Sake fashewa da kukan tace"mami ashe duk jiran nan danayi ma yah Ahmad a banza nayi shi,malaman ma dakike zuwa wajen su dukan su ma karyata ne karya suke miki ba gaskiya ko daya cikin maganan su sai cuta.

Zaro idonta tayi tace"ke banson sakarci ni duk kinsani a duhu yi mun dalla dalla yanda zan gane"to mami yah Ahmad da matar sa yazo yanzu haka yarinyar tana cikin gidan nan kuma ɗaki ɗaya za su kwana yau na shiga uku.

zufa ne ya shiga tsastsafo mata a goshi tana kai komo cikin falon ta dun ƙule hannun ta ɗaya tana kaiwa iska naushi tace"ya akai nayi missin target bayan malam yace mun aure tsanin sa da basma babu shi koda kuwa a mafarkine balle a zahiri to wacece ita wannan me son wasa da wutan?

Kede shiga ki kwanta ki kwantar da hankalin ki tunda muka samu ya dawo nan komai yazo gidan sauki kede ki kiyaye dukkan sharuɗan da malam din yace.

*******
WASHE GARI:
Bayan tayi sallan asuba zama tayi tana yin azkar dinta kaman yanda ta saba tana nan zaune saiga shi ya shigo ɗakin da sallama ƙasa ƙasa ta amsa ba kuma lalle ya jita ba,miƙewa tayi da kyar tana dafe da kanta da har sannan yake sara mata kaɗan kaɗan.

Kallon ta yayi  kaman ba zeyi mata magana ba sai kuma ya ga hakkin sane kula da lafiyar ta da tsare mutuncin ta tunda ya rabota da kowa ya kuma dauko ta ya zo da ita inda batasan kowa ba sai shi,a jiyar zuciya ya sauke yace

"Ya jikin naki?
A mamakance ta juyo tana kallon sa ko ba tayi magana ba ya gane mamaki take ta yanda yasan bata da lafiya,kaman ko ya shiga zuciyar ta ya gani yace"jiya da daddare koda na shigo na taddaki zazzaɓi ya rufeki shine na miki allura.

A hargitse ta juya tana kallon sa jin abunda yace na ya mata allura kenan ya gama kallar mata jiki"ba fa abunda kike tunani bane kawai alluran namiki ya faɗa yana shiga toilet.

Falo ta koma ta zauna shiru tayi tana tunanin yanzu a wani hali ƴan ƙannen ta suke na rashin ta kusa da su,duk da tasan anty hajia anty malika malik ya faisal dukkan su ba za su bari suyi kukan rashin ta ba,amna ita dole tayi kukan rashin su kusa da ita idan ta tuna da wa take tare da.

Fitinannen kamshin nan nashi shiya fara isar mata da sakon zuwan sa kafin shi,yana daura agogo a hannun sa ya karasa shigowa falon ko kallon inda take zaune beyi ba yace"ki shirya zamu shiga ciki mu gaisa da mami yana fadin haka ya  zauna saman ɗaya daga cikin kugerun falon ya daura ƙafa ɗaya kan ɗaya ya dauki remote yana kara gudun ac.

A sanyaye ta miki ta shiga ciki wanka tayi ta fito ta shafa mai ta ɗan murza hoda a fuskar ta,ta feshe jikin ta da turare ta dauki ɗaya daga cikin unders din da ya siyo mata tasa tayi mamakin yanda bra din sukai mata cif cif ya akai yasan size dinta?ganin zata ɓatawa kanta lokacine wajen tunane tunanen banza yasa ta ture komai gefe ɗaya ta saka doguwar riga daya daga cikin.wanda yakawo mata jiya kalan sun mata kyau takalmi shima data gani cikin ledar ta saka ta ɗan murza turaren misik kaɗan ta fito tana yane kanta da gyalen kayan.

Yana ganin fitowar ta yamike yayi gaba ta rufa masa baya, duk da beyi mata magana tasan nufin sa nayin gaban babban part wanda take ganin kaman yafi sauran girma ya nufa tana biye dashi a baya saida yayi knocking sannan ya tura ƙofan ya shiga tunda suka doshi nan haka kawai takeji faduwar gaba tana ta addu'a a ranta.

shiga cikin falon tayi da ƙafar dama bakin ta dauke da addu'a zaune take a kan kugera da gani wannan zatayi izza kallo ɗaya Aisha ta mata ta sauke kanta kasa ta zube a gaban ta tana gaidata ganin idon Ahmad yasa mami amsa mata tana tambayar gajiyar hanya itade Aisha kanta a ƙasa.

Bayan sun gama gaisawa Ahmad ya miƙe ita ma saurin miƙe tayi,ganin kaman fita za suyi mami ta rigasu magantuwa tace"bade komawa zakuyi ba?

Sosa kansa yayi yana cewa"dama maidata zanyi ni akwai inda zani ne.

"Amma ai ka tsaya kuyi breakfast kafin ka fita,ta faɗa tana tsare shi da ƙananun idonta kaman na ƴan china a ranta kuwa addu'a take na Allah yasa karyaƙi ci take.

Har ta miƙe da nufin su je dining amma sai Ahmad ɗin yayi sauri katse mata hanzari dacewa"sauri nake mami karna bar mutane na jirana"to me aciki african time ne fa akeyi kuma ba lalle su din ma sun ()bata ƙarasa ba wayan tayi ringin ya kara a kunne yana cewa "on my way nan da minti goma zan iso daga haka ya kashe wayan yana dan kallon ta  dan ta koma inda ta tashi ta zauna"ok mami sai na dawo a dawo lafiya tamasa tana cewa amma nan zaka bar mana ita har sai ka dawo ko?"da ba matsala  ya amsa yayi saurin fita.

Aisha komawa tayi ta zauna a hankali tana jin zuciyar na tsananta bugawa haka kawai taji wani abu mai kama da tsoro na ɗar suwa a zuciyarta haka kawai.taji matar ba tayi mata ba.

Sun zauna shiru tsawon  minti uku sai mami ta muskuta ta gyara zaman ta ta kalli Aisha a wulakance tana yatsne fuska tace"yarinya ya sunanki?

Aisha ta amsa mata da"Aisha
Hmm"Aisha suna mai daɗi tafaɗa tana kafe Aishan da ido da ita kuma tayi kasa da kanta tana wasa da zobe hannun ta.

"Me haɗinki da Ahmad?
"Eh Aishan tace ganin kaman bata gane tambayan ba yasa ta sake cewa"in nufin shiɗin  me hadinki da shi?
Miji?ko saurayi?ko kuma aboki?duk da kin masa ƙanƙanta amma zan so sanin wanne daga cikin wanda na lissafa kike?

Kai ta girgiza ta alama babu'babu kike nufi ta daka mata tsawa ganin kaman raina mata hankali takeson yi gashi taƙi ta bude bakin ta tayi magana.

Safna da tasowar ta daga bacci kenan ta fito tana ya mutse fuska ta tsinkayo muryan mami tana magana a tsawace ta ɗaga murya tana cewa"kode zaman daduro suke?

Kallamar daduro nan tama Aisha zafi dan haka mikewa tayi tsaye ta zabgawa safna wani mugun kallon tace"daduron ma iya wace wani inya isa yayi mu gani ta faɗin haka tayi ficewar ta daga falon biyo ta safna tayi tana cewa"gidan ai bana ubanki bane dan haka ba zaki kizo ki kawo mana raini ba shegiya ƴar matsiyata da gani asiri kika masa idan ko ba haka ba me yah ahmad zeyi da ke du beki fa.

Ta fada tana nuna Aisha tana mata kallon sama da kasa.

Ita de Aisha bata sake cewa kala ba,mami ce ta fito tana tafiyar nan tata kamar ta agwagwa cike da izza tace"ke Aisha zo ki bata hakuri.

Ko kallon inda suke Aisha bata sake yi ba,zuciyar ta namata suya ji take kaman zuciyar tata za tayi mata bindiga ta faso amma haka ta rinƙa tausan kanta da kanta"Aisha jeki ki bata hakurin tsunawa wada ba gajiyawa bace abunda gefe ɗaya na zuciyar ta take faɗa mata kenan.

Aisha be kamata da haduwarki da mutane ki nuna halin rashi hakuri ba yi hakuri ki bisu a sannu ta hakane kawai zaki san inda suka dosa tana kare wannan tunanin ta nufo su ta tsuna tace"yi hakuri
"Ban jiki da kyau ba.
Kiyi kakuri tasake faɗa cikin ɗan ɗanga murya daidai Ahmad da yayi mantuwa ya shigo gidan ta ƙaramin ƙofa ya ga komai nan ita ma wasu hawaye masu dumi suka shiga zarya saman kumatun ta.

Mami da safna dariya suke ɓaɓɓakewa dashi harda su tafawa kaman wasu ƙawayen juna,juyawar da za suyi idanun su ya sauka kan Ahmad dake tsaye goye da hannun sa saman ƙirginsa ya zuba musu ido.



ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now