Kai ta jinjina "Baka da yadda zakai Mukhtar".Ta fad'a tana tashi ta wuce toilet ya bita da ido yana girgiza kai ya rasa wace iriyar birkitacciyar yarinyace.

  Zainab a dining ya ji dad'i don baro baro bacin rai ya fito a tare da Ummin,tashi tayi ta bud'e miyar ta ta'be baki "Ko kamshin kirki".

  Murmushin mugunta tayi , jin motsin Mukhtar yasa ta saurin komawa ta zauna ta dan marairaice "Yaya Mukhtar hope lafiya?"

  "Ba wani abu bane fa,kawai karki damu da daddare ba sai kinyi wani girki ba ita ma tayi".

  "Awww ayya shine wannan fa ban zaci ma da abu ciki ba,ni kaina da bazan ba next time".

  Bai iya karashe abincin ba ya sha ruwa ya tashi ,ta tattare kwanunkan ta na wucewa kitchen.

******

   Ummi da fushi irin nata wunin ranar da takaici tayi shi abincin ma taki ci ,har dare ya shigo bata ce komai ba.Washegari da ta farka dukda zuciyarta ba dad'i amma Yusrah da maganganun ta ta tashi sabida haka ta hada abin karyawa ,dankali ta soya da kwai ta kai dining da wuri d'akin ta komo ,ta ce masa "Ga breakfast can".

  Dago ido yayi ya dubeta wai Ummin canjawaa ta soma yi ko akwai abinda ta ke kullawa? Wata zuciyar tace ka je ka ci kawai.Mikewa yayi ya dubeta "Muje tohm"

Kallonsa tayi tana ganin rashin yarda tare dashi ,hannayenta goge a kirji suka nufi dining din ta zuba masa kamar dole ake mata kai da Gani kasan she is just forcing things.Sai da ta gama yace ta zauna su ci tare.Ba musu ta zauna zata zuba nata yace "Anan zamu ci taren".

    Murmushin takaici tayi wannan ya tabbatar mata da zargin nata yake,bata musa ba ta dauka cokali ta diba ta sanya a baki. Sai da tayi loma biyu ta hada da tea sannan ya d'auka ya soma ci, hawaye take ta kokawa dashi kar ya zubo ta kasa yarda Mukhtar din tunani yake zata kasheshi.Tissue ta dauka tana share fuska ya dubeta tuni ya gane kuka take ajje spoon din yayi.

  "Ni ba zarginki nake ba Ummi ko da ba ki ci ba ba abinda zai hana na ci ka...."

Tahowar Zainab ce ta sa ya tsagaita da maganar a firgice ya ganta tana ware ido "Ya Mukhtar maciji a d'aki na".

  Dire cokalin yayi ba shiri da mamaki"Miciji fa kika ce?"

Kai ta jinjina ya tashi ya nufi d'akin ta bi bayansa tana lekawa ,d'akin ya shiga ba abinda ya gani ya duba can ya duba nan harda daga kasan gado "A kan pillow dinnan na gansa ya gangara daga fitowata a toilet fa".Ta furta Mukhtar yace.

  "Ko dai kawai kin sa a ranki ne?"

  Kai ta girgiza tana sake jaddada masa "Yace nidai banga komai ba".

  "Sai dai idan ta window ya fita"Ta fad'a tana binsa da ido ,da ya gama iya dube dubensa fita yayi ta fita itama don ta ce tsoro take ji , abincin da bai gama ci ba kenan Shafiu ya kirasa,tea din kawai ya karashe ,Ummi ba haka ta so ba goge hawayenta tayi ta karasa ci ta tashi ta wanke plate amma wani sashe na zuciyarta ta ji dad'i ganin ba Zainab din ce ta ci dashi ba.

  Bangaren Zainab kuwa a birnin zuciyarta dad'i ta ji don shiri ne tunda ta leko ta ga Ummin na zaune dashi ta tabbatar girki ta masa haka kawai taji bazata juri ganinsu ba haka.Ko ba komai bai ci ba sosai tayi tunani a ranta.

  ******

       Ummi da rana ma sai da ta masa girki ,kiransa ta fara yi ta tambaya idan zai dawo don ya fita ya jaddada mata da zai dawo da ranan bayin sunyi sallama ya dubi wayar da ido yana mamakin Ummin ce ta kirasa da kanta?

     Zainab ta ga da gaske ta ke Ummin wannan yasa hankalinta ya soma tashi har kwanan ya juyo kanta har bata so ya kare wata soyayyar da take nunawa Mukhtar har da ganin idon Ummin don ta lura bata iya boye bacin ranta.

 
    Mukhtar bangaren sa kuwa abinda ya sa gaba yanzu maganar gona ce ,kamar yadda suka zanta da Kawun suka je kauye ,girman gonan ba karamin mamaki ya basa ba amma haka Ikon Allah ya a ke Koda wasa Bai zaci irin haka ba.Kudi akayi mata ta tashi kudi mai tsoka sosai ,nan ne aka zauna da Umman harma da sauran kannensa kowa ya amince a raba gadon.Umma da take da yara maza Kuma nata sun fi yawa sai ta tashi da fin na su Mukhtar din ma da yan uwansa mata biyu ,tasan shine mai dawainiya da su yasa ba ta rufe ido ba ta ce ya kulawa da Yan uwansa dukiyarsu don yarane ,Yan uwanta sun fara zugata ko ta karbe kudin ta ce aa wani dad'i da taji gidan da suke ciki ya fado kan nasu rabon.Duk wannan wainar da ake toyawa Ummi bata da masaniya Zainab kuwa komai a kunnenta ,sabida kusancinsu da su Umman.

    

   *Ghost readers I will change am for you ooo you can't be reading and not dropping comment idan kuna son ya koma na kudi ne kuma tohmmm writing has been hard this time coz of  little time that I have non like before da nake free be voting and comment please*

Dijensy

   

YADDA NA KE SOOnde histórias criam vida. Descubra agora