Chapter 1

105 1 0
                                    

*🪷 DARAJAR ƘWARYA🪷*


_Mom Islam_

Page 1-2

Safiyar juma'a ta kasance safiya ce mai cike da ni'ima, garin ya haɗa hadari sosai yayinda yawancin mutanen garin masaƙa ke sa rai da zubar ruwan sama,
Gidane babba, wanda yake cike da ƴan haya, kowacce mata tana haramar sanya abin tarar ruwa banda Haseena, wacce take ɗaki a takure sai kuka take, daga can tsakar gida Lami me gari tace "Haseena bazaki taso ki tari ruwan ba, kinsan da cewar idan ruwan sama ya ɗauke bamu da inda zamu samu ruwa akan lokaci?" kamar Lami me gari ta sake tunzurata ta sake fashewa da kuka tana gyara kitson kanta da aka yishi da zaren lilo, tashi ɗaya ruwan ya sakko da ƙarfinsa dan har da feshi, a raɓe Lami me gari taho har tana jiƙewa ta bubuga ƙofar ɗakin Haseena tana cewa "baiwar Allah lafiyanki kuwa rabonki da fitowa tsakar gida tun jiya?" Zainabu me kunun Zaƙi tace "kema da cusa kai a abinda babu ruwanki me ya kaiki shigar mata bayan kinata yi mata magana taƙi amsa miki?, ke da kikeda uzurin tarar ruwan ai sai ki tara tunda ba ƙanwar gyatuma bace" Lami me gari ta harari Zainabu me kunun Zaƙi kafin tace "kinga babu ruwanki, kekuma ƴar sa ido, haƙƙinmu ne mu kula da ita a matsayinmu na ƴan gida ɗaya" ganin Haseena taki buɗe ƙofa yasa Lami me gari raɓewa ta koma gurin tarar ruwanta, zuciyarta cike da tararradin lafiya kuwa Haseena take?"
Mata biyar ne a gidan, sannan ko wacce tana sana'a, Zainabu tanayin kunun zaƙi, Lami kuma tana siyarda gari, Lubabatu tana siyar da Kamu, Dije kuma tana siyarda kayan miya, Haseena kam bata sana'ar komai, tsakar gidan a farfashe yake dan babu simintin kirki, ko wane ɗaki ledar tsakar ɗaki ne a ciki, banda ɗakin Haseena da ya kasance daga ita sai jakar kayanta, da farin buhun masara wanda take zaune akai, daga can gefe kuma akwai bokitin fenti babba sai buta shikenan abinda ke a cikin ɗakin nata, safiya nayi ko wacce zata kama sana'arta me fita dashi zuwa tasha ko gareji duk suna fita dashi, haka zasu daɗe subar gidan abar Haseena ita kaɗai.
Lokacin da ruwan saman ya ɗauke gari yayi duhu, sbda an jima anayi gashi har yamma tayi, gabaki ɗaya ƙasa ta jiƙe tayi sanyi, dalilin da yasa kowa zaka gansa sanye da rigar sanyi, kiran sallahar Magriba yayi daidai da shigowar wani matashin saurayi, fari dogo bakinsa na kewaye da gashin baki yayinda idanuwansa suka kasance madai-daita, yana da tsayi ba sosai ba, yana sanye da riga t-shirt baƙa sai wandon jeans fari dogo amma ya fara yin datti, kowacce mace ta shige ɗaki hakan ya bashi damar bubbuga ƙofar ɗakin Haseena yana cewa "Haseena Please open the door" sai da taɗau tsawon lokaci kafin ta miƙe taje ta buɗe masa tana gyara zaman ɗankwalin kanta, sai da ta tabbatar ya shigo kafin ta tura ƙofa ta sake danna saƙata, sannan ta koma kan buhu ta zauna zuciyarta babu daɗi sam, cikin sassanyar murya yace "Haseena dan Allah ki kwantar da hankalinki me yasa kike abu kamar bamu yarda da junanmu ba?" Murya irin ta wacce tayi kuka ta gaji tace "nikam bazan iya zaman nan ba, dan Allah ka mayar dani garinmu wlhi bazan iya ba" ta faɗa tana fashewa da matsanancin kuka me tsuma zuciya, "zaki iya Haseena idan na mayar dake meye ribarmu a ciki, haba Haseena ya kikeyin abu kamar ba wayayya ba?" ya ciro baƙar leda me ɗauke da ƙosai a ciki ya miƙa mata, kallon ledar tayi kana ta kawar da kanta, kafin tace "Abdul-Jawwad karka manta rabona da cin abinci tun da safe, ban ƙara sanya komai a bakina ba sai yanzu da ka dawo kuma ka kawomin ƙosai na nera hamsin?" be kula da maganar da take yi ba, ya kawar da zancen yace "dan Allah kici ko zan samu zuciyata ta samu sassauci" tunzurar da zuciyarta tayi ne ya sanya Haseena ta wurga masa ledar ƙosan tana ce masa, haba dan Allah kasan bazaka iya dani ba, meyasa zaka dinga barina da yunwa wlhi sai na koma garinmu".
Ta faɗa tana ƙare maganar da galla masa harara.
Kamar koda wane lokaci watan Agusta ya kasance cikin ruwa ko yayyafi, tunda taga an fara yayyafi ta fara rawa tana cewa "wallahi kyan ruwannan honey ya dawo mu shige daga ɗaki, ta kalli matar dake zaune saman kujera tana rawa tace "Aasma ki siyar mana da kwanan nan Please ko nawa kike buƙata zan baki" Aasma tayi murmishi kafin tace "karki damu indai kwana ne na bar miki nayau asha daɗi lafiya.
Gidane babba me kyau da tsari, mamallakin gidan sunansa Alhaji Ibrahim Sagir, babban ɗan kasuwa ne sannan Allah ya azurtashi da arziƙi naban mamaki, idan ka shiga gidansa sai ka rantse ba talauci ake yi ba, duba da inda ake waja-waja da komai, matansa biyu, yaransa biyu, Aasma itace babba, sai Hadeeyya itace amarya, yaran biyun duka na Aasma ne, dukkansu mata, Ayra da Farha, Ayra itace babba shekararta goma sha uku, sai Farha ita kuma shekararta bakwai, tun daga aihuwarsu aihuwa ta tsaya mata badan taso ba, Hadeeyya bata taɓa koda ɓari ba, sbda ta faɗa ta ƙara ta ce koda wasa bazata taɓa bari ciki ya shige ta ba, bare har Alhaji ya fara sauya mata sheƙa, gara kullum ya dinga jinta zam-zam, hakan yasa da taimakonsa take tazarar iyali, ga baki ɗaya harabar gidan mamaye yake da intaloc yayinda gefen da ya zagaye gidan duk flawoyi masu kyau, daga can gefe kuwa rumfa ce da ake ajiyar motoci, duk da Alhajin ya fita, akwai ragowar motoci guda huɗi, sababbi amma alamomi sun nuna ana shigarsu, babban parlo ne mai kyau, yana ɗauke da kujeru kyawawa kalar Brown sai carpet na tsakar ɗaki shikuma yanada flowers me kalar Brown da fari, sannan tayel ɗin parlon ya kasance dark milk color, sai ƙaton Tv dake manne a jikin bango, fentin gidan gabaki ɗayansa milk color ne, me maiƙo, daga can nesa kamar zaka shiga saitin ɗakunan mutanen gidan labule ya raba me kyau, sai fridge guda biyu da frizer da kuma ƙaramin fridge, ɗakuna biyar ne a ciki, ɗakin Aasma shine a farko, sannan na Alhaji Ibrahim Sagir, sai na Hadeeyya, sannan nasu Farha, sai ragowar ɗayan na baƙi, sai kitchen a gefe, ɗayan ba wani girma ne dashi ba amma shine store cike yake da kayan abinci, amma sam basa cin masara,
Miƙewa Aasma tayi tare da mayar da kujerar kitchen tana cewa "na jera abinci a dining banajin zanci sbda bana jin daɗin jikina, cikin rawar kai Hadeeyya tace "laha karki damu zan kula da yaran Allah ya baki lafiya" Aasma tace "Amin kana ta shige ciki" Alkur'ani mai girma ta ɗauka tare da fara karatu tun daga alhamdu har zuwa sama, sakamakon lokacin anyi sallahar isha'i dukansu sunyi, bayan ta idar da karatun ta shiga toilet ta sake ɗauro alwalah ta kwanta bayan tayi adu'ar kwanciya barci,
10:11pm na dare, ƙugin motarsa ne ya sanyata sake mulke wuyanta da zafafan turaruka, sannan ta sanya riga da wando, wandon gajere ne yayinda rigar ta kasance me shara-shara, sai da tasa ƙaton hijabi kana ta shiga bedroom ɗinsu Ayra, bayan tayi sallama tace "akwai abincinku a dining"
"Toh anty"
Suka amsa mata suna ci gaba da danne-danne a waya, ta ɗauki na Alhaji Ibrahim Sagir ta shige dashi bedroom ɗinta, lokacin da taji sallamarsa a parlon tai saurin sake feshe ko ina da turare, kai tsaye ɗakin Aasma ya wuce, lokacin har tayi barci tana lulluɓe cikin bargo, murya ƙasa-ƙasa yace "Aasma har kinyi barci?"
Cikin sanyin murya da kuma yanayi na barci tace "ai munyi magana da Hadeeyya tace in bar mata kai nikuma na amince" Alhaji Ibrahim Sagir yace "haba Aasma meyasa kikeyin abu kamar ba mace ba, shin kina ganin ita zata iya ɗaukar kwananta ta baki?" ni nayi dan Allah ne, tunda na riga da nayi mata magana kaje kawai" ta faɗa tana sake lulluɓe jikinta, haushi ne ya kamashi wanda yasa be sake yi mata magana ba, ya fice kai tsaye ya leƙa ɗakinsu Ayra yaga har sun yi barci, ya rufo musu ƙofa kana ya buɗe ɗakin Hadeeyya da sallama ya shiga, da sauri ta rungumeshi tana yi masa kiss ta ko ina a fuskarsa, kafin ta riƙe hannunsa ta zaunar kan gado, cikin salo na kissa tace "Barka da dawowa mijina farincikina, tashi ɗaya yaji duk wani ɓacin ran da yake ciki ya yaye, ta kawo masa ruwan gora me sanyi tare da janyo masa table me ɗauke da abinci, Tuwon shinkafa Aasma tayi miyar wake wace taji naman kaza, kasancewar bataci nata ba, tace "gaskiya my honey cin soyayya zamuyi a baki zan baka" yayi murmishi shikam rawar kanta yana burgeshi sometimes kuma bata da daɗin sha'ani, a tare sukaci abincin, kasancewar da hannu yake ci, ta ajiye masa ruwan wanke hannu bayan ya gama takai ɗan ƙaramin kitchen ɗin da akayi wa kowanne ɗaki, ba wasu kayan abinci ne a ciki ba, iya kayan tea ne, ta wanke kana ta dawo ta zauna kusa dashi tana ɓalle masa botir na rigarsa, a hankali ta raɗa masa, dama dai ruwan sama be jiƙamin kai ba?" shima yayi mata kamar inda tayi masa yace "eh" a hankali ya matso da ita kusa dashi yana jifanta da wani irin kallo wanda ita kaɗai tasan ma'anarsa, ruwan da ake tsugawa ne yasa ta sake ƙamƙameshi tare da kai bakinta cikin kunnensa, harshenta ta zura tana wasa dashi a hankali ya fara zamewa yana wani irin surutai, kan kace me ta gama rikitashi da salonta, cikin hikima irin tasa ya dinga rage mata komai na jikinta har ya cire nasa, sam taƙi bari ya kasance ta a lokacin har sai da sukayi ta romance sosai,
Ƙarfe 1:am na dare Aasma ta farka tare da kwararo adu'oi sannan ta yaye bargon da ta lulluɓa ta sakko da ƙafafunta ƙasa kafin ta shiga toilet bakinta ɗauke da adu'a, alwalah tayi ta fito kana ta shimfiɗa sallahya ta kabbara sallah, sai da tayi raka'a huɗu ko wacce biyu da sallama kafin ta ɗaga hannunta tana adu'ar neman kusanci ga mahalincinta, ta daɗe tana yiwa yaranta adu'a daga ƙarshe ta shafa, kana ta ɗauko alƙur'ani me girma ta fara rera karatu cikin sanyin murya, ta dade tana karatun daga ƙarshe ta rufe da adu'a kana ta shafa ta mayar da Alkur'anin mazauninsa kafin ta shafa adu'ar ta yaye hijabin dake sanye a jikinta, ta koma kan gado ta kwanta zuciyarta wasai, daga nan barci me daɗi ya sake ɗaukarta.
Washe, ɗaukar ƙosan da ta miƙo masa yayi kana ya ajiye akan murfin robar fenti, kana ya shimfiɗa buhu can gefe ya kwanta, ita ma ta kwanta tare da lulluɓe ƙafafunta da ɗankwalin kayan jikinta, cizon da sauro ya bashi ne yakai duka a ƙafarsa haka suka kwanta har wayewar gari...!
Shin ya kukaji salon labarin?

DARAJAR ƘWARYAWhere stories live. Discover now