Chapter 3

43 2 0
                                    

*🪷 DARAJAR ƘWARYA🪷*

       
           _Mom Islam_

Page 3

A hankali take tafiya har ta ƙaraso gurinsa, cikin nutsuwa ta ajiye, kafin ta kalli brown ɗin ƙwayar idonsa, sai kuma tayi saurin kawar da kai, zata juya  ya ɗaga farfesun ya watsa mata, a zuciye ta juyo tare da yi masa wani mugun kallo, cikin gadara yake cewa "hii ko akwai abinda zaki iya yi?" tabbas faɗa ba halinta bane, hasali ma ko cacar baki ake yi takan tashi a gurin, yau kuma ta kasance rana mafi tozarci a rayuwarta da wani banza ya tozartata, bata saurareshi ba ta wuce tana tattare mayafin jikinta dan ya ɓaci da miyar romo, Allah ne ya taimaketa bai shige mata ido ba, bata bari Lami ta ga halin da take ciki ba, da sauri tasa omo ta ɗauraye mayafin kafin tazo ta shanya shi a igiya, ɗaya daga cikin ƴan matan da suke aiki a gurin ta taso tazo kusa da inda Haseena take zaune, murya ƙasa-ƙasa tace "ni sunana Suhaima, dalilin zuwana nan ina hannun matar babanmu ne, tana tsangwamata ga yawon talla Allah yayiwa mahaifiyata rasuwa tun bansan kaina ba, sannan na kasance mai zuciya, matar babanmu da kanta ta tambayi Hajiya Lami maganar aiki, nikuma na amince domin ba son tallah nakeyi ba" Suhaima taja dogon numfashi kafin tace "kinsan mai yasa na fara baki tsakuren labarina?" Haseena ta girgiza kai, Suhaima tayi murmishi kafin tace "zuwana gurin an na haɗu da ƙalubale iri-iri musamman ga wancan yariman mugu, sannan akwai wata kamar budurwa kamar matar aure, ko ruwan wanke hannu kika kawo mata sai da kwara miki a jiki" Haseena ta zabura kamar mai shirin yin dambe kafin tace "wlhi ƙarya take" babu macen da ta isa ta takani"  Suhaima ta dafa kafaɗar Haseena tana cewa "aiko tunda kikazo aiki dole zakiyi arba da wulaƙanci"  suna cikin magana Lami ta ƙwalawa Haseena kira, Suhaima tace "nidai shawarar da zan baki ki kiyayi yiwa waɗannan mutanen gautsin baki domin kuwa babu wuya sun tozartaki a idanun jama'a"
"Bani aron mayafi, tunda kina nan a zaune" Haseena taja mayafin Suhaima ta wuce kiran da Lami takeyi mata, "gani"  Haseena ta faɗa murya a sanyaye sannan kuma kanta a ƙasa, "Haseena dan Allah kije gurin Yarima ki karɓo min kuɗi yanzu yayi min waya yana can jikin mota" har zatace "to maiyasa bazai kawo Miki ba?" sai ta kawar da zancen ta hanyar cewa "toh", a hankali take tafiya har ta iso gurinsa, yana cikin mota mazaunin driver murfin motar side ɗin da yake yana a buɗe tayi sallama kafin tace "Hajiya ce ta aikoni" sai da yaɗau tsawon wasu mintuna kafin yace "gidanku ba'a koya miki ladabi bane?" Sai da ta ɗan cije lips ɗinta na ƙasa kafin tace "kayi haƙuri ina wuni" harara ya watsa mata kafin ya wurga mata 10k  yana cewa "last time idan na sake zuwa naga jar fuskarnan sai nayi maganinta, ya faɗa yana figar motar kamar zai tashi sama, a hankali ta lumshe idanunta, sam bata buƙatar zubar hawaye a yanzu tafi son ta cimma ƙudurinta akan burin da ta ɗaukarwa zuciyarta, jiki a sanyaye ta koma gurin Lami, kana ta miƙa mata kuɗin, Lami tayi mata Godiya kafin tace "akwai baƙi da suka shigo dan Allah a sallame su" a zuciyarta kuwa cewa take "nifa na gaji bana tunanin zan sake dawowa gobe" a zafafe Lami tace "haba Haseena masu son abinci na jira gayi can sunata masifa, kafin Haseena ta ɗauka ta miƙa musu abincin kowa da nasa,  bayan ta gama ta dawo gurin Suhaima ta miƙa mata mayafin lokacin nata ya bushe ta lulluɓa, dan har yamma tayi, sai da suka kammala gyara ko ina kana suka shi shigigar da kayan ciki, lokacin babu kowa, sannan ƴan matan sukazo yi wa Lami sallama zasu tafi, itakam abin yayi mata ciwo, Sbda idan ba ƙarya idanunta sukayi mata ba, ɗari shida ne taga an miƙawa ko wacce, lokacin da ake kiran sallahar magriba sannan suka tari mashin suka koma gida.
Washe gari da safe, ma sai da ya sake sussukarta sannan ta barshi zuwa gurin aiki, sai ƙarfe 7:am ta fito haɗa breakfast ta samu Aasma tayi komai ta gama, cikin nuna rashin damuwa tace "anty ashe har kin kammala?" eh wlhi na gama" Aasma ta faɗa tana goge su Tv da fridge, ko irin cewa "anty zomuci, a'a batayi ba, ta wuce dining ta fara cin abinci, Farha da Ayra suka fito cikin shirin tafiya school, zama sukayi a dining suna kumbure-kumbure Hadeeyya tace "ah yarana meke faruwa haka?" Ayra tayi shiru batace komai ba, haka itama Farha, sai lokacin da Aasma ta iso dining ɗin, ga mamakinta sai taga plate biyu anci abinci a ciki, tana buɗe food flaks taga wayam abincin saura kaɗan, Aasma ta sauke ajiyar zuciya Kafin tace "Hadeeyya waye ya cinye abinci?"
"Anty naga kowa ya gama cine shine naci"
Cike da mamaki, Aasma tace"shine har plate biyu" Hadeeyya tayi shiru, Ayra ta miƙe a zuciye kana ta danna number dadynsu a wayar tafi da gidanka, yana ɗagawa cikin shagoɓa tace "Dady kaga anyi momy tayi mana breakfast gashi munyi latti amma ta cinye abinci" kasancewarsa mai faɗa sannan baya son yaga yaransa sun wulaƙanta yace "ina Hadeeyya?"  Ayra ta turo baki kafin ta ɗago wayar tafi da gidanka ta ajiye a kan dining ɗin kafin ta miƙa mata tace "gashi Dady yace a baki" sai da ta juya idanu Aasma na tsaye riƙe da ƙugu kafin tace " Honey nayi zaton kowa ya gama breakfast ne" rai a ɓace yace "kafin ranki ya ɓaci kiyi gaggawar shiga kitchen ki ɗora musu abinci"  rai a ɓace ta ajiye tana mita, a gurin tabar wayar kana ta wuce bedroom ɗinta, Ayra da Farha suka kalli momyn nasu a shagoɓe Farha tace "momy dan Allah ko indomie ne ki dafa mana" Aasma tace "wlhi a yanzu bazan sake shiga kitchen ba, inhar zaku shiga ga hanya nan, tun ƙarfe huɗu na farka har yanzu Ban Koma na kwanta ba" Aasma tana faɗar haka ta wuce bedroom ɗinta rai a ɓace" Farha dole ta shiga kitchen ta soya ƙwai sai ruwan shayi da suka sha, ko sallama basuyiwa mutanen gidan ba suka wuce, suna zuwa parking space driver yace "aiko saura kaɗan kuyi latti, suka shiga backside ya jasu zuwa makaranta,
Ƙarfe 2:30pm Alhaji Ibrahim Sagir yayi horn a bakin get, mai gadi ya buɗe masa yana yi masa sannu da dawowa, cike da fara'a ya amsa kana yayi parking a inda ake ajiyar motoci, kana ya fito tare da ɗauko ledar da ya siyo su fruit, da sauri mai gadin yazo ya karɓa kana ya shiga dashi ciki, sai da mai gadin yayi sallama kafin ya mikawa Hadeeyya dake zaune a parlon ledar kafin ya fito, lokacin Alhaji Ibrahim Sagir yake shiga, sallamarsa ce ya sanyata tahowa da gudu zata rungumeshi, cikin zafin rai ya kauce murya sama-sama yake faɗa yana cewa "idan banda ke daƙiƙiya bace, meyasa zaki cinye abinci baki bawa yarana ba?" ta ɗauka faɗan nasa ba irin gaske nan bane ta taho tana cewa "nifa banyi tunanin babu wanda yaci ba, tunda abincin babu yawa" Alhji Ibrahim ya wanka mata mari, zatayi magana ya nuna ta da yatsansa cikin tsananin ɓacin rai yace "nayi nadamar asarar kuɗina da nasa na auroki ashe kashemin yara kikeson yi? me amfanin nemana idan har yarana bazasu ci su ƙoshi ba?" riƙe da kumatu tana huci tace "wlhi zakasan me ka mara yau sai kaga masifa a tare dakai" tai kukan kura ta kamo gabansa ta riƙe kam, hakan yayi daidai da shigowar su Ayra da Farha da gudu Ayra ta wanka mata Mari, ta sake da sauri, tana juyowa farha itama ta wanka mata Mari, numfashinsa na neman ɗaukewa yace "na sakeki bana son ƙara ganinki muguwa jahila"  ta bugi ƙirji tana cewa "ni ka saka, wlhi sai na ɗauki mataki, idan banda ƙaddara mezai kaini aurenka, talakan banza wanda ba'aci a ƙoshi a gidansa" sam baya iya buɗe ido bare yasan abinda take cewa "Ayra da Farha sukayi gudu zuwa kitchen, Farha ta ɗauko muciya Ayra ta ɗauko sanda, lokacin Hadeeyya ta matso kusa dashi tana neman shaƙe masa wuya duka suka bubuga mata, bugun da Aasma taji ne yasa ta taso da gudu, har tana rasa hanyar fitowa, batasan me ake yi ba, tunda tana kan sallahya tana karatun Alkur'ani, tana zuwa ta gansu a sunkuye gurin dadynsu, ita kuma Hadeeyya tana can a yashe kamar gawa, Aasma ta ƙaraso da gudu tana cewa "me kuka aikata?" Bakin Farha na rawa hawaye na zuba tace "Mo...mo....mi....mi...wlhi any ce" sai kuma ta fashe da kuka, Aasma tace "ki gayamin meke faruwa Farha?" Sai da tayi ƙoƙarin tare kukan da yazo mata kafin tace "anty ce ta riƙe gaban Dady ta murɗe momy mu kaishi asibiti ko mutuwa yayi" Aasma ta fara ja da baya tare da zaro ido, tasani duk abinda akace Hadeeyya ta aikata zata iya, sai dai wannan yafi na ko wanne lokaci muni, tunda ga dadynnan a kwance idanuwansa a kakkafe, kafin ta juya gurin Hadeeyya tace "ita kuma me ya sameta" Ayra da jikinta keta rawa da abin duka a hannunta, Farha ce tace "dukanta mukayi" cikin faɗa da tashin hankali Aasma tace "kuna nufin kisan kai zakuyi mana a cikin gida?" dukkansu suka sunkuyar da kansu ƙasa, cikin sauri Aasma ta ɗauko wayarta ta danna number family doctornsu, yana ɗagawa tace "dan Allah yazo gidansu babu lafiya" kasancewar ba aikin yake yiba aiyukan sunyi masa sauƙi, ya shiga motarsa mintuna ƙalilan sai gashi ya iso, da sallama ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shigo kana ya zube a inda yaga Dady a kwance, cikin yanayi na tashin hankali ya kalli Aasma dake kuka tana sanye da hijabi yace "Hajiya ya akayi kuka bari hakan ta faru" Aasma da ta gama mayar masa da abubuwan da suka faru, ta ƙara da cewar, "wlhi doctor ina ɗaki kawai ina fitowa na gansu a zube" doctor yace "gaskiya dukkansu sai an kaisu hospital babu abinda zamu iya yi anan" cikin amincewar Aasma doctor ya tafi dasu asibiti, Ayra ce ta bisu kasancewar itace babba, kafin Aasma ɗin ta ɗauki kayan tea da ruwa a flaks tazo parking space tayiwa driver magana ya wuce da ita Diza hospital, a mota driver yake tambayarta waye babu lafiya?" Aasma take sanar masa da cewar "Dady da Anty ne babu lafiya" yayi musu fatan samun sauƙi har suka iso asibitin, bayan drivern yayi parking ta fito da sauri dan tama mance da kayan tea ɗin, drivern ne yabi bayanta da gudu yana bin duk wata hanya da tabi, har suka shigo office ɗin asibitin, daga nan ne aka nuna mata inda aka kwantar da Anty dan ance mata jikin Dady ya tsananta, babu halin ta shiga ta ganshi, dole ta haƙura aka nuna mata inda aka kwantar da antyn ta buɗe ƙofar ta shiga, saninta tayi idonta biyu amma babu kowa a gurinta, abin ya bata mamaki a zuciyarta tace "ina farha???....!
Domin magana da marubuciyar 08141799224

DARAJAR ƘWARYAOn viuen les histories. Descobreix ara