"Kai ka haifeni ya amsa cikin sanyi murya.
"To inde ni na haifeka to kashirya zuwa ba ruwanka da halin da nake ciki abun kunyane gareni ace ɗana ze auri kaman ƴar Alhaji sunusi amma ina da kuɗin nakasa ɗaukan ɗawainiyar komai na barmasa,sannan ita wancan mata taka ban amince da tare warta nan kusa ba,duk da dama ni banwani dauki auren nan a aure ba dan nafi daukansa da auren wucin gadi kokuma auren jingina.

"Alhaji yanzu bakaji kunyan tattauna irin wannan da danka ba,kai da yaka mata kaimasa addu'an Allah yatayashi riƙo amma kake wani zance mara dadin ji da sauraro to wallahi kasa aranka cewa wannan da kakewa fatan auren jingina ko na wucin gadi in sha Allah itace wacce zakayi alfahari da ita gaba,dan wannan ƴar gwal ɗin taku da ubanta ba komai suke yiwa ba sai abun hannun ka ina kyautata zaton akwai abunda wannan mai ido a tsakar kan yakewa bazaka taɓa ganewa ko kayarda ba sai lokaci ya ƙure maka idanma bacci kake ka tashi wallahi ko wannan abunda yafaru dakai bana zargin kowa sai shi tabbas dasaka hannun sa ciki wallahi Allah ko kaffara bazanyi ba,sannan kuma bincike da ake shine ze kara tabbarwa da shidinne da sannu zaka gane bason Allah yake maka ba.

Tunda Ammi ta soma magana yayi saroro yana kallonta ko kiftawa bayayi saida ta dire sannan yasamu zarran cewa"amma ma'arufa bantaɓa sannin ƙiyayyarki da Alhaji sunusi yakai kimasa sharri ba sai yau yana fadin haka mikewa yayi yayi wucewarsa daki.

Hajiya mariyah da kawarta hajia shema ne gurfane gaban wani gajeren mutum mummuna da wagege baki hanci kaman ƙofan kasuwa..bude baki tayi da nufin tamasa bayanin abunda yakawota saurin dakatar da ita yayi da cewa"tun ma kafin kuzo anfaɗamun so kuke yaron nan yanuna musu wani ƙwaya dake gaban sa cike daruwa matso kugani matsowa sukai ai kuwa azabure suka ja baya ganin Ahmad tsaye jinjine jikin mota waya kange a kunnesa yace ko bashine ba.

Saurin amsa masa sukai cikin rawr murya da"wallahi shine"ai kinku mai saukine amma sai kunsamo mana sunan ita matar tasa da kuma ta mahaifiyarsa sai kuma bayan ita mahaifiyarta sa akwai wata ɗaya da ita ke juya uwar yaro bata iya tsalleke maganarta ba.

Ina zuwa tace sannan ta kira wayan mijinta yana dauka tace"Alh wai ya sunan mahaifiyar yaron nan ne dan malam yace sai an samo sunan su sannan aikin zeci,dan jim yayi kaman mai tunani sai can yace"marfu'at ne ina ji"kana tantamane?kode ka tabbata karfa asamu matsala Alh"hakanne ma ita kuma matar tasa kibari zan tambayo badamasi idan yaso ko a waya kyafada masa zuwa gobe"tom ta amsa tana kashe wayan.

Cike da kwarin gwiwa ta faɗawa malamin sunan sannan ta daura da cewa"sunan ita matar tasa zuwa gobe zankira ka ko ta waya idan yaso nasanar dakai"ba matsala yace.

Dan Allah malam aiki mai zafi nakeson ai mun akansu so nake wannan yaron yamace akan yarinyata sannan inason a dasa tsana mai tsanani tsakanin sa da iyayensa shikuma yazama bashi da maganan kowa saita basma duk abunda yasamu da wanda ya mallaka duka ya mallaka mata.

"Wannan shiyafi komai sauki amma kafin sannan duk yanda zakuyi kuyi dan ganin be tare da matarnan tasa sunyi taraiyar ba idan ko ya tare da ita duk aiki da mukai ze karye karshe komai ze koma kanku dan haka ku kiyaye kunisanta shi da duk inda kukasan yarinyar take idan baya ganinta baze taɓa tunawa da ita ba.

Kayan aiki muna bukatan  hantan baƙar karya da huhun cinnaka sai maniyin sauro da sune za haɗa maganin.

"La'ila ha illallahu"yimun shiru yadaka mata wani gigitaccen tsawa dayasa duka dajin amsawa rai a mugun ɓace yacigaba da cewa kinsan da Allahn kika kawo kanki wurin mu"tuba nake ran malam yadaɗe ruɗewa nayi"ki kiyaye gaba dan duk wanda kika gani anan ya kauce hanyane ɓatacce kaɗai kanzo nan.

"Tuba muke baza kara ba suka faɗa kaman zasuyi masa sujuda.

"Yawuce yanzude ku chake kuɗin da zabada dan nemo muku kayan aikinku aikinmu kaman yankan wukane"munsani ran malam yadade amma dan Allah aimana sassauci kar atsuga mana kuɗi dayawa shekara da shekaru muna tare.

"Hakane yanzu de kuɗin kayan da nafaɗa dubu ɗari biyar zaki bada sannan zaki bada dubu ɗari da hamsin kuɗin kafin alkalamin aikinki idan aiki ya kammala saiki cikatomun da dubu hamsin.

Jiki na rawa ta ciro damin kuɗi cikin jakarta ƴan dubu dubu sabbi kar dasu ta ajiye masa daukan kuɗin yayi yana shinshinawa yana babbaƙewa da wani irin dariya mara daɗin sauraro saida ya tsagaita da dariyan sannan ya ɗaga hannun sa sama saiga wani ƙullin magana ya miƙa mata yace duk yanda zakiyi kiyi yau din nan ki tabbata kin bada anzuba masa a abinci ko abin shansu dan yau shine ranarki ɗan tsuku yana kan aiki shi kuma yaron ze zo taron da tawagarsa dan haka amshi nan hanzarta kar asamu matsala kuma duk yanda zakiyi kisa ƴarki ta tambayo sunan matar tasa kutashi kutafi,kufita da baya da baya kutaka a hankula karku taka mana yara suna wasa duk sun tsure baramma hajia shema da bata taɓa zuwa irin wannan wajen ba.

*****
Aisha tunda Ahmad ya fita a ɗakin zaune tayi bakin gadon dafe da kanta yafi minti talatin kafin yasake shigowa ɗakin yanda yabarta haka yashigo yasameta tunma kafin ya karasa shiga dakin yasoma tattare hannun rigarsa kaman mai shirin kaukawa da gefe idon take kallon yanda yake takowa da karfin sa fuskar nan tasa ba alamun rahama a tare da shi take taji cikin ta yasoma kugi kuuuuuuuuu wani kakkauran ƴawu ta haɗiye mukut miƙewa tayi da hanzarin ta dan shiga toilet tama kanta maɓoya saide tana miƙewa taku ɗaya biyu taji anyi sama da ita buɗe bakinta tayi da nufin fasa ihu kaman ko yasan abunda zatayi yayi saurin rufe mata baki da ɗaya hannun sa.

ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now