"Ina so ka mini alƙawarin bayan raina zaka auri Salima."

Yana tunawa sai da suka kusa yin faɗa da Hafiz sannan ya amince amma bai tsaya a nan ba sai da shima Hafiz ya sa ya mishi alƙawarin zai auri matarshi Juwairiyya. Karkaɗa kanshi yayi cikin sauri ya ce,

"Halin Salima da matarka daban ne, a yanzu ma matarka bata ganin girmana ina ga kuma in baka doron ƙasa? Ni ina da tabbacin Salima zata yarda ta aureka idan ka faɗa mata ni na aikoka, sannan ni ba zan iya aurenta babu jituwa a tsakaninmu ba."

"Ban san dalilinka na cewa in auri matarka ba amma maganar gaskiya shine if you won't return the favour nima zan ajiye nawa." Faɗin Hafiz cikin finality a maganarshi.

Dogon tunani Muhammad yayi domin dalilinshi na son Hafiz ya auri Salima shine she is too soft and submissive! A yau idan baya duniya ta auri wani to ragamar ɗan cikinta zai koma hannun mijin nata ne, hakan na nufin duk hukuncin da ya yanke a kan ɗan shi zata bi saboda bata iya voicing mind ɗinta, he can't risk that kuma ya sani duk duniya Hafiz ne zai iya riƙe mishi matarshi da ɗanshi cikin amana babu cuta ko cutarwa.

"Kai me yasa kake son in aureta?" Ya tambayi Hafiz.

"Ba zan tambaye ka naka dalilin ba amma ni nawa shine Juwairiyya yarinya ce da zan iya cewa tana da zafi wanda zafin nata yana sa tayi making rash decisions ba tare da tayi tunanin consequences ɗin ba. Yawanci kuma they backfired, amma hakan duk bai sa ta hankalta ta daina ɗaukan komai da zafi ba. Wallahi mutumiyar kirki ce, ita dai ta ƙi jinin wulaƙanci ne da cin zarafin mutum, kuma kaima in zaka mata adalci zaka faɗi hakan domin abu ka mata wanda ta ɗaukeshi a matsayin wulaƙanci. Amma ba gashi she goes along with your wife ba! Why? Saboda bata da fitina, wulaƙanci ko cin zarafin mutum. Ina tausaya mata idan ta shiga hannun mutum mai mugunta amma kai zaka iya riƙe mini ita amana. Ka kula mini da ita da duk abun da ta haifa in Allah Ya bamu rabo."

"Na yadda zan aureta amma in har ta nuna bata so I won't pressure her. But bana ma tunanin hakan zai faru domin ni ne zan mutu Hafiz kafin kai."

"Ka daina cewa haka, mutuwa tana kan kowa sannan sau nawa mutumin da yake kwance a asibiti rai a hannun Allah ya warke sai wani da yake bacci a kan gadonshi ya tafi ta can? Allah Ya sa mu cika da imani kawai Muhammad."

Bayan wannan maganar ta su ya samu Salima da maganar a ranar bai bari ya kwana ba ya umurceta da cewa in ya mutu kar ta auri kowa sai Hafiz domin shi kaɗai ne zai riƙeta amana da ɗan cikinta, tana kuka ta amince don ta faranta mishi rai kuma ya sani ba zata tsallake ba saboda ta san Hafiz mutumin kirki ne to me zai hanata amince mishi? Ya ji daɗi a ranshi domin yanzu yana da tabbacin ahalinshi zasu faɗa hannu mai kyau bayan ranshi, abun da bai sani ba shine ashe Hafiz ne zai tafi ba shi ba.

Faɗin irin tashin hankalin da ya shiga ba zai iya faɗuwa ba sannan ganin Juwairiyya da yayi yasa yaji tausayinta matuƙa a zuciyarshi domin Hafiz yana faɗa mishi irin soyayyar da take nuna mishi. Ya sani tana jin mutuwar fiye da yanda take nunawa a fuskarta idan ya shigo da abokansu gurinta don su gaisheta, sannan ganinta kaɗai kan sa ya ji shima kuka na son kwace mishi, domin daga shi har ita sun yi rashi babba a rayuwarsu.

Tun bayan rasuwar ya ɗaukarwa kanshi nauyin kula da ita domin ya sani da Hafiz ne yake da rai zai kula da iyalinshi sai inda ƙarfinshi ya ƙare, to shi me yasa ba zai yi hakan ga nashi ba? Bayan takabanta ya so ya zo mata da batun Hafiz amma kullum sai ya ji shakka ya shigeshi domin bai san yaya zata ɗauki zancen ba, bai san ko Hafiz ya faɗa mata sun yi wannan alƙawarin wa junansu ba. Sannan zai aureta amma ba don yana sonta ba sai don shima ya fara jin tausayin nata domin kamar bata da wayon zama da mutane. A yanda yake mata hidima ya kuma sauƙe duk wani jin kanshi da yake nuna mata a da, ya kamata a ce tana mishi godiya ko kuma ta nuna abun da yake yi yana taimakonta. Tana buƙatar koyon zama da mutane babu tantama.

TAFIYAR MU (Completed)Where stories live. Discover now