_kowa da kudinka saida rabonka bawai ina magana kan kaina bane a'a ina maganane kan wannan riga dake jikina matsayina na ɗiyar da nakowa ba ban isa na mallaki wannan kayan ba,Abu na Allah wai budurwa da jika kasancewa ta telah sai gashi na dinka abata na nasaka ina alfahari da sana'ata ta telah muba abun rainawa bane kaman yanda wasunku suka daukemu neman gumin mu muke bawai roƙo ko bara muke ba,kaman yanda wasunku suke ɗaukan mu kawai sukawo muna kaya mu ɗika musu subamu kuɗinmu idan kuma akasamu akasi rashin gama musu ɗinkinsu akan lokaci su rufe idonsu suci mana mutunci basa tunanin gobe ma zamu sake gamuwa sude ganin su ai kuɗinsu ke aiki dan haka bamu da saura mutunci awajen su tunda kudi suke biyanmu.
Tellah ba ƙasƙantacce bane mu teloli jajirtattune jinjina ga telolin da ke faɗin duniya baki ɗaya dan ko shugaban ƙasa ayau da bazarmu yake taka rawa dan sai mundika sannan ze saka tufafin da zefiti jama'a suyaba na jinjina mana matasa ƴan uwana kumu riƙe sana'armu hannu bibiyu watarana ze kaimu inda bamuyi zato ko tsammani ba mukasance masu cika alkawari sabida girmanta_ 👏🏽

Tana turawa sai kawai kira yashiga wayan ta ƙirgijinta ne yashiga lugude yana dukan tara tara dan yafi karfin uku uku bata taɓa jin faduwar gaba irin haka ba,idan yakirata koda yaushe takan tsimayi kiransa cike da zumuɗi take ɗaga kiran har Allah Allah take lokacin kiransa yayi susha hira amma yau itace rana ta farko da taji hakan a ranta kuma ta tabbata ba komai yasa tashiga wannan yanayin ba sai girma igiyan auren mutumin da bema dauki abun dawata daraja ba akanta wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauke daidai kiran ya katse wani kiran yasake shiga.

Ƙuntum bala tayi wajen dauka wayan tayi takara a kunne batare da tayi sallama ba,ajiyar zuciya taji yasauke mai karfi cikin sanyi murya kaman na wanda bashi da lafiya yafurta"so keki kikasheni ko hamaira?

Batasan sanda kuka ya kubce mata ba,kawai sai ta fashe masa da kuka jin kukanta yasa hankalinsa ya dugunzuma wajen tashi ji yake kaman yajawota tacikin wayan yabata hakuri"Ana asif ya habibi shine kawai abunda take iya faɗi cikin kuka.

Kusan minti goma tadauka tana kuka shi kuma yana sauraronta,abu biyu takewa kuka na farko mahaifiyarta da har yau bata da yaƙinin shin tana rayene ko kuwa wane hali take ciki shin tana cikin ƙoshin lafiya ko tana halin jinya shin tama samu taci abinci ko tana can tana bara su suna zaune anan hankalin su kwance duk daren duniya sai tayi kukan rashinta atare dasu,abu na biyu kuma shine Suhail dole ta fito ta faɗa masa gaskiya bazata rufesa ba ko dan darajan soyayyar gaskiya dayake mata.

Cikin rawan murya tace"Suhail kai hakuri dan Allah badan halina ba banyi hakan dan na ƙona maka rai ba,saide inaso matsayinka na musulmi wanda yayi imani da Allah da kuma kaddara maikyau ko akasinsa Suhail kaine wanda nafara so tun bansan menene so ba,inaso kamun alkawarin duk abunda na faɗa maka zaka daukesa matsayin kaddaranmu bazaka kuma yimun mummunan fassara ba"cike da zaƙowa yace nayi duk da wani sashin na zuciyarsa tana faɗa masa wani abu abu mara daɗi amma haka ya daure yace yayi.

Dakyar ta aro jarumta tasakawa kanta tasan wannan itace hanya daya dazata faɗa masa gaskiya kafin yaji abakin wani yadauketa mayaudariya"inaso ka auri ƴar uwarka Suhaima dan itace ta dace dakai.

Wani irin miƙewa yayi tsaye dayajawo hankulan iyayensa da ƴan uwansa duka dake zaune a falon dan tattauna ta yanda zasu ɓullowa abun ganan suhaima ta kusan kamuwa da ciwo zuciya sanadin sonda take masa shi ance ya hakura a aura masa ƴar uwarsa yanzu in yaso daga baya suje nigeria neman masa auren wacce yakeso yaƙi yace shifa sai idan ansoma nema masa auren Aishan in yaso ayi na suhaima daga baya.

Ita kuma suhaima cewa tayi inde ze aureta koda na wucin gadine ta yarda muddin zata amsa sunan matar sa yaje ko Aisha uku ze auro ya auro.

Jikinsa sai kyarma yake kaman mazari besan sanda ya faɗa saman kugera daya tashi ba,umminsa ce ta karɓi wayan daga hannun sa tasaka ta hands free tayanda kowa zeji.

"Habibi kai ɗin ka kasance masoyin gaskiya dakai nake kwana dakai nake tashi acikin raina tunaninka betaɓa gushewa acikin raina kodana na diƙiƙa ɗayane ba,saide bazan yaudare ka nakuma yaudari kaina mufaɗa cikin fushin ubangiji saboda son zuciya ba.

An dauran aure da waninka bansan ya ze karɓeni matsayin mata ba,shin zan dace da auren koko?

Nide nayi bibiyane nasan kuma duk wanda yama iyayensa biyayya Allah ze dubi lamuransa,Anta mahbub da'iman kukane yaci karfinta ta yanda baxata iyayin wani maganan ba sai sautin kukanta dake karaɗe kunnuwan su tsit kakejin falon shikansa suhail ba zakasan awani yanayi yake ciki ba saboda kasa dayayi da kansa,suhaima ce ta rarrafa tazo ta faɗa jikin sa tasaki kuka mai karfi tana cewa"akhi kaje kazo da ita itaɗin masoyayiyar gaskiyace hakiƙa ni naza maison kaina nasan Aisha ta gujeka ne kawai sabida goranta mata launin fata dakuma kiranta da kwaɗayayya mara asali da nayi yasa ta yanke wannan hukunci,tabbas ita ɗin mai zuciyar zinarice tunda bata taɓa faɗama irin cin mutunci da zaginta danakeyi a waya ba,bayan sakon txt dake rubutawa na cin mutunci da tozarci danake tura mata bata taɓa maidamun da amsa koda sau daƴane ba nasan hakkin wannan abunda namata shike bibiyata Allah yajifa mun soyayyarka acikin zuciyata gashi tana bara zana ga rayuwata wacce na raina nake ganin nafita dakomai ita tayi nasaran mallakan zuciyarka dan allah akhi alfarma ɗaya zakamun koda na rasa rayuwata kazamo....sauri rufe mata bakinta yayi da tafin hannunta yana girgiza mata kansa dagowa yayi da rinan nun idanunsa dasuka kaɗa sukai jajir dasu fuskar nan tasa ita tayi jaa sabida tashin hankali dayake ciki,miƙewa yayi batare da yace komai ba,yayi hanyan ɗakin sa sai juwa dake kokarin kadashi saurin miƙewa ummi tayi dan bin bayansa amma sai Abbiy ya katse mata hanzari yace"barshi yana bukatar keɓe kansa ku barshi ya huta,da haka taron ya watse sai suhaima da aka bari falo tana rizgar kuka da kiran duka lefinta ne ita tajawo Aisha ta guji suhail tayi da tasanin bin shawaran kawaye datayi sosai.

ALHAJI SUNUSI
Sai gabda kiran sallar magariba sannan yazo gida koda yazo ɗakinsa yawuce direct saide yana bude kofan ɗakin wani kamshi mai daɗi yabugi hancin sa,lumshe idonsa yayi dan shifa gani yake tunda yake a rayuwarsa betaɓa jin kamshin turaren daya tafi dashi irin wannan ba.

Haj mariya dake laɓe bayan labule tafito cikin takun katsaita tazo ta rugumesa tabaya take yaji wani irin azabebben feeling wanda betaɓe jinsa ba akanta rugumeta shima yayi nan labarin yasha bamban nima mai dauko muku rahoto sai fitowa nayi naja musu ƙofa dan fa abun na manyane.

Ahmad
Baccin sa sha sai karfe biyar ɗin yamma yasamu daman farkawa da azaban ciwon kai lallaɓawa yayi yafaɗa toilet wanka yayi tare da dauro alwala yazo ya gabatar da sallan la'asar da besamu yayi ba karamar wayansa yaɗauka wanda bakowa keda wannan lamba ba yakira Ammin sa lokacin tana ɗaki zaune ta rabka tagumj hannu bibiyu ita tarasa meke damun mijinta kowa nason ganin farin ciki da walwalan ƴaƴansa amma banda shi,gashi yanzu yaɓatamun rai amma bemasan yayi ba yanzu haka jira yake naje nabasa hakuri wallahi wannan karon baxan bada hakuri ba tunda kan wannan mutumin ne.

Wayanta dake ringing ne ya katse mata hanzari dagawa tayi batare da tasan wanda ke kan layin ba"Assalamu alaikum Ammi yafurta cikin sanyi murya.

Wani irin dadine ya ziyarci xuciyar ta har hakan ya bayyana a muryarta amsa masa tayi da"wa'alaikum salam Ahmad ina kashiga ne duk katamun da hankali.

"Ammi kwantar da hankalinki tafiyace ta kamani na gaggawa zanyi sati kafin naxo"Allah yakamaku ashe keke zuga yaron nan yake mun iya shegen da yaga dama bani shi bani shi yafada yana warce wayan daga hannun Ammin saide kafinma yakai wayan kunnesa Ahmad yariga daya kasheta baki ɗaya tunda yaji muryarsa yakuma daura damarar yakan Alhaji sunusi da fiddashi cikin rayuwr mahaifin nashi......ja'irin yaro yakashe wayan yafaɗo rike da wayan a hannun sa.




ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now