Yau kwananta ne Ummi sam ba ta so hakan ba shiru tayi kawai Zainab din ta juya ,d'aki ta koma Ummin ta Yi wanka ta shirya cikin doguwar riga atampa ta Yi light kwalliya tana fitowa sai ta ji tsayawar motarshi Zainab din kamar Jira ta ke a parlourn ya isketa daman haka ta ke so fuska a sake ya karaso Ummi tana kallon hannunsa da leda ya mika mata tana murmushi sannu da dawowa Yaya ya gajiya? Ta tambaya tana karba Ummin ta basar kamar ba ta gani ba ta karasa tana sakin fuska "Sannu da dawowa"Ta furta tana mika hannu ya bata jakarsa ya mika mata ta juya ya bi bayan nata bayan ya tambayi jikinta.Da ido ta bisu ta maida kallonta ga ledar Rufaidan da ta sa ya taho  mata ne ta bude tana sha.

    Ummin kuwa ta ajje jakar ganin Yana shirin rage kayan jikinsa yayi saurin iskeshi ta ce zatayi,abinda ba ta taba ba murmushi yayi yana sauke hannayensa ya barta.Rigar ta cire masa abinka da bata saba ba ta ji wani iri dakewa tayi ta Sanya hannunta kan mazugin komai da ta ke kallon fuskarta ya ke tunani  kala kala Koda ta gama ta juya zata ajje kayan ya rikota ta fad'a jikinsa.
  "Bazaki min wankan ba?"

   Dan gefe tayi da ido tana Jin nauyi tunda ba tabawa' tayi ba a zuciyarta ta ke tunanin wannan dama ce dole tana so ta saki ji dashi.Kai ta jinjina "Mu je to".

     Tana jin nauyi yau dai Ummi ta yi 'kuru ta wanke mijinta suka fito ta shirya shi cikin kananan kaya har da kwantar mishi da gashi da brush , Mukhtar wani irin jinsa yake kamar sabon aure wannan gatan kan baya samunsa wani irin kaunarta yaji tana fisgarsa ya kamo hannunta  cikin nasa  yana murzawa.

   "Kullum 'kara dad'a kyau ki ke mene sirrin?" Haka kawai ya ji zuciyarta ta ce masa Ina ma Ummin ke da ciki.

   Murmushi tayi "Yau ba ka nin yunwa ne"Maganarta ta katse masa tunani.

"Ganin ki ya sa na daina ji,madam".

  "Yakamata ka tashi muje tohm ".Ta furta tana murmushi.

  "Mai kika tanadar min haka kike ta so na ci abinci?"

  "Taso kai dai ".

Ta fad'a tana dan jan hannunsa "D'aga ni mana toh".Ya fad'a Yana sakar mata nauyinsa .

Dariya tayi kadan "Ka min nauyi Allah".

"Ni din har nawa nake ai. Kin fini fa ko bakisan kina ta yin  kiba ba?see your cheeks?"

"A a fa Ina fa ma da school?"Tayi dariya.

"Yanzu ba hutu kike ba?"

"Eh dai wai".Ta sake fad'a.

   Tashi yayi tare suka fito suka iske Zainab din tuni ta zo ta zauna tana jiransu ,Ummin ya dan kalla ta dan yi yake 'Tare zamu ci".

  Ya daga gira yau alamar  kuma a fili bai ce komai ba suka zauna dukansu adjacent to him.

  Ummi tayi serving sai faman iyayi Zainab ta ke yi na iya yadda zata zuba mata.Dadewar da sukai ta ke kallansu sai kace me son gano wani abun ,don a kalla sunfi awa kafin su fito ta rasa gane kansu  kwana biyunnan wani mannewa Ummin yake.Sau da dama ta kan Yi tunani Mukhtar din ya fi son Ummi.

   Gyaran murya yayi Yana cewa "Yau wa ce ta tsara mu ci abinci tare haka?"Finally ya tambaya don abin ya burgesa.

  Ummi ta dago ta Kalli Zainab da take shirin amsawa Ummin tayi saurin tare mata numfashi da fadin "Nice ,ni nace yau yakamata muyi dinner tare".Ta fad'a cikin dakiya gefe guda tana gudun kar Zainab ta karyatata , ita kanta Bata San mene yasa tayi karya ba kawai dai ta rasa gane manufar Zainab din akan suggesting cin abincin tare.

 
Murmushi yayi sosai ya nuna ya ji dad'i wani irin abu ya tokare a wuyan Zainab ,lallai ma Umminnan? Ta ke ta nanatawa.A daddare ta gama ci tana kokarin tashi ya ce "Dan tsaya ,time like this ina da albishir gareku".

  Ba shiri ta dawo Zainab Ummin ta bisa da ido tana jiran yayi magana.

  "A cikin satunnan na ke so zamu tattara kayanmu mu koma sabon gidanmu".

  Waro ido Zainab tayi Ummi ta daga gira "Sabon gida?"

  "Yaya Mukhtar gida fa kace , yaushe ka Yi gida? Daman kana gini"

Yadda suke jero tamabyar yasa shi yar dariya "Calm down ,ya kuke mamaki?"

"Eh man ai dole ne Ya Mukhtar yaushe?"

  Gyara zama yayi ya labarta musu a ta'kaice Zainab ta Yi hamdala ta hau zumudi tana tambayarsa hoton gidan yace surprise me sai idan sun je Ummi ta Yi addua sa albarka ta nuna masa tayi murna.Zainab cikeda farinciki ta koma daki ,Ummin bayan sun koma daki kafin kwanciya ta kasa rike abinda ke ranta.

  "Ya Mukhtar ".Ta kirasa ya juya baya ya waiwayo ta Dan gyara murya don son ya fiskanci zancen nata.

"Nasan kayi kokari sosai I am happy Kuma Allah ya Sanya albarka sabon gidannan ,Amma amma Ina ganin me zai hana ka raba mana gida da Zainab?"

  Tashi yayi daga kwance yana kallonta sosai "Sabida me kika ce haka?"

"Ya Mukhtar understand me ,gidannan bashida wata matsala wlh ni sai na zauna ita ta zauna sabon gidan".

A yanzun ya Gane kishi ne irin nata yanzu ya sake tabbatar da ummin tana da kishi.

  Murmushi yayi yana tasowa gunta ya zauna gefe ya na riko hannunta "Ummi ,na fahimta abinda Zaki tunani Amma ni bani da raayin raba muku gida ,bana son raba kan yarana gaskiya gaba ake ji and gidannan sama da kasa ne duk inda kika za'ba Nan zaki zauna Amma wannan gidan Allah ya amfana mun gama zama cikinsa zan bawa Baba mukullinsa ke ba Kya son canji?"

  Kai ta girgiza ta dago ido ta kallesa "Ina so".

"Tohm kin gani ,ko tsoron kishin kike? akwai wata matsala ne bansani ba?"

   Kai tayi saurin girgizawa "To me yasa bakya son zama da ita ,ke fa uwargida ce?"

    Soothing words dinsa da su yayi amfanin Ummin ta hakura har suka kwanta bacci.

★★★

   Tunda Zainab ta ji batun sabon gida hankalinta yaki kwanciya duk ta fad'awa kawaye da Yan uwa sai murna take abinda Bai mata dad'i ba da akace 'kasa zata zauna ba yadda ta so ne.Kafin ranar tashinsu yasa Akai sauka gidan ,kowacce yayi mata furniture sai wannan Wanda kowacce zata Kara a dakunanta ,Ya Abdulbasit Jin haka ya sa ya tura mata da kudi yace Suma ta sauya su tasa sabo Umar da suke Nan sun sukai mata wannan dawainiyar komai nata sabo ta samu hatta kayan kitchen rabinsu sai da ta sake da kudi me tsoka ya turo  mata shiyasa take Jin qaunar Yayan nata duk cikin yan uwan yafi nuna mata gata shikuwa tausayi take basa na rashin yar uwa mace da mahaifiya gashi yayi nisa.Ummi wasai ta ji ta kamar wata amarya ba abinda ya ke damunta ,sun dawo sabon gida suka tsinci kansu sabuwar rayuwa irin kayatuaar gidan ya Basu mamaki gaskiya batayi expecting din gidan haka ba , kodayake tasan Mukhtar din akwai zuciya ba karamin alfahari ta ji ba ,Baba ma yayi murna sosai a yanzun ya sake tabbatar da namiji ya aurawa yarsa gashi baya Jin ana kawo kararta shiyasa hankalinsa ya kwanta  yanzun har waya sukan Yi da Baban tana kiransa shima haka.

   Zainab tun da aka koma gidan wani sabon yanga ta ke ji ,yanzun take sake Jin dadin auren Mukhtar da tayi ashe gata aka mata don da tana jin kila wa  kala ashe dai zata dandani Jin dad'i bakincikinta daya yadda Ummi take shan gata gun Yan uwanta komai bata nema ta rasa.

     **** Tsaye take bakin mirror tana kallon cikinta a budubi , lokaci yayi da zata kawo karshen wannan karyar kar Mukhtar ya Gane don zuwa yanzu yaci ace ya fara tasawa.Tunanin plan dinta take tana sake duba lokacin dawowar Mukhtar din tayi ,kayan jikinta ta sauya zuwa wata doguwar riga milk me dan santsi ta kamata kadan ,yar kwalliya tayi kadan mara nauyi ta shiga ban d'aki tana zame pant dinta ta cire pad dinta cikeda addua kar planing dinta ya tafi ba dai dai ba ta fito tana addua kar tayi staining da wuri kafin ta cin ma burinta.....

🤔Oh ni dije mene hakan da Abu ta ke shirin yi???

  
   *Yan Wattpad am proud of you , honestly comment dinku Yan whattapp bana gani ba kwa gingering dina ehen kusani the more Kuna comment the more Ina Jin zumudin update*

  Dijensy

  

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now