"Zan samu ?"Baba ya sake tambaya don ya ji Mukhtar ya dauke wuta .

   Tsaka me wuya ya shiga sai dai bazai iya denying ma Baba ba domin ya na musu halacci yana ma kanyi ,baisan dai mai yake nufi dashi ba amma haka ya jin jina kai "Ba abinda zaka tambaya a gurina na gagara maka ". Muhktar ya fad'a cikin dauriya.

  "Alhamdulillah".

  "Bana son ka ji wani damuwa ,duk wani abu hidimu tn aure idan ka cire sadaki duka ala'ada ce da bidia sabida haka banson komai daga gurinka sadaki kawai ya isa ,akwai bikin Abdulbasit da ya rage sati biyu idan Allah ya yarda nake so a hada tare da naku,kana da gidan zama?"Ya tambaya

   Kai ya girgiza masa Baban ya ce "Ba wani abu ,ina da gida da zan iya baku ku zauna,bana so ka dasawa zuciyarka tunanin irin wacce yarinyar ka aura ,nan da ka ganni ba da arziki nayi aure ba zai da aka Yi gwagwarmaya Allah ya hore sabida haka kar ka ji komai zaman aure fahimtar juna  ce ,da hakuri da juriya.Yabawa da halinka ya sanya  ni neman wannan alfarmar Mukhtar".

   Addua ya yi masa da godiya Baban kafin ya tashi ya tafi,kamar bai da jini a jiki ya hau keke hular kan ma gagararsa tayi ya rufe face dinsa Yana jingina a kujera.Sam bai son issue irin wannan ,ba wai bai gode  bane yasan wannan gata ne  wanda har yayi yawa a baka aiki a baka mata sannan a baka gida?   Babbar matsalarsa yarinya ba bata son shi tana son shi Allahu aalamu? Duk wani abu da zai ja masa rainin baya son shi bacin duk da fadawa Baba da yayi bai da gida amm ya ce zai bashi ??? Baya son abinda zai zo ya biyo baya.

   Ya shiga gida ya ji ya kasa samin nutsuwa , Shafiu  ya kirawo gidan ya labarta masa kamar mafarki ya gani
"Abinda nake ji a gari yana faruwa daman har yanzu? Abokina Allah ne ya baka wlh ".Shafiu ya fad'a.

  Kai ya dago Muhktar"Shafiu hankali na ya kasa kwanciya fa ba wai abin wasa bane fa".

  "Alkairi ne in sha Allah ka da kayi mamaki akwai wani abu da yake tunkararka ne , nutsuwa zakai abokina kayi tunani  sannan kayi addua"

Kai kawai ya gid'a Shafiun yace "Mai ne plan naka toh yanzu?"

"Plan what ,2 weeks fa ni mai na tsara?"

"Tohm ba yace zai baku gida ba ,mai ya rage lefe nw shi ma an yafe naka kai kai wamnan a sadaka aka ma aure"

Harararsa yayi "Be serious mana"?

  "Okay ,zakai event ne?"

   Kai ya girgiza "Event ana zaune kalau?"

  "Abokina  bansanka da tsoro ba fa kai da kake da dakiya akan aure duk ka razana ko tsoron auren kake ?"Ya fad'a da zolaya.

 
    Shiru yayi sai da ya bashi baki sosai ya samu relief tare suka sauka kasa wajen Umma ,suka fad'a mata ta hau jinnina Lamarin  ,a fili tace Allah ya tabbatar ya sa albarka  a ranta kuwa bata ji dad'i ba don akwai yar kanwarta da take masa sha'awa amma ya zatayi harkar manya ake yanzu dole ta ja baya da wancen batun yanzu su ci arzikin tare.

 

     Ummi a gida bata san wainar da A
Ake toyawa ba ,wuni tayi ta kasa fitowa sai da daddare ta zo ta dauko abinci ta ci ta koma miss calls din Faruk ta tarar sai sanna ya kirata ta shiga bayi ta amsa ,kuka ta fashe tana fad'a masa ya janyo mata  Babanta yayi fushi ta bashi labari har asibiti suka je hakuri yayi ta bata ya mata alkawairn idan dad dinsa ya zo nan da next month zai masa maganarta iyayensu su shiga tsakani nan da Nan taji nutsuwa ta zo mata ta kuma amince da hakan sukai sallama tayi kwanciyarta.

   Washegarin da safe wayar ya Abdulbasit ce ta tasheta ta ,da fad'a ya hauta ko da ta daga.

"Kinsan me kika jawa kanki? Baba aure zai miki kuma wlh ba ruwana kowa ya aura miki kar ki kuka "

YADDA NA KE SOOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz