Da Ameen ya amsa suka fita ,ta leko ta window tana Jin haushi tsoro ta ke ji Allah yasa dai ba ciki bane da Ummin ,don idan cikine planning dinta bazai tafi yadda take so ba.

   Da sake sakennan ta tashi ta shiga bayi tayi wanka ta fito wayarta tayi ruri kawarta ce Saliha makarantarsu daya ajinsu daya.

  "Kawata ,ya kike ".

  "Lafiya lau ,ya an samu abin?".Cewar Zainab

  "Kiran da na kira na miki ne ai ,an samu amma fa kawata da tsada wlh don daga Niger ake kawosu sadidan ne wlh har da na mallaka ,dubu 60k"

   Waro ido Zainab tayi "Haba ,sai kace kudin rago Kai Saliha mene sauki kudin wajena Ba zai Kai ba fa,inba So kike na sayar da gold Dina ba?"

  "Banza ko kin manta kwalliya zata biya kudin sabulu sai fa kin saki jiki kin cire kyashi ,na fada miki suna da guarantee magungunan".

  "Tohm yanzu ya za ai 34k ce a account dina gabadaya"?

  "Ki Saida gold dinki yaso an kwana biyu ki je masa ya 'bata ,that is bayan an kawo miki maganin kin fara using dashi"

Shiru Zainab tayi kafin ta jinjina Kai "Toh ya za ai yaushe Zaki rakani muje kasuwar?"

  "Ko gobe ma ai Zaki shigi school sai mu biya".

"Tohm shikenan ,amma kin San me akwai matsala yanzu suka fita da da ita wai bata da lafiya zasu asibiti shegiyar yarinya duk ta fara sauyawa wlh ,kamar nema take ta janye ya Mukhtar buni buni Yana dakinta yanzun ma tare suka fita".

  "Karki wasu damu maganinnan sadidan ne wlh sai ya raina ta ma indai kika fara amfani da shi tsabar aikin da yake yi".

   Sun dan jima suna waya kafin daga baya sukai sallama ta sanya kaya ta fito kitchen.

"***

A asibiti bayan an yi tests aka tabbatar malaria ce kawai da dan zazzabi aka tabbatar ba ciki a test din da Akai mata har da na pregnancy Amma ba ciki .Maganin aka hado ta da shi suka dawo gida ,sai sannan hankalinta ya kwanta don har ta ji tsoro kar a gane tana shan magunguna Amma me ta tsinci kanta da Jin wani iri,da ta dan Kalli Mukhtar din bai sani ba yanzun idan ya sani ya kenan? Anya ba zata daina Sha ba juya kar ya mata fa illa?

   "Tunanin me kike?"Ta ji muryarsa tayi saurin girgiza Kai tana fitowa daga keke napep din suka shiga gida d'aki ta wuce.Zainab ce ta shigo ,hannunta har da food warmer da plate ta ajje ,tana Yi mata sannu da murmushi a fuska.

"Ga jollop nayi ,nasan kina Jin yunwa tunda ba lallai kin ci abinci ba kan ku fita ,yaya ga abinci".Ta fad'a tana kallonsa ya jinjina kai "Sannunki to".

   "Nagode ".Cewar Ummin ta tashi ta shiga bayi fita Zainab din tayi zata so ta San me ke damun Ummin don ba taji an ce mata komai ba anya ba juna biyu bane?

    Da wannan sake saken ta koma dakinta Ummi kadan ta ci abincin don hankalinta  Bai wani kwanta ba don dai Mukhtar din ya zuba musu tare ne ,bayan ta gama yace ta sha maganin ta dakko ta sha ta d'an kwanta ya dauke kwanan ya fita.

   Abdool ne ya kirasa yake sanar masa an samu filayen ya zo ya gani ,ya ce masa da yamma zai zo ya samensa yanzun uwar dakinsa bata da lafiya yace dashi toh kafin suyi sallama....

   A daki Ummi tana tunanin makircin Zainab din yanzun ta soma ganewa a gaban Mukhtar tana forming good co wife amma bayan idanunsa tana nuna mata kishi.

    *****

   Ummi ba ta jima ba jiki yayi sauki ta koma school, Zainab kam ta sayar da gold dinta an aiko mata da maganin mallaka kamar yadda aka fad'a mata ,humra da sauran magunguna ne kala kala.Mukhtar kuwa ,tuni ya sayi filayen ma yan uwansa kowanne ya saya masa da kudinsu sai ya siya shima wanda zai gina gidansa.

    Ana cikin haka bikin Abdool ya zo aka sami akasi Zainab suna bikin cousin dinta don haka bata samu zuwa na Abdool din ba ,Ummi ce ta je da Mukhtar din duk a tunanin Zainab Mukhtar baza shi dinner ba tunda ba ta taba ganin yaje ba sai bayan sun je ta ke ganin pictures dinsu shi ma a status din wata da ta San matar Abdool din ne ,taji haushi ba kadan ba amma ta danne.

      Yau ranar kwananta ne ta gama shirin komai ,bayi ta shiga Mukhtar din yana d'akin waya yake dannawa.A cikin yar farar roba ta lakato wani abu creamy shi ba man shani ba shi ba cocoa butter ba ,ta sunkuya tana cusawa a kasanta ta tabbatar ya mamaye ko ina ,humran ta zuba ta shafe ta itama a jikinta tana fitowa a yanga take takawa zuwa gadon ta haura ,rigar bacci mai daukan hankali ce jikinta.Ta dubi Mukhtar din still waya yake dannawa kanta ta dora a kafadarsa "Ya Mukhtar da alama abi kake me muhimmaci a wayarnan ,tundazu fa kake daddanawa".

  Dagowa ya danyi ya dubeta ,kamshin humran ya sake bugun hancinsa ya sa ya dau seconds kafin ya amsa Yana binta da ido.

"Kawai dan wani aiki ne yanzu ma zan ajje".

"Better nayi kewar mijina".Ta furta tana narke masa a jiki ya gane me take nufi yayi murmushin ya'ke ,sam ita bata wai gajiya da wannan abun  ta banbata da Ummi idan zai jima bai nema ba zata nuna masa.Sanya hannayenta yaji tayi wayar hannun nasa ta karbe tana kashe data din ta dora a drawer gefensa ,ba yadda ya iya dole ya barta sai da ta ja hankalinsa akanta ya kwanta da ita,burinta ya cika bukatarta ta biya yanzu jira take ta ga maganin yayi  aiki.Bayan tayi wankan tsarki ta koma tayi bacci abinta zuciyarta wasai.

    Da safe bayan sallahr subh bata koma bacci ba ta shiga kitchen ta hada masa girkin da zai tafi dashi gun aiki da wanda zai karya.Dining ta jera musu bayan ya fito ,suna zaune ta soma tunanin yadda zata fad'a masa gold nata ya bata.Tana so ta gane maganinta yayi aiki?

    "Uhm..Ya Mukhtar,kasan mai ?"

    Dagowa yayi "Sai kin fad'a".

  "Ban fad'a maka gold  dina ya bata ba ?"

  Gira ya dage ta jinjina Kai tana nuna damuwa "Bikinnan da mukai ranar yini wlh bansan ya akai ba yana jakata na nemesa na rasa".

"Kema ,ta ya zaki Sanya gold a jaka?"

   "Ban San haka zata faru ba don ban ma fiya sa shi cikin jaka ba tsautsayi ".

  "Tohm Allah ya maida alkairi,Kuma nawa kika siya?"

  "200k"Ta amsa ya jinjina kai "Har 200k a great lost Allah ya hore sai mu sake wani".

Ameen ta amsa zuciyarta ba dad'i har ya fita ta komo d'aki ,kira ta hau yiwa Saliha tana bacci ta ga kiran Zainab din."Yar jaraba zata damen"Cewar Saliha tana daukaa.

  "Ke ,wani irin maganine haka ba abinda yayi wlh na tambayi Yaya wai Allah ya hore bai ce zai siya min wani ba fa".
 

  "Me kike ci naa baka na zuba hajiyata ki nutsu just da jiyane ki bari ke dai kiga". Saliha ta fad'a Zainab din ta jinjina Kai "Shikenan toh Amma dai Allah sa Yana yin".

  "Yana ma Yi"Cewar Saliha sukai sallama Saliha tayi gwalo.

  "Shegiya kina gidan mijinki bazaki gode Allah ba sai ki wahalar da kanki wai mallaka ,dad'i ne ya miki yawa nidai tunda na samu 50k dita ai shikenan "Ta kyalkyale da dariya "Mu gidan auren ma ya gagaremu".Ta fad'a tana tuna abubuwan da ta kwa'ba ta sa a robar a matsayin maganin mallakar sauran kuma normal magunguna ne na mata sai humrah mai 'kamshi da ta ce mata itama an zuba abin Jan hankali a ciki.



Dijensy

  

   

      
       

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now