Chapter2

40 1 0
                                    

*🪷 DARAJAR ƘWARYA🪷*


_Mom Islam_

Page 3-4

Kiraye-kirayen sallahar da yaji ne yasa ya tashi zaune, tare da ƙarewa ɗakin da suke ciki kallo, tunowar da yayi wani mutumi yace masa yazo ya kwashe ne yasa ya miƙe zumbur, tare da ɗaukar buta ya buɗe ƙofa kana ya nufi banɗaki, sai da yayi alwalah kafin ya taho ya ajiye butar, daga bakin ƙofa yake cewa "Haseena..Haseena" a tsorace ta farka kana tayi tsaki sannan ta tashi zaune tace "gani" sai da ya ɗan shigo kafin yace "zan je in kwashewa wani mutumi shara ƙila ma samu kuɗin karin kumallo" komawa tayi ta kwanta, yana ce mata anayin sallah kana ya wuce.

Tafiyarsa keda wuya ta miƙe zaune tare da yin tagumi tana neman mafitar da zata dace da rayuwarta, a hankali tayi murmishi tare da miƙewa tsaye ta shiga toilet, bayan ta fito tayi alwalah kana ta wuce ɗaki, gyara zaman buhun tayi tare da buɗe zip na jakarta ta ɗauko hijabi kana kabbara sallaha, tana idarwa ta dinga kwararo adu'oi, jin hayaniyar aikace-aikace na mutan gidanne yasa ta ɗauko man shafawa na ƙaramin kuɗi, ta shafa a fuskarta da hannayenta sai ƙafafunta, miƙewa tsaye tayi ta buɗe labulen ɗakin nata tare da leƙa mutanen gidan, "ina kwanan ku" Haseena ta faɗa tana daga bakin ƙofa, abin ya matuƙar basu mamaki, Lami me gari tace "lafiya Haseena da fatan kin tashi lafiya?" kafin mutanen gidan sukaci gaba da amsawa, sai da ta ɗanyi jimm kafin tace "Lami ko zaki fita gurin abincinki yau?" Lami ta jinjina kai kafin tace "mezai hana ni fita? ai fita ta zamo dole" Lami ta faɗa tana gyara zaman tukunyar miya dake kan wuta, Zainabu me kunun Zaƙi tana daga bakin ƙofarta tace "Haseena manya sautu zaki bayar kenan?" Haseena ta girgiza kai kafin tace"ina ruwanki" Lami tace "gaya mata dai Zainabu uwar kankamba" 🤭 nafa mance takwaratace.
Sai da Lami ta kammala haɗa abubuwan da zata tafi dasu, harda garin masarar da take siyarwa kana ta shiga ɗaki ta ɗauko kwandon sosan wanka ta wuce banɗaki da bokiti mai ɗauke da ruwa a ciki, ba wani daɗewa tayi ba sai gata ta fito, ta ajiye bokitin a ƙofar ɗakinta kana ta shige ɗaki, ɗakin nata ya kasance cike da shirgi, nan jakunkunan kaya can buhun gari can doguwar kujera me zaman mutum uku, daga can bakin ƙofa randa ce ɗakin ma ciki ɗaya ne, daga can jikin bango kuma gadone ne me rumfa, da sallama ta shiga ɗakin kafin ta ɗauko abincin da ta zubawa Haseena wanda ta ajiye akan randa, ta fito tasa takalmi ta nufi ɗakin Haseena, sai da Lami tayi sallama kafin tace "babu kowa?" Eh ki shigo" Haseena ta faɗa tana gyara ɗaurin ɗankwalin kayan da ta sauya, Lami ta cire takalmi ta shigo tana cewa "Haseena iyayen kwalliya amma gashi Allah ya haɗaki da miji marar hali" Haseena tayi murmishi kafin tace "ba fa mijina bane" Lami ta riƙe baki cike da mamaki tace "to meye silar haɗuwarku?" shiru Haseena tayi kafin tace "dama inason idan zaki fita in dinga taimaka miki gurin siyar da abinci kina biyana, inason tara kuɗin tafiya garinmu" tunda taga kamar Haseena bata son yawan tambaya, sai tace "amma ki nemi izinin mijinki, kinga ni anjima zan tashi a gidannan saboda ya matsamin da maganar kuɗin haya, me gidan an bashi da mutunci ko laɗan" Haseena ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta tunanin su kenan ma masu sana'a, ina ga ita da bata juya biyar ta dawo goma, tabbas dole ta nemi mafita kafin me gidan yazo ya tayar dasu cikin tijara"
Amsar Lami take jira, hakan yasa ta kalli Lami,
"Naji zaki bini, amma kina ganin zaki iya miƙawa mutane abinci maza?"
"Inhar zan samu kuɗi zan iya wlhi zan iya"
Ta faɗa tana gyaɗa kai.
Lami tace "to shikenan barin ƙarasa shiryawa kici abinci, sai dai ina tsoron kar mijinki ya shigo ya kama faɗa" cike dajin haushin maganar Tata tace "na gaya miki ba mijina bane" Lami tace "to jirani Zanyi miki magana"
Bayan fitar Lami ta buɗe abincin kana ta jingina da jikin bango, a zuciyarta tace "gaskiya Lami mutum ce, ko garinmu na koma bazan mance da ita ba, kaf gidan an itace zata bani abincin dare safe, da ranan ma dan bata wuni a gida ne, tana cikin cin abinci ta tuno da wasiyyar mahaifinta me tsananin karya mata zuciya, a hankali ta lumshe idanunta kana ta buɗesu sannan ta ci gaba da cin abincin, ga mamakinta ta cinye duka, ta ɗauki yankan naman guda ɗaya ta sanya a baki, kana ta miƙe hannunta riƙe da mudubi tana kallon fuskarta, atamfa ce a jikinta super Holland sai ɗankunnen kunnenta shima me tsada, sannan takaminta marar tudu shima ba na ƙaramin kuɗi bane, man da take shafawa ne bazai wuce 300 ba, sai da ta gyara zaman mayafinta kafin ta nufi gurin Lami ta miƙa mata robar tana godiya, lokacin Lami ta fito sanye da doguwar riga ba wata sabuwa bace, da kaga rigar zaka san taji jiki" horn ɗin da me mashin keyi daga can bakin ƙofa ne yasa Lami tace "Haseena ɗauki wannan bokitin kibi Tanimu nima gani nan" kamar inda Lami ɗin ta gaya mata hakan tayi, bayan ta ajiye bokitin a gaban me mashin ɗin ta haye tana adu'a, sam yanzu bata tsoron haɗuwarta da Abdul-Jawwad ko kaɗan, suna isowa Tifa Gareji, me mashin ya sauketa a gaban shagon Lami me gari ta sauka tare da sauke bokitin sannan ta wuce kan wani benci ta zauna kasancewar shagon a kulle yake, bata wani jima ba mashin ɗin su Lami ya iso, bayan ta sauka ta miƙa wa Haseena mukulli kana tace "anjima da yamma yazo tana da saƙo, bayan Haseena ta buɗe ƙofar ta miƙawa Lami key ɗin, tare da ɗaukar wani abun goge-goge da ta gani, sai da ta goge ko ina kana ta ɗauki tsintsiya ta fara shara, lokacin Lami tasa kaskon suyar waina gefe kuma kular shinkafa ce a ajiye sai miya a tukunya, wasu ƴan mata guda biyu suka sauka akan mashin suka taho suna gaishe da Lami, amsawa tayi cike da fara'a kafin tace "yau kun makara gashi kun samu wata ƙawa" ƴan matan suka leƙa ciki suna murmishi kafin suka miƙa wa Haseena hannu suka gaisa, ko wacce ta kama abinda tasan tanayi,
Gurin cin abincin a tsaftace yake, gini ne na bulon siminti sai tayel a ƙasan, sannan windown glass sai fararen labulaye masu ado sannan kuma shara-shara, kujerun roba ne jere a gurin sai table shima na roba, a taƙaice dai gurin bashi da makusa ko kaɗan, ƙarfe 8:am mutane manya-manyan masu kuɗi suka fara parking motarsu a gefen gidan abincin, gidan abincin Lami me gari yayi suna a guraren masu motoci Masu mashina da sauran masu zirga-zirga a gari, har mata wanda basa ra'ayin girki sukanzo da motarsu harma da yaransu, sabda tsaftace girki da duk wani abu da zai saka masu cin abincinta su gujeta sannan sai da ta nemi maganin kasuwa a gurin malamai,
Lokacin da su Haseena suka kammala gyara gurin suka feshe ko ina da room freshener me sanyin ƙamshi, kana ko wacce ta fara kula da masu shigowa,
Wata hadaɗɗiyar mota ce tayi parking, kana kallon motar zaka san mamallakin motar abin hannu sun zauna masa, zaune yake a mazaunin driver idanuwansa sanye cikin baƙin gilashi, yayinda fuskarsa ta kasance fara sol sai kace Balarabe, yana da dogon hanci, bugu da ƙari yana da faffaɗan ƙirji, ga hannayensa da suka wani murɗe, riga ce t-shirt a jikinsa fara sal sai blue jeans wanda daga gwaiwarsa a farfashe yake, hakanne zai nunar da ɗan gaye ne, ƙafafunsa sanye suke cikin canvas fari me tsada, Prince Anoush kenan yaro ɗan sarki jikan sarki, yaro matashi me ji da kyau kuɗi izza sarauta kai kace shine sarkin, amma abin da zai baka mamaki gidan cin abincin Lami me gari yake zuwa cin abinci, a hankali ya zuro da ƙafafunsa waje, kafin ya fito da kansa sannan ya fito gaba ɗaya, babbar wayarsa dake ringing ya ɗaga tare da karawa a kunnesa kafin yace "ina jinki Please inada wani uzuri yanzu zuwa anjima zan kiraki" sai da ya furzar da huci kafin ya ƙarasa ciki, kamar ba shine me tamke fuska ba, yace "Hajiya da fatan komai ya kammala" bakin Hajiya Lami me gari a washe tace "insha Allah yarona ka shiga kawai" dama idan yazo a can gefen harabar gurin ake ajiye masa table da kujeru uku, ba a cikin mutanen yake zama ba, kasancewar abincin da takeyi kala-kala ne, dan sukai wajen kala Goma shinkafa da miya waina farfesun Ganda soyayyen dankalin turawa burabisko da miyar ganye, funkaso da sauran su, a haɗaɗen plate aka zuba masa funkaso sai wani ɗan dinner set da aka zuba miyar funkaso ɗin taji ganda sai ruwan wanke hannu da abin goge hannu, bayan ta gama ajiye masa abincin ta juya zata wuce, cikin Cold voice ɗinsa me daɗin sauraro yace "bakijiba" sam bata kawo da ita yake ba har sai da ya ɗaga murya yace "hii" ta juyo tare da jan dogon tsaki kafin taci gaba da tafiya har ta kawo gurin Lami, wani irin ƙululun abu ne yaji ya tokareshi, a zuciyarsa yana cewa "kamar ni Prince Anoush har an haifi yarinyar da zata tozartani?" Haseena jeki kaiwa Prince wancan farfesun tun ɗazu yayi magana Allah yasa be zuciya ba" mamaki ya kama Haseena ta ɗauki farfesun cikin nutsuwa ta nufi gurinsa....!
#Love
#Romantic
#Funny
#Destiny
Cakwakiyar soyayya me sanyi hhh Free pages yana iya ƙarewa a ko wanne time

08141799224
Mom Islam

DARAJAR ƘWARYAWhere stories live. Discover now