Itama murmushin tayi, suka dunguma sukayi gida Norah a motar babanta yayinda hidayat da miss Mary suka tafi a motar da suka zo na gida, sun samu su Aisha sun dawo har ma sun ci abinci, Seda hidayat ta fara taimakawa Farrah da wanka kan ta zo tayiwa Aisha, Norah ta shigo itama tayi wankanta ta zauna wurin hidayat tana sauraran darasussuka akan period wadda ita bata taɓa sani ba..

Hidayat sossai ta tsoratata da hulda da maza, ta nuna mata hadarinshi ba ga lafiyar ta ba har ma ga addininta, kuma sossai Norah ke ɗauka, kiran landline ne ya katse musu Hirar tasu Norah taje ta ɗauka dad ne yace ta kawo mishi Junior..

Ɗaukan shi tayi ta fito ta bar hidayat ɗin da Tunanin sabuwar yanayin da take tsintar kanta a ciki wadda bata taɓa ji ba..

A tsararriyar bedroom ɗinshi ta same su, Aisha na yin homework yayinda Farrah ke yin game a iPad kunnenta headphone ne tana jin wakar da game ɗin ke yi, haushin kasancewar su tare da Aishan take, karbar junior yayi yana mishi wasa yaron na bangala dariya..

Kwarai yake yabawa da tsabtar maman yaran sbd yadda a duk sadda ze ɗauki Junior kamshi na musamman ne ke tashi a jikinshi goyon ta Sam ba kazanta, a hankali ya tuna ranar da aka samu yaron da abunda ya faru, shi dae kwana biyu da suka yi da Hidayat kai tsaye ze iya cewa bata cikin mutane masu fitina ko rashin kunya, to meyasa babansu ze zaɓi wulakantata ta wannan hanya kawai don bata da kowa?

Da fa shima macece hakan za'a yi mishi, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Wayanshi da ya ɗauki ringing ganin sunan Godfather yasa ya ɗauka facetime ne, hakan yasa wani kasurgumin pastor ya bayyana sanye da kayansu na father, hannunshi rike da Bible kaman yadda bayanshi ke nuna a church yake..

"Hey my son!"

Raed na murmushi yace
"father good af, trust you are doing great?"

Da gudu Norah da Farrah suka zo fuskan wayar tashi suna leke ganin da gaske father ne yasa suka fara mishi surutu
"hello grandpa ka ce zaka zo har yau baka zo ba, we are really mad at you"

Murmushi yake yana cewa
"am so sorry my queen nd my princess, by God grace I will be with you guys in a jiffy, ayyuka ne suka min yawa a nan muna ta bada word of God, mutane na karbar almasihu"

Norah tace
"u r always talking abt this almasihu but Miss hidayat said he is also a Prophet sent by Almighty Allah, bcs Allah doesn't have a wife nor a son"

A take fuskar mutumin ta sauya yace
"who is miss hidayat?"

Farrah tace
"our new nanny from Nigeria grandpa I don't like her"

Raed na kallon Aisha yace
"hey Farrah be nice ok?"

Mikewa tayi ta fice wai tayi zuciya, girgiza kai yayi yana jin amsan da father yake baiwa Norah a lallai lallai se ta amince da faɗar cewa Almasihu is a son of God, ita kuma hankalinta ya fi kama na miss hidayat, daga karshe kyale ta yayi suka maida call ɗin phone call da Raed..

Kai tsaye ya nuna be son sabuwar nanny ɗinsu ze turo wata daga Amsterdam garin da yake a yanzu yana yaɗa addinin kiristanci ta cigaba da kula dasu, Raed be ce komai ba har suka gama wayan ya kashe..

Da Junior ya cigaba da wasa Aisha da Norah na mishi hira jefi jefi kaman daga sama ya jiyo ihun Farrah, da sauri ya miƙe ya nufi waje cikin Tunanin abunda ya same ta, a ɗakin hidayat ya ji kukanta shi da Norah da Aisha ne suka shiga ɗakin..

Tsaye suka ganta tana kuka sossai riƙe da kumatunta yayinda hidayat ke tsaye idanunta duk a waje zuciyarta kuwa banda skipping babu abunda yake..

"Farrah what is it? Me ya same ki?"
Raed ya watsa mata tambayar yana kokarin cire hannunta da ta saka a kumatunta cikin kuka tace

KOWA YA GA ZABUWA...Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora