A bangaren Ummi kuwa yana fita ta rufo kofarta ta koma ta cire kayanta sannan ta sanya na bacci riga da wando ta kwanta.

  Washegari da safe 6am ta farka ta ga asuba ta wuce ,Koda tayi sallah wata yunwa ta ji ta addabeta ta fara tunanin me zata ci,wanka tayi tukun ta sanya doguwar rigar atampa ta fito ta duba kitchen shi kansa ta raina kitchen din ba haka ta so shi dukda yana da girma kawai tsarin ne bai mata ba ,ta hau bude fridge ba laifi da kayayyakin bukata a ciki ,sai dai ita ba ta Jin tana da energy girki ,locker ta duba ta ga kayan tea har da quicker oat da cornflakes tayi saurin dakko conflakes din ta hada ta aha sannan ta fito ,tana duba ko Ina ta ga dining madaidaici ta wuce d'aki ta zauna.Kamar saman yana biyw da ita ta gansa ya turo kofar d'akin Bata ko dago Kai ba tana ta latsa waya.

   "Kin tashi lafy?"Ya furta ba tare da ta dago ba tace "Akwai wata matsala ne?"

  "Babu".Ya amsa tare da juyawa kamar zai fita kawai ya dawo ,takowa yayi sai sannan ta dago ido ta sauke kansa yana sanye da jallabiya brown a ranta tayi tsaki don wani haushi da tsanarsa ta sake ji ,banda ba'ki ashe harda rashin iya dressing duk ya hada.A ranta ta fad'a.

  
  Zama yayi bisa gadon ta day'an gefen ta bisa da ido.

  "Khadija,ina so ki sani daga ni har ke wannan auren a kaddara ya zo mana ,ko ni ban taba zaton hakan zata kasance ba rashin yarda bashi zai daidaita matsala ba ,bance sai dole kin nuna min kulawa ba ko makamancin haka what I want is just respect from you, please idan na samu wannan I will be delighted shi kadai ma is enough ko da bazan samu sauran ba.Kiyi hakuri na shigo rayuwarki ,ba yadda zanyi ne nima nayi accepting offer mahaifinki ina so ki san da wannan".

   "Duk abinda kike bukata kada ki gaza tambayarta in sha Allah zan iya kokarina na dauke miki shi"

  Tashi ta ga yana yunkurin yi ta dubesa "Dakata,nan ka zo ka min waazi ne ? Ko kuwa gargadi kake so ka min ban fahimta ba?  See I am not hear for all arrange marriage wahala zancen hakuri ma bansan jinsa don ba yi zan ba indai kana son zaman lafy free me that is the only way zan san da gaske kake and ta wannan kadai zaka samu respect a guna".

   Tashi yayi bai mayar mata ba ta ga ya tashin cikeda jin haushi  "Magana nayi fa?"Ta furta.

  Tashi tayi ta taka gunsa ya waiwayo Kai da ganin yanayinsa Bai shirya wata rigima ba he is not ready for all this fight childish thing da kyar ya iya budar baki yace.

  "You need some rest ,na ji ana knocking a kofa".

  Harara ta bisa da ita kamar ta shakosa ta ga ya fice wai shi baya fishi?

   Tsaki ta ja "Dan iska maye".Ta fad'a don mamaki ma ya fara ba ta ta ya bazai yi fushi bane shi? Ta zaci tun jiya zata sare masa ya fara shawarar canja raayi meke damunsa?

***

Kannensa ya gani maza sun kawo masu abinci a lunch box yayi godiya suka tafi bayan ya basu kudin mota ya koma ciki ,a plate ya zuba mata ya kai mata d'akin ya ajje ya fito parlour ya zuba masa ya soma ci yana hadawa da tea ,kwai ne da chips Umma ta kawo.

 
Duba abincin tayi ta juya shi a wulakance ,guda d'aya ta dauka tasa a baki ta ji yayi dad'i suyan nan ta sakko dashi ta soma ci shayin dai taki sha da ta gama a masai ta juye shayin tunaninta ko ya sa magani a cikin shayin tazo tayi baci haka kurum ya haike mata?

    Tunda tayi breakfast ta rufo kofarta ta kwanta tare da kunna data ta shiga Netflix Muhktar yana parlour ya Lula duniyar tunani don ya ji sanda ta karkame kofarta , tambayar kansa yake a haka za su cigaba da zama?

'Ka bata lokaci idan aka kwana biyu zata canja '

  Zuciyarsa ta fad'a,wayarsa ya Bude ya soma dan duba chat's wasu duk na Allah sanya alkairi ne reply ya danyi kafin ya fita ya ajje wayar shingida yayi a kujera bacci ya dauke sa.Ya shafe wajen 2 hrs kafin ya tashi lokacin 12 tayi.

  Kamar dazun Umma ta sake kawo musu abincin rana ,Bai kasa a gwiwa ba yayi knocking din d'akin hakimar kallo take ba ta ji ba ya yi bugu ya gaji ya kira sunanta shiru shi tsorata ma yayi ya fara tunanin ko wani abu ne ya faru da ita ,d'akin da ya kwana ya shiga ya dakko spare key ya bude ta Yi ruf da ciki ta dora kirji Saman pillow tana kallo ya tsaya bayanta more than 2min ba ta sani ba don ta juya baya sai da ya karaso ya cire earpiece daya ta waiwayo a masifance.

   "Me ye ne?"Ta furta tana masa kallon banza.

   "Ina ta magana".Ya fad'a ba tare da daga murya ba.

   Tsaki ta saki tana zare dayan kunnen ta mike zaune.

  "Sabida zaka min magana sai ka taban kunnen? Beside kofa ta a rufe take da me ka Bude?"

   Yayi second 20 kafin ya amsa ta "Spare key , sorry for distracting abinci aka kawo na ajje miki a dinning ki taso mu ci".

  Gira ta dage"Kai da wa zaku ci abincin?"

  "Ni da ke".Ya amsa a ta'kaice".

  "Sabida?"

  "Ni mijinki ne".

Wata dariyar raini tayi "Sabida ka biya yan canji ka ke ganin you have right a kan komai nawa?".

  "Ya rabbil Al'ameen"Ya furta a fili.

  "Ka koma ta bana ci idan kana so naci order zaka sa a kawo min ba wani kwashe kwashe ba na zuba a ciki"Ta kare maganar kasa kasa.
   
    Zuciyarsa ba dad'i ya fita daga d'akin ya zauna kujera parlor yana zabga tagumi.A tunaninsa kyautatawa ce zata karkato da zuciyarta ,kojarinsa ya dan faranta mata ko yaya ne amma ya ga yadda ta ke behaving ma.

   "Allahumma ajirni fi musibati".

    Ummi kuwa maida headphones dinta tayi "Aikin banza dole sai nasan da existing dinsa".

     Wunin ranar dai ba dad'i yayi shi da daddare kamar jiya ta rufo kofarta abinci kuwa kin ci tayi karshe sai bawa almajirai yayi ya wankewa Umma kwanta ya ajje ya shiga d'aki  ya kwanta.

   Kwana uku Umma tayi tana Aiko da abinci yau ne na hudu da safe ya tashi da kansa ya dora doya ya fere ya dafa sannan ya zo ya soya da kwai ,inda Allah ya taimakesa yayi zaman hostel ya dan iya girki.Tea ya hado ya zo ya zauna ,ita kuwa baya sa ran ma zata fito don kwana hudu dinnan tana d'aki indai ta fito kitchen zata shiga shan qaucker oat ko cornflakes su ta mayar abincinta sai indomie.

 
    Tunda bai gama cika 1 year da aiki ba he is not entitle for leave ,hutun nasa sati daya ne don haka litinin mai zuwa zai koma.Wanke wanke yayi ya dawo parlour nan ya ga kiran wayar Baba ,ko da ya dauka bayan ya gaishesa a ladafce Baba ya ce masa yana waje.

    Tashi yayi ya duba ta a daki ta fito kenan daga wanka ba ta rufe kofar ba tunda ta tabbatar yana da spare key ,duk abinda ya gani shi ya ja ma kansa ta fad'a a ranta yanzun da ta ga shigowarsa tsuduk ta basar daga ita sai towel dan karami ko wuce cinya bai ba.

  Da har ya dan cake daga kofa kar ta masa rashin kunya tace ya shigo mata ba knocking ya ga ba ta ce komai ba.

"Idan kin shirya ki fito Baba yana waje zai shigo yanzu".

  Tun shigowarshi bata dago ido ba sai yanzun tsoro ta ji ko kararta ya kai ta amsa da toh a sanyaye ya fita ta Yi saurin ciro kayan da zata sa tana 'Allah yasa ba karata ya kai ba'.




Dijensy

 
 
   

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now