"Ai cewa mayayi kar'a faɗamaka sai gaka kaima kazo,cewar Ammi.

"Kar'afadamun kuma?yasake tambaya da mamaki"eh ninace karta fada maka saboda banason katada hankalin ka,kumama menene dan  an fadama din amfanin me jinnaka zeyi?eh sosai sukai mamaki da yanda yake magana duk ya birkice sai yanzu ma Ahmad ta lura da yanda falon yake a hargetsa.

Ɗagowa yayi ya zubawa Ammin sa ido itama shiɗin take kallo idonta na cikowa da ƙwallah"dawowata kenan daga gidan ikilima na tadda duk ya birkita komai bama falon kadai ba hatta da ɗakin kwanan sa sai kaga yanda yayi filla filla da komai duk ya birkita komai kaman mai neman wani abun, waya Ahmad yaciro bayan yagama sauraron Ammin nasa yakira family dr dinsu da yazo yaduba Alhajin ko alluran baccine amasa.

Ba ɗauki lokaci mai tsawo ba kuwa saiga dr balami yazo wayan Ahmad din yakira yace gashi a ƙofan shigowa falo fitowa Ahmad yayi yashigo dashi saida ya gwada masa bp ɗinsa sannan yamasa alluran bacci,yace bara zeje ya haɗo masa magani yatafi kawowa shikuma Alh badanasi be jima ba bacci yayi awon gaba dashi nan suka sauke ajiyar zuciya Ammi ta sauke.

****Aisha kallo nan juyawa tayi tana kallon abunda ake nuna matan" jarida kuma?tafaɗa tana karɓa a hannun anty malikan head line ɗin kawai ta kalla.

Cikin zaro ido tana dan rufe bakinta da hannu tace"Anty malika dama haryanzu ana safaran mutane kaman wasu kaya bayan ta miyagun ƙwayoyi da akeyi?

"Nimade abunda nagani kenan abunne da daure kai wallahi Aisha yanzu a yanda ƙasarmu take muna da ƴan sanda soji mobil ace ana irin wannan abun kuma wai ace basu da masaniya ai akwai ayan tambaya suma akansu.

"Yanzu anty malika idan na fahinceki daidai kinason cewa jami'an tsaron mu na ƙasa basa aiki yadda ya kamata kenan?

"Kusan hakane Aisha?"to yanzu idan basu din bane suwaye suka kame waƴan nan din?tayi tambayan dan son kore zargin ta"wasune da ba'asan ko suwaye ba Aisha ai wannan ma abun taƙaicine kiduba irin yanda yah faisal yake aiki tuƙuru ba dare ba rana amma ace wai wasu daba jami'ai bane zasuyi wannan aiki daya dace ace sune sukai.

"Kinga Antya malika shirya dawuri muwuce kar ayi bamu wajen kuma magana dakike ai ko ke zaki iya saukakawa jami'an tsaro nauyi idan kinga wanda baki yarda dashi ba ko kinga ana wani abun da baki yarda ba sai kiyi shiuttt dan a kamesu"hmmm Aisha kenan wai yanaga kaman yau kinma fini zumuɗi da zuwa gidan su antyn takine wai me sirri?takare tana ɗaga mata giranta ɗaya'kawai de inason zuwanne saboda inga yau kuma wacce ƙaryar za'ayi"kede faɗi gaskiya hajia kode kode"a'a wallahi anty ko wancan na sameta nabata hakuri kuma ita ta buƙaci naje ɗin,shiru Anty malika tayi dan kanta ya kulle"kika bata hakuri kikace?

"Eh anty
"Kan wani dalili kika bata hakuri kuma yaushe kuka haɗu da ita kode ita tasa akayi kidnapin dinki?"anty duka wannan tambayan lokaci guda wanne kike son na amsa miki"duka tace tana tsareta da ido kafin Aisha tayi magana saiga khadija tashigo da gudu tana cewa"anty wai kuyi sauri inji yah malik.

Da sauri Aisha ta miƙe tayi waje dan gujewa amsa tambayar anty malika tana cewa"kisamemu waje daga haka ta riko hannu khadija sukai waje saida suka biya ta ɗakin anty hajia sukai mata sallama tana sake jaddadawa Aisha takula da kanta banda keɓewa ke kaɗai ki zauna cikin mutane inma kinji bazaki iya zaman ba to yi zaman ki a gida.

Aisha dake da target akan tafiyar tayi sauri tana cewa"karki damu anty hajia zan zauna bazan tashi ba,tafaɗa nan anty malika tasameta tare suka fita inda malik ƙe tsaye da mota yana jiran su.

Tare suka shiga bayan mota da ummu salma autan anty hajja khadija ce tashiga gaban tafiyar minti ashirin ya kaisu gidan Alh sunusi inda anan zasuyi taron,kasancewar gidan babba gidane anƙawata inda za'ayi taron amarya da ƙawanta duka sun saka kaya iri ɗaya sai taka rawa suke mai kiɗan ƙwarya nayi amarya na zaune hakimce.

Gurin amarya suka fara zuwa sukai ggaisa sannan suka koma gefe suka zauna suna tafi can Aisha ta duna agogo dake daure a tsintsiyar hannunta tayi tsuka tasake yin tsukan akaro na biyu kallon ta anty malika tayi tace"lafiya ke kaɗai kike ta tsuka?"fitsari nakeji kuma banson tafiya ni kaɗai.

in banda abunki ai nan cikin gidane kinga jeki kiyi kidawo,mikewa Aisha tayi tanufi cikin gidan bayan tasaka face mark ɓaki tana shiga falon tafara ƴan dube dube  Alh sunusi ne ya leƙo daga can saman beni yana tambaya"waye anan ɗin? cikin kamewarta tajuya tana kin kallon sa tace"nice fitsari zanyi bayi nake dubawa.

Zonan ki biyoni yafada yanayin gaba bin sa abaya tayi tana hawa benin tanabin ko ina da ido bayan ta seta cameran dake jikin veil ɗinta wata kofa yanufa tana biye dashi a baya mutum ukune sune zaune a ɗakin tagane Alh shehu saurayi fadila kawarta daya kamo yace ita yakeso,sai Alh sunusin da kansa ɗayan ne bata sanshi ba.

Shiga can ki haɗo mana coffee akwai komai gyaɗa masa kanta kawai tayi batare da tayi magana ba,tana shiga inda yanuna mata tafara jin kaman nishi tawani ƙofa dake kulle ta cikin kitchen din jikinta ne yaɗauki bari take wani irin zufa yashiga karyo mata ta ƙofofin gashi dake jikinta.

A hankali take takawa harta isa bakin ƙofan dakin leƙawa tayi ta ɓulin makulle"kee yi sauri kikawo magana da tajine ya hanata lekawa taga komai aciki komawa tayi da sauri kunna gas tayi ta haɗa masu ta zuba cikin flaks tahaɗa da kofi ta dauka ta kai musu,tana ajiwa tamiƙe jiki na kyarma ta nufi fita daga ɗakin"ina zaki bayan kin gane mana sirri  saura kaɗan Aisha ta saki zawo yanda cikin ta yamurɗa ganin yanda ta ruɗe yasa suka kwashe da dariya dukkan su Alh shehu yana nunata yace"kalli fuskarta jeki wasa muke miki ya sunan ki?saboda yanda ta ruɗe batasan sanda tace izawaka'a ba sabida tsaɓan ruɗewa tana fita a ɗakin da gudu,bayan fitan ta Alh sunusu ko me yatuna oho yamiƙe tsaye kaman wanda aka mitsina yace"kai ina da tantama akan wannan yarinyar izawaƙa'a take ko ya?gudu gudu sauri sauri yamiƙe yabiyo bayan ta amma bega kowa ba harde wajen taron yan matan yashiga yana kiran"izawaƙa'a da babban murya ita ko Aisha sai sake lafewa take bayan anty malika.


ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now