira suka taɓa kaɗan nan yake sanar da Faisal ɗin maganan su Mami dama shi Alhaji na Allah dan ganin Aisha ta koma ɓangaren su ɗakin masu aikin gidan da zama.

Shiru Faisal yayi na minti biyu sai yace"ina ga kabarta ta riƙa zuwa tana tay masu aikin gida da wasu aikace aikace hakan kuma ze taimaka mana wajen samun wani evidence da zamu riƙa sannan kaima inason kayi kokari dan ganin an samu wani abun ta gunka kafin zaman kotu.

"In sha Allah Faisal akai nake ina cikin damuwa sosai wallahi dan nakasa samun nutsuwa cikin zuciya ta,tunda nabaro gida banida nutsuwa zuci data ruhi,yanda yayi maganan akarye saida ya karyama Faisal zuciya kwantar masa da hankali ya shiga yi yana bashi ƙwarin gwiwa saida ya tabbata ya dan rage damuwa sannan sukai sallama yana kashe wayan sa.

"Alhaji an samu matsala,miƙewa tsaye yayi yana kallon wanda yake tsaye a gaban sa yace"idon mikiya kasan bana shiri da kalmar matsala bana kuma son jin sunan ta meyasa kake kiramun ita anan,bayan kasan bani da alaqa ko jituwa da wannan sunan.

Yafaɗa a fusace cike da fushin da yasaka ɓoyeshi  hatta a muryar shi"Allah ya taimaki Oga tun safe yaranmu suna airport ɗin nan amma har yanzu nadake magana dakai sunce basuga koda mai kama da Gazali ba balle akaiga Zulai.

"Kai ina karyane haka sam baze faruba yafaɗa da karaji yanda yayi tsawa har saida idon mikiya yaɗan razara danjin yanda yayi maganan cike da ƙaraji.


ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now