Ahmad sai yau ya shirya zuwa gidan su karfe goma daidai na safe yasame shi a ƙofar gidan saida yashiga ya daidai ta parkin din motarsa ya fito yana tafiya kaman wanda bashi da laka ajikinsa main falon gidan nasu yanufa kansa tsaye bakinsa dauke da sallama.

Auta meera ce tamiƙe da gudunta tana masa oyoyo daukanta yayi ya ɗagata sama yana juyata kaman wata bebi itako sai dariya take Fadwa ma tazo ta faɗa jikin sa tana cewa"ya Ahmad ina kashiga kwana biyu baka nan kullum Ammi sai tayi kuka gashi kuma daddy bashi da lafiya wai wai ....sai kuma tayi shiru tsareta da ido yayi zuciyarsa dake faman bugawa da sauri da sauri meera ce ta amshe da cewa"a school dinmu ba wai kawayen mu cemana suke daddyn mu macucine yana cutan al'umma da saida musu da ƙwaya da sunan magani shiyasa aka rufe masa company da muka faɗawa uncle Sam sai yace ai gaskiya aka faɗa mana mu yaran maci amanan kasane yau kwana biyu bamuje school ba saboda ko munje yara da malamai zagin mu suke.

Besan sanda ya dire meera ƙasa yanufi ciki ɗakin Ammi da sassarfa ba,zaune ya taddata ta saka daddy gaba da ban baki yasha koda tea ne,amma yaƙi amsa yayi baƙi kirin ya rame cikin kwana biyu kaman wanda ya kwanta ciwon shekara,zuba masa ido sukai suna kallon sa"Ammi wai me nakeji daga bakin yaran nan yanzu?

Ajiyar zuciya ta sauke tana maida kanta kan Alh badamasi dake zaune cikin sanyi murya tace"wai ana zargin sa da sarrafa miyagun ƙwayoyi ba bisa ka'ida ba,shine aka rufe wajen.

Kai ina kashiga kwana biyu wayanka baya shiga ina kake tsawon kwana biyu baka da labarin abunda yake faruwa a garin?ta tambaya tana tsareshi da ido"yanzu de ba wannan ba Ammi shi daddyn wani irin mataki ya dauka dan kare mutuncin kansa dama companyn nin baki ɗaya.

"Babu nadeji ɗazu yana waya da Alhaji sunusi yana cewa zasu sami manyan akan maganan?

Wannan ba yi vane Ammi

Kallonsa daddyn nasa yayi yace"kadamu danine  da katsallaƙe kayi tafiyarka kwana biyu batare da ka waiwaye mu ba?

"Yi hakuri daddy yanzu ba lokacin yin wannan magana bane inason sanin shin akwai waƴanda suka saka hannu jari a company ko kuwa?

Shiru yayi dan yasan da zaran yace Alhaji sunusi yanzun nan zasu haushi da masifa shisa ma koda faisal yazo jiya du tambayan da yayi masa be yarda koda wasa ya ambaci sunan sa ba.

Jin shirun yayi yawa yasa Ahmad miƙewa rai a ɓace yace"daddy zanyi duk iya yina dan ganin nakare mutuncinka da martabanka da ƙimar wannan gida tamu koda zan rasa raina ne amma fa hakan baze samu ba harsai ka bani haɗin kai,daddy idan har ba wani abu mara kyau a wannan company naka ba bukatar bin manya da basu cin hanci.

"Ahmad company nawane ko naka?
Alhaji badamasi ya tambaya rai aɓace dan wani mugun haushin Ahmad yakeji,abu yau kwana biyu bayanan sai yanzu ne ze zo masa dawani zancen banza.

"Naka Ammjn ta amsa masa
"To inde nawane ba ruwansa"da ruwan sa harda tsakin sa dan hakkinsa ne kare mutuncun gidan nan matsayin sa na magajin ka.

Banga dalilin da wani bare da ze saka bakinsa cikin wannan magana ba,idan bada wata a ƙasa ba mai nawani cewa za bada kuɗi abi manya dan kawai son rashin gaskiya idan ba wata a ƙasa abar jami'an tsaro suyi aikin su kaman yanda suka bukata idan kuma dama kasan da wata aƙasa kayi gaggawan fayyace mana ta yanda zamu gane.

Menene alaƙanka da Alhaji sunusi dan shi kaskane raɓi...."ya isa yafaɗa a tsawace da daurawa da cewa kufita kubani waje.

"Zamu fita yanzu kaman yanda ka bukata saide abu na farko kuma ba karshe da zan faɗa maka shine babu zancen wannan bikin na Ahmad cikin wannan sati kaman yanda kuka tsara harsai komai ya daidaita dan baza'ayi biki aure ana cikin wannan hali ba tana kaiwa karshen maganan ta taja hannun Ahmad daya kafawa daddyn nasa ido suka fita daga ɗakin.

*******
"Aisha Aisha Aisha har sau uku Anty malika na kiran sunanta amma bataji taba saboda nisa datayi da tunani da take,barin abunda takayi tayi taxo ta zauna saman gadon kusa gare tana mai dafa kafadanta firgigit tadawo hayyacinta tana ƙakalo murmushi da iya kacinta kasan saman leɓɓen tane tace"Anty malika karde hankin gama?

Gyaɗa mata kai tayi cike da tausayinta tariƙo hannunta tace"nasan da wuya ace rana tsaka karabu da abunda kakeso dakuma ciwo amma idan kika saka hakuri aranki kika kuma dauki abun da sauki saiyazo miki da saukin.

Hawaye datake ƙokarin tsayarwa ne yasamu nasaran xubo mata daga gurbin idanunta tace"Anty malika hakika nayi rashin masoyin gaskiya shin faɗa masa gaskiya danayi kafin yaji abakin wani yaɗauka na yaudare sane kuskurene yin hakan?

"Bakiyi kuskure ba koka ɗan hakan da kikayi shine daidai"to amma Anty meyasa koda sau ɗayane be tsaya ya saurari abunda nake faɗa masa koya nuna yajini ba sai shirun da yayi kinko san yaren shiru kuwa Anty malika wannan shiru yana neman kasheni naso ace koma yayane ya tsaya ya fuskance ni nide wallahi an cuceni da wannan auren wucin gadin nan wallahi ta faɗa tana sake fashewa da sabon kuka,dr sufyan daya zo shiga ɗakin yaji dukkan abunda suke tattaunawa baya yayi a hankali batare dasun san da tsayuwar sa awajen ba.

Suhail tunda yashiga ɗaki yarasa meke masa daɗi yasan tabbas gaskiya Aisha ta faɗi dan betaɓa kamata dayi masa karya kokuma wasa irin haka ba,shin awani mizani yakamata yaɗaura kalamanta cin amana ko yaudara"la la la yafurta a fili to ma waye wannan dayayi musu ƙatsalandan shiga cikin rayuwarsu bayan sun riga sungama tsara yanda zasuyi rayuwarsu ƙarƙashin inuwar aure.

Kukansa yayi mai rai da lafiya dan yasan kukan ne kaɗai ze iya saukar masa da abunda yajiki a ransa gwara yayi ko ze samu sassauci da salama a zuciyar sa amma de yasan yayi rashi rashi irin wacce bazai taɓa maida irin sa ba.

ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now