Instagram @Bakhoor_by_faixy

Page 1️⃣

******************************

         Zaune take gaban dan Camping gas din su,wanda ke ci sosai,tukunya mara girma ne daure akan gas din,yayin da ta dan dauraye spoon din da take jifan danwake da shi a cikin ruwan da ke gefen ta,dan turo baki tayi gaba sannan cikin azama ta cigaba da jifan danwaken nata da chokali,ba karamin danasanin cewa Umman ta suyi Danwake yau tayi ba,domin da ta san zai dauka mata time haka da azumin ta kawai ta dauka yau,gashi abun haushi ko iyayi zan kira sa sam bata iya jifa ko ince sakun dan wake da hannu ba,saidai da spoon,domin a cewar ta wai yayi abun kyama ko in ce kazanta wani in ya gani ma ba zai iya ci ba,zan iya cewa tana da mugun tsafta domin a nutse ta ke komai,sannan kuma tana da kyankyami don ko kadan ba za ta iya siyan dan waken siyarwa ta ci ba,murmushi na ga ta sake a kyakyawar fuskan ta,sakamakon ganin jifan nata ya zo karshe,da sauri ta rage wutan gas din domin fara alamun tashowa sama da ruwan dan waken ya fara,gudun kar ya zube ya bata guri,cikin sassanyar siririyar daddadan muryan ta,ta shiga kwalo wa Mahaifiyar ta da ke daki tana nadin kaya kira,fadi take

         " Ummah!Ummah!!!ki zo don Allah"jin kiran Autar nata ne ya sanya Ummah aje zanin hannun ta,sannan ta fito daga dakin tare da sanya slippers din kofar dakin,sannan ta nufo dan matsakaicin kitchen din su wanda ya ke daidai rayuwar talaka me karamin karfi "kin san Allah mun kusa samun mugun matsala dake akan irin kiran makafin da kike kwala mun,haba ina daili yarinya kira haka kamar Makauniya"baki ta dan turo tare da mikewa daga yar mitsitsiyar kujerar da take kai,cike da barkonci tace "Allah ya bar min ke Hajiya Ummah me gadon zinari ta" dan dariya Umma tayi sannan tace "Hajiyar dadin baki,yanzu kuma wani munafurcin ake son isarwa?" Itama dariya tayi domin ganin Umman tayi saurin gano ta,ka fin ta ce "Yauwa Umma daman Dan waken ne za ki dan kalla min na gama jifawa,in yayi ban fito ba sai a taya ni soya mangyada,wanka anyi,muna da submitting din assignment early in the morning wlhy" ta kare tana narai narai da idanu kamar wata karamar yarinya.

Harara Umma ta maka mata sannan tace "Ai dole kiyi narai narai da idanu,na ga dai dan waken nan ke kike ce mun ayi shi,sannan yanzu akan wani dalili aiki zai dawo kai na??" Ai da jin haka ya sanya ta saurin ficewa daga kitchen din, "ni fa taimako nace a taimaka ayi mun Hajiya Umma,ke dai kina shirun ki bari dai Allah yayi na gama sch in ga lafiya na bude katon Restaurant dina kudi su fara shigo mun,yasin dauke ki zan yi mun bar kasar nan ke nan,ko kya samu kiyi rayuwar yanci ki bar rayuwar kuncin cikin gidan nan"murmushi Umma tayi sannan tace "Allah ya amsa Uwata,amman kafin ki kai da yin kudin,ni kam bana hana kunna mun Gas dina anyhow ba?kina gani ganan gawayi muna da amman shine saboda tsaban son jiki baki hada ba ko?Kin zabi ki kunna mun dan Gas din da nake maneji a wannan halin kunci da tsadar rayuwar da muke fama da shi a kasan nan"dan dariya tayi kasa kasa don sanin halin Umman nata sarai da shegen son tattali,tare da kin almabazaranci(domin ance Almubazzari dan uwan shedan ne) ,wato dai Umma so tayi na hau hada gawayi cikin sanyin safiyar nan,ai sai nayi lattin Lecture,gashi sam Malamin da zai dauke su first period bashi da mutunci ko kadan,sannan baya shayin keta maka rigan mutunci ko da a gaban waye kuwa,ya sanya duk iskancin mutum za ka tarar yana shayin sa,domin da an ce shine a class din su ko zai shiga,dole mutum ya nutsu,domin shi bawa students carry over abu ne da ya fiye masa shan ruwa sauki,dan tsaki ta dan ja don sam taki jinin Malamin,tunowa ya basu assignment da za suyi submitting da safe ya sanya ta saurin fadawa dakin Umma,cikin hanzari kuwa ta nufi inda Flask din da ke aje kusa da jikin gado,murmushi ta sake wanda ya kara bayyana asalin kyan ta domin irin mutanan ne masu manya da kuma kananun kyau,jin cike ya ke dam da ruwa ya sanya ta murmushi,cikin sauri kuwa ta juye ruwan a bucket wanda sai tururi yake alamun da zafin sa,domin flask din irin manyan nan masu rike zafi da nauyi ko in ce muku irin flask din masu jego,aje empty flask din tayi a inda ta samu,deep down ta san sarai irin dramar da za su yi da Umman nata in ta gano ta juye mata ruwan zafin ta,hakan ma ba tare da tambaya ba,domin sam bata da lokacin hada murhu har ta tsaya daura ruwan zafin wanka,Umma kuma ba bari za ta yi tayi using mata Gas ba.

 A SIMPLE DARE (WASA DA SO)Where stories live. Discover now