Taƙare maganarta tana wani jijjiga jiki,da mamaki Sajidan ke kallon ta dan ita batasan ma me take cewa ba"ta bude baki da nufin tayi magana kenan sai Fauza ta rigata tana cewa"karkiyi sammanin dan kin riga wasu shigowa ki ɗauka kedin ta dabance ki mike ƙafa ki zauna gwara ki zauna a ɗosane dan da zaran mai waje tazo dolen dolenki ki naɗe ta barmarki ki bar waje.

"Ikon Allah wai Fauza lafiyan ki kowa yau kode baki da lafiyane?kuma maganan me kike nifa bansan akan me kike magana ba,Sajida ta faɗa da damuwa saman fuskarta.

Madadin ta bata amsa sai kawai tace ke ta faɗa tana nuna Aisha da tun shigowarta kallo ɗaya ta mata ta dauke kai ta cigaba da kallon hotona da take,bata amsa mata ba saide ta ɗago ta zuba mata idon ta na mai kama da mai jin bacci .

"kizo Mami tana kiran ki tafaɗa tana yatsine fuska kaman wacce taga wani abun ƙi daga haka tayi gaba mikewa Aisha tayi ta rufa mata baya binsu abaya Sajida tayi.

Da sallama ta shiga falon ba wanda ya amsa sallamar nata daga Mami data sa akayi kiranta har ita Fauza ta wani hakimce saman ɗaya daga cikin kugerun alfarma dake zagaye da a falon ta harare ta ta motsa fuska.

Tsayawa tayi daga bakin ƙofa kanta a ƙasa"gani Mami tace cikin sanyin murya kallon ta Mami tayi sannan ta watsar kaman ba zatayi magana ba sai kuma tace"na ganki ai jita kamar wata ta kirki saboda munafirci wai gani tace tana kwaikoyon muryarta.

"Idan ba kyason barin Gidan nan dole kibi duk wata doka daxan gindaya miki da farko de meke a tsakanin ki da Amadu wace irin alaqace dake tsakanin ki da shi?

"Babu tace da ita a takaice.

Da sauri Fauza ta mike tsaye ta dire gabanta tana kallon ta cikin sakin fuska tace"maimaita abunda kikace yanxu,

"Eh ina nufin babu kawai shiɗin Oga nane kuma wani aiki muka zo yi nan din ta tsinci kanta da faɗin haka.

"Yauwa dama me nafaɗa miki Mami me Yah Ahmad zeyi da kucakar yarinyar nan amma baki yarda dani ba kinfi yarda da maganar da Yah Sajid yafaɗa miki sai kace ba jinin sa bace ni bansan abunda nasama ba da bayasona da Yah Ahmad ɗin.

Ta kare maganan cike da shagwaɓa tana tura baki,ita kanta Mami ajiyar zuciya ta sauke cike da jin daɗin amsa da tasamu a wajen Aishan tace"yauwa kinga yanzu abunda nakeso dake ki koma can ɓagaren ki ɗauko kayanki ki dawo nan da zama ko a ɗakin masu aikine zefi da ku zauna tare da ƙato daga ke sai shi.

Kuma zakina kama ma ma'aikin namu wasu ayyuka dan aiki yana neman yi mata yawa.

Gobe mai Gidan ze dawo daga tafiya inason ki shiga ki gyara masa ɗakinsa ki canza sabon zanin gado abunda ya kaiki kawai zakiyi ki fita bana son yawan kalle kalle na wuce ƙa'ida.

Sannan gyara ɗakin Fauza da wanke mata banɗaki sai wanke mata kaya duk wannan magana da take tanayin sane cike da izza tana zaune a inda take ko motsawa batayi ba,saima ƙafanta ɗaya data ɗaura saman ɗayan.

Ganin tayi shiru yasa Aisha ɗagowa ta kalle ta cikin sake yin ƙasa da kanta tace"Mami niɗin ba'a juyani cikin sauki sai abunda naga dama zuciyata ta aminta nake.

Batun share ɗakin mai Gidan zanyi,amma Mami idan har kina tsoron wani abu maiyasa ke ba zakiyi hakan da kanki ba,kiyifa hakuri idan magana ta taɓata miki rai.

Sannan bazan taɓa yima wannan wanki da gyara mata ɗaki da kika ce ba,dan itama macece wataran Aure zatayi idan tayi aure a irin haka itama  zata sa ƴan aiki ɗakin kwanan su suna gane musu sirrin su ne?

Sake baki Mami tayi tana kallon Aisha tare da mamaki karfin hali irin nata,dan ita ba taɓayi mata irin haka ba.

Sajida dake tsaya a wajen sai kumshe dariyar ta take gudun kar tayisa a bayyane ta shiga uku gun Mami da ƙanwar mijin nata dan Fauza ba kunyace da ita ba,idan ta tashi rashin kunyar ta hatta da Yayan nata ba ragamasa takeyi ba.

Suna nan tsaye a gun Ahmad ya dawo daga wajen aiki yashiga sashin Sajid basa nan shine yazo nan din da sallama yashigo Mami da Fauza basan wanda yafi ɗan uwan sa ba,gun nuna farin cikin shigowar sa nan din idan suka tuna a yanda yafita daga gidan ɗazu duk da ko a fuskane be nuna musu komai ba,da fara'a tare haba haba suka shiga amsa sallamar nasa.

Tunda yashigo idon sa kurr akan Aisha ko kiftawa babu itama din sai akayi sa'a shidin take kallo.

Kana ganin yanda suke kallon junan su cike da shauƙi harma sun mance da akwai wasu halitta a wajen bayan su ɗin.

Takowa yake a hankali a hankali harya iso gareta yakai hannu saman tattausan fuskarta kenan "Amadi me haka Mami ta faɗa a tsawace dan ita kanta batasan tayi hakan ba.

A tare suka janye daga kallon junan nasu ko wanne na kokarin basarwa,kallon ta yake cike cikin kamilaliyar fuskarsa ya ɗan ɓata fuska sai yace"Mami barka da yamma.

Ba karamin ƙoƙari tayi wajen tattara nutsuwarta dan ganin bata kofsa ba,ita ko Fauza tunda taga yanda suke kallon junan su ta fece dan bazata iya tsayawa ta kalli wannan kayan taƙaicin ba.

"Yauwa barka Amadi fatan ka dawo lafiya?"komai normal ya amsa mata idon sa nakan Aisha da taƙi tasake kallon sa,saide tanajin a jikin ta kaman idanunsa na kanta.

Sajida ta kalle sa cike da zolaya tace"irin wannan kallo haka Yah Ahmadi kamata kurage wa Yaranku su samu na kallo wataran.

Mami ta faki idon Ahmad ta harari Sajida dake kallon ta a fakaice dan ita Allah yana gani tafison Aisha da Ahmad din fiye Fauza data take kawar mijinta ma.

Ahmad ba kunya yaja Aisha suka fita daga falon sakin baki Mami tayi tana jinjina girman rashin kunyan Ahmad ɗin  shikuma yana sane da gayya yayi hakan.

A zafafi Mami ta koma kan Sajida tana surfa mata ruwan masifa ta inda ta shiga ba tanan take fita ba karshe tace"wallahi kin bani mamaki Sajida na dauka ko ba komai kemai tsayama Fauza ne kan abunda take so harsai inda karfin ki ya kare amma dake za hada kai a hana mata samun wannan farin cikin .

"Yi hakuri Mami aini bansan da alaqa dake tsakanin ta dashi ɗin bane"dallah rufamun baki kuma wallahi nasake jin yarinyar nan ta zauna wajenki kaman yanda naji ɗazu kemadin zamanki ya kare a gidan nan karki dauka zan daga miki ƙafane dan Abot da ke tsakanina da Mahaifiyarki wallahi sai in rufe idona naci miki mutumci dan farin cikin Fauza yafimun komai aduniyar nan.


ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now