"Ina jinka." Kawai ta iya cewa dashi tana sauraronshi.

Gyaran murya ya fara kana ya gyara tsayuwarshi ya fuskanceta tarr yace,

"Juwairiyya ina sonki ina kuma da niyyar aurenki, sai dai a yanzu matata ta samu labarin ina nemanki muna ta fitina a gida. Yanzu abun da nake so dake shine ki yarda mu yi auren sirri tsakaninmu, zan baki sadakinki ba tare da kowa ya sani ba sai mu biyu, da zarar nayi settling ɗin matata sai mu bayyana auren ki zo ki tare."

Shiru ta yi har na tsawon minti ɗaya kanta a ƙasa tana tunani, shi kuma Ilyas ido ya zuba mata yana ta gyara tsayuwarshi kamar mara gaskiya. Can Juwairiyya ta ɗago kanta da ɗan guntun murmushi a fuskarta tace,

"Shikenan zan yi tunani a kai. Amma yaya batun....?" Ta nuna kanta sannan shima ta nuna shi.

Ƙura mata ido yayi yana son fahimtar me take nufi, kashe mishi ido ɗaya ta yi wanda hakan yasa fuskarshi ta washe hakwaranshi suka bayyana cikin farin ciki.

"Yauwa ƴar gari, wannan ba matsala bace. Nuhu abokina da name baki labarinshi yana da gida a nan cikin New GRA, unguwar ma ba'a gama cika ba kuma gida ne mai kyau. A can zamu dinga zuwa muna rage zafi har lokacin da zamu bayyana auren."

"To idan nayi ciki kafin nan fa?"

"Zamu yi amfani da protection ko kuma ki sha maganin hana ɗaukan ciki." Ya faɗa hankali kwance kamar dama ya jima da wannan nazarin.

"Da alama ka jima kana tunanin nan, amma kuma meyasa tun zuwan ka baka faɗa mini hakan ba ai da yanzu an wuce gurin, nima da na samu sauƙi."

Wata dariya Ilyas ya saka Juwairiyya kuma ta murmusa tana kallonshi.

"Ke ɗin ce an bani labarin kina da zafi, gashi kuma in bakya son abu babu mai sakaki dole. Amma dai nace musu sai dai in ba'a bi dake yanda kike so ba. Kin ganni nan? Bana son na ga ana takurawa mace ko kaɗan, ku mata sai da lallami."

"Hakane kam. Kuma idan mutum yana son yin zina da mace zai iya shafe har wata biyu yana bibiyarta don buƙatarshi ta biya. Su waɗanda suka faɗa maka ina da zafin sun manta basu faɗa maka cewa ina da ilimin addini ba, sannan ni ba shashasha ba ce."

Nan take annurin fuskarsa ta ɗauke, domin sai a yanzu ya gane cewa shigo-shigo-ba zurfi ta mishi. Fuskarshi ya tamke don ya san daga yanzu duk wata kalma da zata fito daga bakinta ba lallai bane ta mishi daɗi ba.

"Ilyas ka bani mamaki ka kuma saka na ƙara tsorita da mazan yanzu. Masu hali irin naka sun zo amma da buƙatarsu suke zuwa a tafin hannunsu babu ɓoye-ɓoye, kai kuma sai da ka yaudareni da kyawawan hali har na faɗa sonka. Wallahi ni ba mazinaciya bace Ilyas, sannan na ɗauka zuwa kayi ka rufa mini asiri ashe kai tona mini asiri ka zo yi. Ka yaudareni ka kuma cuceni, Allah Ya saka mini." Sai a lokacin muryarta ta fara rawa ta nufi cikin gidan su cikin sauri tana share hawayen da ya zubo daga fuskarta.

Bata kai ga shiga ɗaki ba ta ji ya kunna motarshi ya tafi, ta yi tsammanin zai kirata ya ce gwadata yake yi, amma shirunshi har ta shigo ya nuna cewa da gaske yake. Kuma tunda bai samu abun da ya zo nema ba ya tafi.

Baby wanda ya ga shigowar Juwairiyya balle ya ga halin da take ciki, tayi kuka sosai domin ta san in ba mutuwa ba bazata samu kanta a cikin wannan halin ba, da Hafiz ɗinta yana raye da babu wani ɗan iskan garin da zai zo ya nemeta da lalata, ashe an yi gaskiya da aka ce 'Mutuncin mace ɗakin mijinta' ashe aurenta ba ƙaramin rufa mata asiri yake yi ba. Yanzu ina zata saka kanta? Ga wa'adin Mama saura wata ɗaya ya cika! Da waye zata haɗata in bata nemo mijin auren ba? Da wannan tunanin Sumayya ta shigo ta sameta, amma ko da ta tambayeta me ya sameta bata iya faɗa mata ba, da haka ta lalatar da zancen.

Sati ɗaya da haka Mama ta lura babu mai zuwa gurin Juwairiyya, hakan yasa ta kirata don a yanzu da biki ya saura sati uku tana son sanin halin da take ciki.

TAFIYAR MU (Completed)Where stories live. Discover now