Da kalamai  Yusrah tayi ta tausarta ta samu dan kwantar da hankalinta,bayan sallama ne shahida ta kirata don ita ta ke gun bikin Bata ganta ba Anty Nafisa ma ta fad'a Bata san meya hana Ummin zuwa ba ,karya tayi musu ta ce Mukhtar ne bai da lafiya sosai sabida haka ya sa bazata zo ba.

*****

   Sama sama take Jin hirarsu suna dariya ,bude ido ta tayi ta dauki wayarta ta ga 10:30am tashi tayi tana mamaki baccin da tayi dayawa haka ,muryar Maman Suhaila ta jiyo don yanzu har muryar makociyar Zainab din ta sheda sabida yawan zuwanta gidan.

     Ringing din wayarta ta ji koda ta duba ta ga Ya Abdulbasit ne ,bayan ta amsa suka gaisa yace.

"Ba kya gida ne muna kofar gidanki da Hafsat ko munyi sammako mu koma??"

  Cikeda farinciki da mamaki ta hau murmushi tana magana "Haba Yaya gani gani wlh ina nan".

  Mayafi ta shiga d'aki ta dakko ta bude kofar ta fito kasan.

  "Saura 'kiris ya rage wlh kofar gidannan sai ya gagareta bazata iya takowa ba".

  Motsin da suka ji yasa suka shiru kamar ruwa ya shanye su,wucewa dafe kirji Zainab tayi "Na shiga uku ta ji mu".

  Maman Suhaila ta girgiza Kai "Ba ta ji ba ,ka da ki karaya man ba ta ji komai ba na tabbatar da bazata fita haka ba a nutse".

"Allah haka kike gani?".

  "Kar fa ki damu ance maki bata ji ba shiyasa kawai dole ki je karasa trial dinki na karshe walhi har yanzu naga kin kasa yarda da kanki".Maman Suhaila ta fad'a.

  Kai ta jinjina Zainab har lokacin hankalinta bai kwanta ba ,  muryar su Hafsat da Abdulbasit din suka ji suna shigowa suka bisu da kallo take Zainab ta sauya fuska ta yafa murmushi itama Maman Suhaila ta hau murmushi suka gaisa dasu Ummin tana mamaki yadda suka canja fuska kamar wani mutunci ake.

   Abincin da bai ci ba ya Mukhtar ta kawo musu ta ajje musu yam balls ne sai yar sauce din kayan ciki ta kawo musu.

  "Anty Hafsat kun zo Kano shine ba labari? Sai yau da zaku koma haba ya Abdulbasit".

  "Ke fa ba dadewa mukai ba shekaranjiya muka zo ni ban ma zauna ba akwai aikin da na zo Yi ne fa ,dole Kuma a yau din zamu koma shiyasa kin ma samu munzo kafin mu tafi don flight din rana ne damu".

  "Anty Hafsat ai da kin zauna ko week ne a Kano uhm"

"Yayanki ya ki".

"Haba ya ya ?"
 
  "Haka ma zaki ce don Kinga

  Yarinyarsa Ameera mai sunan Mummy ta dauka a cinyarta tana ganin yadda yarinyar ta girma har cikin nata ta ji shawara samun nata ta kawara da tunanin tana mata wasa dukda maganganun su Zainab yaki tafiya a kanta.

Mamn Suhaila kafin fitowarsu Abdulbasit ta tafi don ba dadewa sukai ba yam ball en ma kadan suka ci  bayan sunyi yar fira suka tashi har bakin gate ta raka su sukai sallama ,a envelope ya ciro envelope ya kika ma Ummin lokacin Hafsat ta shiga mota .

"Yaya harda dawainiya".

Harara ya Kai mata "Collect jorr wai ke irin matar oga dinnan kike forming ko".

Kai ta girgiza da guntun murmushi tana tunanin if only yasan battle din da take ciki a gidan auren nata .

"Kya gaida Mukhtar din idan ya dawo".

"Zai ji in sha Allah Yaya Allah tsare nagode sosai Yaya Allah Kara budi".

  Ta fad'a tana ma Ameera waving bye ya shiga motar driver ya ja su ta komo cikin,nan ta ga kudin ciki 30k ne sabbin yan 1000.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 16 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now