'ki cire girman Kai you are doing it for him ba wai wani ba mijinki ne komai kikai masa don shi kikai' Maganar Yusrah ta fado mata.

  Wayarta ta dauka ta fito parlour amma sai tayi kacibus da Zainab ta dora kafa daya kan daya,ta ci uban kwalliya harda jan baki.Hajiyar wando da riga ta Sanya falazo baki sai green riga mai wani uban show me a kirji ba wanda zai kalleta bai sake kalla ba.Yawun takaici Ummi ta hadiya anya bata makara ba? Bata jin kuma zata sauya abu  Zainab din ta riga da ta saba har ga Allah bata son ta mata magana su fara cacar baki ta sake raunata don wannan abun da take baida maraba da raini ya ranar kwananta zata zo parlor ta bararraje ba shakka Mukhtar ta ke jira?

  Ummi ko gama disa aya batayi ba suka ji sallama Mukhtar ne ,bata ga tashin Zainab ba ta dai ganta a gaban sa ta rungumesa tana fadin oyoyo mijina.'Lallai matarnan ta iya makirci da kissa 'Ummin ta furta tana raina wani kanta ,a yanzun ta Kuma tabbatar da Zainab din ta girmemata don ita wannan kissar ma bata iya ba ita all this kishi things bata sani ba.Don ita ko novel ko movie na kishiya ba kalla take ba sabida kishin da ta ke ji amma sai gashi yanzu itace da kishiya har take nema ta maida ta baya?

  Mukhtar bai kula da Ummi ba sai bayan ta sake shi tana gwada mishi irin haka amma yawanci side hug ne ba irin haka ba da ta fad'a mishi gabadaya banda ya dan tsaya still da ta hankad'a sa baya ma.Kayan hannunsa ta rike duk a tunaninta na ta ne don ta saba ganin ba kaiwa Ummin ya ke ba ,ta karbe.Ummin ya duba ya gani daga nesa idanunta sun nuna kishi 'baro-'baro.

     
     Kitchen ta wuce da kayan hannunta Mukhtar ya karasa gun Ummin da kyar muryarta ta fito daga busashshen makogoronta "Sannu da zuwa".Ta fad'a Mukhtar ya amsa da yawwa yana kallon shigar tata ,tayi masa kyau sosai da little kwalliya da tayi mata hasken fatarta yasa ko ya tayi applying powder sai ta fito.

     "You look cute".

    Kai ta jinjina "Thank you"Tana Jin zafi a ranta iya abinda zai ce kenan?

"Ina zuwa".Ta furta tana wucewa kitchen,ya bi bayanta da ido he can see it from her side.Dakinta ya nufa ya rage kayansa ya shiga wanka bayan ya fito ya tarar jakar ta shi na tana gun Zainab ashe ta karbe.

  Zainab da ke d'aki tana sane tayi hakan definitely zai zo neman abinsa ta Kuma dau alwashin idan ya shigo sai ta rikitasa zata cire kunyarta da ragowar kwarjini da yake mata a matsayin yayansu Hameeda sai ta susuta sa kwanan ma sai ta kwacewa Ummi.

   Koda ya shirya cikin riga da wando milk bakar riga shirt mai gajeren hannu ya fito.Kitchen ya nufa ya isketa tana hada tray din abincin,ta ga shigowarsa ta karasa fridge ta dakko masa lemon da ta sa a fridge ta dora akai ya lura kamar avoiding dinsa ta ke ya taka inda take ta juya baya.

"Ummi".Ya kira sunanta bata amsa basai tunano abinda ya faru da ta ke ya karasa daf da ita Yana riko hannayenta ta baya spoon din da ta rige ya sa ta ajje kan plate din yana murza yatsunta habarsa ta ji ya dora kan kafadarta yana kai mata light kiss a kumatu wanda ya sa tsikar jikinta tashi ta lumshe ido.

  "Sorry".Ya furta kamar rada ta sake makale wuyanta tana Jin zafin zuciyar Yana sauka.

   "Nace kinyi kyau".

    "Thanks".Ta furta.

    "That's all?".

     "Shikadai ka fad'a Kai ma".Ta furta murmushi yayi ya waiwayo da ita tana sunkuyar da Kai.

"Look at me ,tell me meya bata miki rai?"

   Kai ta girgiza ya ce "Mai karya?"

  Dagowa tayi idanunta sun kada "Sisternki ce?"

  Shiru tayi yace "Sabida abinda tayi? ke ai ba kya min".

  "Ai ba kwanan ta bane meyasa zaka tsaya ta yi maka?"

  Murmushi yayi "Ke mai yasa baki zo kin min ba?"

Haushi maganar ta bata wata zuciyar ta tana fad'a mata 'Ai gaskiya ya fad'a waya Hana ki karasa kafin ita? Azanci ta fiki ki? Ko himma ta fi ki?"

  Gani tayi idan ta tsaya zata Bata ma kanta time Azo abincin ma ya Sha ruwa yasa ta kawar da batun ,ta dauka plate din ta na fita dining ta jera masa ta ga ya fito.Sai sannan ta kuma kallon kayansa ta ga kusan anko sukai , dad'i ta dan ji ko don ya ga irin nata ne?
   
    "Wai duk ni na siyo wannan ? Na dauka kince baki da food stuffs ".

"Na aika an siyo".Ta amsa ta Bude warmer.

"But why ,ki daina is not on you beside na siyo miki".Ya fad'a ya tuna Zainab ta karba ,zai mata magana ta bawa Ummin idan sun gama cin abinci.

    "Iye ,tuwo aka min"Ya furta delighted don yana son shi a cima.

  Kai ta jinjina"Na tambaya kaki fad'a min?"

  "Komai ina ci fa kawai ina son wannan sosai". Mukhtar ya fad'a.

Adjacent da shi zata zauna yace ta dawo gefensa ba musu ta komo itama haka ta so yi amma kar yace don ta ga Zainab ne tana zama.Daya ta sa mishi ya ce "Ni fa biyu nake ci".

"Kasani ko Bai dad'i ba".

  "A ido ma nasan zai dad'i Gimbiya".

   Sunan a bazata ta ji shi ,shi din ma kawai ji yayi ya fad'a ta basar Hadi da murmushi ta kara masa.

"Na 'kara maka".

  "Kin kyauta thank you"Ya fad'a ya soma ci.


Zainab a daki dai jira ta ke ta yi har ta gaji hakan ya tabbatar abinci ta basa tsaki tayi ko ba dade ko ba jima sai ya biyo baya.

 
  "Yaushe zaku fara exam?"Ya tambayeta ta ce.

"Da saura sati uku ya rage".

  "Ohkay ,Daman Abdool ne bikinsa ya zo , invitation din ma yana jakata amarya ta gayyaceki.

   "Allah ya kaimu ,Ina yake".

  "Na sa jaka ,tana gun Zainab zan karbo sai na baki".

  Shiru tayi ta jinjina kai .

   "Yayi dad'i abincinnan I enjoyed it".

  "Thank you".Ta fad'a Yana daukan lemon ya sha.Tashi ya ga tayi tuni Daman ta gama "Ina zuwa?"Ya tambaya.

   Murmushi tayi "Zan dakko Maka jakar ".Ta amsa yace "Okay ,daga Nan ta baki ma siyayyanki" Ya fad'a ba tare da ya kawo komai a rai ba.Kai ta jinjina tana nufar bangaren Zainab ....

 


Dijensy

YADDA NA KE SOUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum