Ya kare maganan dan shi kaɗai yasan abunda yakeji a cikin ransa baya kuma so Ahmad din yagane shine GAGARA BADAU da wuri koda ze gano shidin ne bayaso ya gano dawuri yafison sai zuwa wani lokacin daya cimma burukan sa akansu.

Wanka Ahmad yayi yafito ya haɗa coffee yana kurɓa a hankali hankali ya dubi Mansur yace"Man kunsami wani abu kuwa?

"Eh ranka ya daɗe nan yaciro masa bayanan komai dayake bukata a computer wani malalacin murmushi yana kubce masa sannan bayanan komai na wayoyin su yafito masa dasu,zama yayi yana dubawa ɗaya bayan ɗaya sannan ya maida duban sa kan Mansur ɗin yace"inaso ayimun traking wannan lamba dayafi kowa kiransu da alama wannan shine wanda muke nema ko kuma ze kaimu ga wanda muke neman.

"Hakane Sir
Amma ma mallakin wayan alamba yanuna kaman a Kano yake.

"What Mansur kana nufin mai ita yana Kano ohh ya Allah yace yana murza goshin sa sai can yace bani lambar na turama Faisal ya bincika mana waye mamallakin wannan lamba.

"Da ok Sir ya amsa masa yana tura masa lamban.

Minti ƙalilan da tura sakon Faisal yakira wayan sa bayan sun gaisa yake ce masa"Ahmad kwana biyu na jika shiru bawani labari kasan kuma jibine zaman kotu gashi ba abunda muka riƙa wajen kare kanmu.

Saida ya fesar da iska mai dumi ta bakin sa sannan yace"Faisal ina sane da komai wallahi tunda na baro gida hankalina ba aƙwance yake ba,yanzu haka muna Lagos munyi nasaran kame mutum biyu miji da mace suna hannun mu lamba da natura maka yanzu nakeson kayi bincike akansa da alamu sun nuna akwai alaƙa mai karfi tsakanin su da mai lambar dan a rana mai wannan lambar tana kiransu aƙalla sau kusan goma zuwa sha a rana sannan namijin yanzu haka yana ɗauke da cocaine a cikin cikin sa suna shirin barin ƙasar ne a yau da zuwa saudiyya.katse shi yayi yana cewa.
"Ahmad ina kabar Aisha?

"Tana can gidan Alhaji na Allah ya bashi amsa kai tsaye.

"What Ahmad kana da hankali kuwa kabar ƴar mutane a can kai kuma kana wani jahan.

"Me aciki Faisal ai ba abun damuwa bane ya amsa sashi cike da rashin damuwa.

"No no no Ahmad wannan bayi bane idan ma zeyu yauɗin nan kanemi girji komai dare ka koma in yaso Yaran ka su suƙarasa aikin.

"Faisal wai duk karuɗe daga cewa ma Aisha na gida nasan in sha Allah she's safe tunda Mami na kusa da ita bani da haufi.

"Mami Faisal ya maimaita sunan Mamin kaman bayaso wace Mamin kanen?

"Wai Faisal me hakane?
Banason wulakaci wace Mami kuwa in banda Mami da kasani ba,ina kafi kowa sanin wace ita gareni.

"Haka kace Ahmad to bara nama gwari gwari ta malam ba haushe yace dalla dalla to wallahi karka bari wani abu yasami ƴar mutane kai idan kasan bazaka iya kula da ita ba me naka na ɗaukan ta ka tafi da ita,sai kuma ya sassauta murya yakira shi da Ahmad a halin da muke ciki karka sakan kance akan mutum ko dakuwa ya kuke da shi balle gidan da kuke zaunan dan shima kansa Na Allahn abun zargine a guna,ka koma gida yau komai dare kanemi tiket aiki da ƙwaƙwalwa zamuyi yafi aiki da jiki.

Sannan ka ja Aisha ajiki zamu samu abunda mu bamu isa samun sa ko kaiwa ga sanin sa ba,a gunta ba,ita yarinya ce mai hikima gata da basira tanada maida hankali kan abu da saurin karantar halin mutane da take zaune dasu cikin ƙankanin lokaci,saide matsalan Aisha guda ne?

"Kaman ya kenan?
"Hmm bata barin ta kwana wannan dalilin yasa nasa nace ma kaje gidan,zuwan naka ze kawar da duk wani zargi a kan ka.

"Zargi kuma Faisal waye ze zargeni nifa kana sake dulmiya zuciyata cikin tunani.

"Kaifa jami'ine mai aiki da fikira wai kai komai saina faɗama makane tukunna zaka farga.

Shiru Ahmad yayi yana nazarin kalaman Faisal din sallama sukai yana kashe wayan,yakai duban sa ga Mansur daya duƙufa aiki a computer dake gabansa yace"Mansur kaima Bk magana su bincikamun ko za samu flight din Abuja ya yanka mun tiket zan koma yau.

"Ok Sir amma koda wata matsala ne?

"Yanzun de babu saide tana neman kunno kai,yabashi amsa.

"Subuhanallahi Allah de yarufa asirin wajen aukuwan matsala"Amin yafaɗa a hankali.

Ka kula da abunda ya kawomu zan bar komai a hannun dan na yarda dakai sannan wannan mutumin inaso duk abunda zakayi kuyi ƙoƙarin ganin dan kunyi videos komai dan musamu muriƙe shedan komai a hannu"ok sir.

Karfe takwas na dare ya isa garin abuja motan sa daya bari a airport ya hau be zame ko'ina ba sai gidan Alhaji na Allah dake haɗaɗɗen anguwar masu hannu da shuni horn yayi bakin tangamamen get din gidan mai gadi ya bude masa bayan yaleƙa ya ganshi wuce sa yayi yana masa barka da isowa.

Parkin motan sa yayi a parkin space kai tsaye babban falon masu gidan yanufa,bakin sa ɗaukin da sallama Alhaji na Allah da Mami ne kawai a falon suna zaune da alama tattaunawa suke,murmushi ƙawace fuskan Alhaji yake amsa masa sallamar zama yayi a ƙasan yana gaishe shi dan kallon sa yayi yana cewa"daga ina haka  Ahmad?

Cike da kamewar nan tasa yace"wallahi Daddy daga wani tattaunawa da wasu baƙi daya dauke mu har wannan lokacin.

"Kode ka koma aikin ka na daa ne?

"Wanne Alhaji ya tamvaye shi a mamakance ai ni yanzu ta harka da nake ya faɗa yana miƙawa Mami wayan sa yace kinga sabbin order ne Mami cikin wannan satin zasu shigo nan 9ja ko zaki zama mace ta farko da zata fara saka new brand ɗin mu.

Dariya Mami tayi tana karɓan wayan ipad ɗin nasa tana kallon hoton kayan tace gaskiya sunyi masha Allah katuro mun ta whatapp ɗina saina zaɓa mana dukkan mu har da shi kansa Mai gidan,dariya sukai amma banda Ahmad daya murmusa kawai.

"Ita wannan yarinyar wai me sana'ar ta?

Ina nufin wani aiki takeyi da kai?

"Oh Aisha kake nufi ko wa?

"Eh ita fa Alhaji ya amsa masa cike da ƙwarin gwiwa.

"Hmm ita ɗin gwanace wajen ɗinki dan tana ɗaya daga cikin ma aikatana danake alfahari dasu yabasu amsa a takaice.

"Inde aikine kawai ya haɗaka da ita maize hana ta komo nan wajen namu da zama a ɓangaren masu aiki.

Amsa mata shima Alhaji yayi yana cewa hakane fa dan haɗuwar namiji da mace musamman a wannan shekara naku hatsarine ta koma nan ɗin kawai da zama zefi....

zaune take a falo ta rabƙa uban tagumi tana tuna hiransu da Sajida na ɗazu haka kawai wani abun yake sata taji kunya wani tayi murmyshi wanu kuma yasata dariya.

Ahaka yashigo ya sameta tana kallon sa tsaye daga bakin ƙofar shigowa falo yana rungume da hannuwansa a ƙirji ya kafeta da idanun sa masu sataka kasala.

"A haka ake tarɓan miji a garin ku?Ta tsinkayi muryan sa,ƙasa tayi da idon ta daga barin kallon sa tana kumbura fuskarta"ba kya kyau idan kikayi fushin nan yasake cewa haka kawai ya tsinci kansa da farin cikin ganin ta gabansa.

ALLAH YASA MUDACE.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now