Page 8

35 4 1
                                    

YADDA NA KE SO🌺

  BY DIJENSY


PAGE 8

   Duk wani abunda zasu bukata ya riga da ya shirya musu a kan table din ,gudun kar ma a samu matsala ,ya jera komai ,Ummi na d'aki ta baje ice cream dinta ko a jikinta ma.Shigowarsu ta jiyo suna gaisheshi ta ta'be baki jin muryoyinsu ya tabbatar mata da suna da yawa yaran.

  Kamar yadda tayi tsammanin ta ga ya shigo d'akin "Ummi ,bakinmu sun zo".

  Dago ido tayi ta kallesa "Gani nan zuwa".

  Sai da ta 'kare ice cream dinta Shan yanga ta dinga Yi , sannan ta fita more than 30min shukra suna ta baza ido su ga matar Yayan nasu sai can.

   Fuska ba yabo  ba fallasa ta fito tana 'kare musu kallo one by one 'Tabdijan ji su dan Allah kamar sun zo gidan biki' A ranta ta fad'a.

  Gaisheta suka yi a ladafce tana amsawa kamar an tursasata ,ba ta tsaya wani tambayarsu mutan gida ba ta koma daki , Mukhtar din ya bita da kallo basarwa yayi Yana jan su da hira Yana tamabayarsu makaranta.

  Ta komo d'akin amma kunnenta na  na ta jiyo hirarsa  ga dukkan alamu sun saba da shi ,da alama ma shi yake musu dawainiyar komai sai wani tambayar su sun ji jarabawa sunyi waye .Ta Yi tunanin a ranta.

      Dining ya kira su suka zauna bai samu guri ba ,ya sa shukra ta zuba musu abincin Huda suka hada ido da Hameeda sannan suka kalli Shukra suka maida kallonsu ga yayan nasu Huda ta zunguri Hameeda alama tayi mata da ina matar tashi ?

    Kamar ya san me suke tunani a rai yace "Antyn ta ku ba ta jin dadi sosai".

  Murmushi Huda tayi "Allah sarki Allah ya sawwake".

  Nan suka karkata ga cin abincin abinci dai yayi dad'i suka ci suka koshi suka sha lemo ,harda meat pie ya hado musu suka ci suka rufe sauran ,a take shukrah ta shiga kitchen ta wanke kwanunkan ta tabbatar yayi tsaf ta dawo suka zauna parlour tv ya kunna musu sannan ya dan tashi ya shiga dakinsa.

   Da bayan asr suka ta shi zasu tafi ,Huda tace bara su duba antyn a daki ya kallo suka wuce d'akin tana kwance sannan ta dubesu.Ya jiki suka hau yi mata da ido kawai take binsu har suka gama suka ce sun tafi suka wuce ta saki baki wato karya ya musu?

  Har waje ya raka su ya na jin dadi bata karyata shi ba da bai san ya zai ba sai da ya komo ciki ya nufi d'akinta kamar jiransa ta ke "Karyar ciwo ka min?"

  "Tohm ya zanyi kin je kin shige d'aki me kike tunani zasu ce?"

  Kai ta jinjina "Is well fitowar da nayi banyi maka ba kenan? Hira kake so nayi da su ko cikinsu zan shiga nayi wasa?"

  Kai ya girgiza ya ce "Ni ban ce ba kawai dai you should have sit with them".

  Banza tayi ta na juya baya ta cigaba da danna wayarta ,fita yayi Yana addua Allah ya ganar da ita.

  ****

Su Huda kamar suna jira suna isa gida  suka soma hirar matar Yaya  mara fara'a.

   "Ni duk ba wannan ba Umma shi ya zuba mana abinci wai ya ce Bata da lafiya ni dai ban yarda ba wlh".Hameeda ta fad'a.

  "Ko ta ma tambaya ya kike ko irin ya gida".Huda ta d'ora.

  "Atoh ni daman gudu na kenan yaran masu kudinnan raini da wulaƙanta mutum ba tana gani babanta ne ya dagashi ba".Umma ta furta.

      "Ga shan kamshi da kyar ta ke amsa gaisuwa". Shukra ta fad'a

  Daren ranar akan Ummi suka yi ta hira,Ya Mukhtar ya kira ya musu ya suka je gida suka tabbatar masa da lafiya.

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now