🅿️9️⃣⏩1️⃣0️⃣
Hindatu ta shiga makaranta kuma alhamdulillah tana k'ok'ari sosai, dan duk da makarantar k'auye ce amma hakan bai sa malaman makarantar suna yin ojoro ba. Dan haka sai ya zamana Hindatun ta k'ara sanya abun a rai kullum tana karatu sannan da yamma ta tafi makarantar allo ta kofar gidan su. Ikilima ma kwa na arabi ba boko sai shegen yawan tsiya da fad'ace -fad'ace a gari gashi idan ma Ummarta ta d'ora mata talla sai dai ta kawo kud'in ba dai -dai ba amma hakan bai sa Ummarta ta tsawatar mata ba sai ma ta d'akko sabon salo na koyawa yarinyar kaiwa tallan gurin maza a cewarta sun fi siya dan wani lokacin ma har su kan yi juye ko su ba da kud'in fiye da na kayan ,hakan yasa yarinyar ta ke kai wa talla shago da duk in da ta san maza suna zama ganin tana samun kud'i fiye da na kayanta yasa take kai musu dan ba wai haka kurum suke k'ara mata kud'in ba suna yin wasan banza ne da ita dan tsabar mulmulata da maza ke yi yasa ta fara k'irgen dangi ita kwa uwar ba ruwanta in dai zata ta kawo mata kud'i to babu ruwanta da me zai faru wanda hakan bata san kuskure bane babba amma ita ko a jikinta Ummi Ishalle ce ke k'ok'arin ganar da ita amma ta mata rashin mutunci, shi kwa Malam da yake a shanye sai kallo da ido.Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa har Hindatu ta kammala karatun ta na primary school ta shiga junior, bayan ta kammala Junior School sai kawai ta maida hankali kan karatun arabi dan dama iya Junior School ne yanzu haka ta kusa ta yi saukar Alqur, ani mai girma. Ikilima ma kwa sai dai gyaran Allah a lamuranta dan yanzu ta zama bata da wasu abokan huld'a sai maza ta je su mammatseta su bata kud'i ta yi harkar gabanta, dan ma dai Ummi Ishalle tana mata nasiha idan ta ga Ummarta ba ta nan duk da ba wani saurarenta take yi ba dan ko tana mata fad'a waya take dannawa dan yanzu wayoyinta har biyu da samarinta su ka siya mata dan haka ba ta ko bi ta kan Ummi Ishalle ba ta tashi ta shiga d'aki abin ta.
"Allah kyauta ya shirya mana zuri, a baki d'aya "cewar Ummi Ishalle itama ta nufi d'akin malam za ta gyara.
Washe gari da safe Hindatu na sharar tsakar gida dan gaba d'aya ita ke share ko ina ta wanke kwanuka, tana cikin sharar Ikilima ta fito daga d'aki da wata riga mai k'aramin hannu sai zani da ke daure a jikinta tsayawa ta yi tana k'arewa gidan kallo tana wani yatsina.
"Kai ni daman ba a gidan nan aka haifeni ba wlh me za,ayi da talauci gida duk yab'en kasa ga wasu dabbobi su yi ta damunka da kuka su hanaka barci mai dad'i,hmmm gaskiya ni ba na son talaici" Ikilima ta fad'a tana wani kama tsantsa.Ummi Ishalle ce da ke baiwa dabobi ruwa ta juya ta kalleta ta jijjiga kai cikin takaicin hali irin na Ikilima duk da ta san ba laifinta bane laifinta laifin mahaifiyarta ne dan gaskiya akwai k'arancin tarbiya a tattare da Ikilima.
Hindatu kwa da ke shara ko d'ago kai ba ta yi ba bare ta kalli Ikilima shararta kawai ta ke a nutse, dan ita har ga Allah tausayin y'ar uwarta ta ta ke yi dan gaba d'aya rayuwarta babu wani hali mai kyau sai dai addu, a kawai Allah shiryeta.
"Ke zo ki kwalfa min ruwa ki kai min bayi zan yi wanka"Ikilima ta ce rai b'ace dan ganin jelar gashin Hindatu da ya fito tana k'asan d'ankwalinta gashi har tsakar bayanta amma ita nata ko parking bai yi sai dai ta je a mata k'arin gashi.
"Babu ruwa a gidan yanzu za,a kawo sai dai ki jira idan an kawo komai zuba ki kai sai ki yi wankan "Hindatun ta fad'a tana had'e rai itama.
"Ke ni ki ke fad'awa haka da me zan ji, da rashin ruwan ko da maganar ki in banda ma talauci ace ruwan wanka ma sai ka jira an kawo yanzu da a birni aka haifeni ruwan wanka ma sai dai in kunna famfo in d'auka, wlh duk laifin Umma ne da ta yi aure a k'auye"ta fad'a a zafafe.
"Ke Hinde ki ke ko Hindu wato har wuyanki ya yi k'warin da za ki fad'a mata wannan maganar bayan kin san gaba ta ke da ke ko dan ba tarbiya gareki ba, ba, asan girman na gaba ba amma ba laifinki ba ne laifin gyatumarki ne da ba ta koya miki bin na gaba ba"Umma Kande da ta fito daga d'aki ta fad'a tana kamo Ikilima ta rungume ta da hannu d'aya.
"Ki yi hak'uri Umma walllahi ba haka bane, kawai dai na ga kullum ni ta ke sanyawa in kai mata ruwan wanka amma iya biyayya ai ina mata "Hindatu ta fad'a a sanyaye dan ba halinta bane raina babba duk kuwa da tana jin ciwon abinda su ke yiwa Umminta amma sai Ummin ta ke tausarta dan bata tarbiyar da ta dace.
"Kande wai dan Allah me yasa ku bakwa son zaman lafiya ko kad'an, kullum ace da tashin hankali ake karyawa a gidan nan duk da ba kulaku mu ke yi ba amma sai kun tarko abin da zai zama b'acin rai, yanzu menene laifinta dan ta ce in an kawo ruwan ta zuba da kanta duk kuwa da ita ke zuba mata ruwan kullum ko da kuwa makaranta za ta tafi sai ta zuba mata amma ba ta tab'a gode mata ba, amma yau ki ke cewa ban bata tarbiya ba,shin har kin kasa gane Hindatu tana da tarbiya ko ba ta, ko kuma kin kasa gane ke ce baki baiwa Ikilima tarbiya ba" Ummi Ishalle ta ce tana kallonta dan abin da ta fad'a ya sosa mata rai kawaici da kauda kanta ya sa Kande tana ganin kamar tsoronta take, wanda ba haka bane kawai dai ba ta son tashin hankali sannan kuma duk abin da za su yi shi y'ay'ansu za su je su aiwatar a gidajensu wanda ita kuma bata fatan haka.
"Lallai Ishalle ni ki ke fad'awa son ranki to wallahi kin d'akko ruwan dafa kan ki, kuma Hindatu ce marar tarbiya ba Ikilima ma ba kuma wallahi har gobe a matsayin mak'iya ku ke a wurinmu dan Y'AN UBANCI tsakanin Hindatu da Ikilima yanzu aka soma ko ma in ce ba,a soma ba"Kande ta ce tana girgiza jiki.
"In dai Y'AN UBANCI kar ku daina ai ba kan mu ba aka soma ba za, a gama ba kuma a kan mu, tunda Allah ya had'asu UBA d'aya to har gaban abada ubansu d'aya ne"Ummi Ishalle ta ce tana baiwa Hindatu umarnin shiga d'aki itama ta mara mata baya, dama Malam yana wurin almajirai.
"Haba Umma wai ma me yasa ki ka auri wannan Baban namu, baki auri mutum saurayi ba kuma ki sa shi ya miki alkawarin ba zai miki kishiya ba kin ga d'aya yanzu barin ni da Y'AN UBA, amma ga talauci ga zaman k'auye .
"Yi hak'uri y'ar lelena akwai dalilin da ya sanya na auri babanki, sabo da tarin kadarorin da ya tara kuma mu kad'ai za mu ci ba tare da wadannan y'an bak'inciki ba, kin ga idan mu ka mallaki kadarorin sai mu je binni mu sayi tanfatsetsan gida" kande ta ce tana washe baki kamar dai abin ya faru ma.
"Yauwa Ummana ashe akwai abin da ki ka shirya mana "Ikilima ta fad'a tana k'ank'ame Kande.
"Haka ne sha kuruminki komawa binni kamar an yi an gama kuma ko ba mu koma binni ba a binni za ki yi aure, dan sai dai wasu su ga ana zuwa binni amma su da binni sai a labari "
"Yauwa shi ya sa nake sonki, ki bud'e k'aramar jakata ki irgi dubu biyu "
"Yauwa y'ar albarka Allah k'aro miki masoya amma a binni "Umma Kande ta ce tana wata dariya.
*Bayan wani lokaci*
Rashin zama lafiya da ya ke gudana a gidan Malam Buba ya sa Nana ta nemi izinin mijinta ya zo ta d'auki Hindatu ta tafi da ita Maigatari domin cigaba da zama a can dan dama tana da burin haka dan ta san zaman gidansu sai a slow, kuma ta samu miji mutumin kir ki ya amince mata, dan har lokacin Allah bai ba ta haihuwa ba.Sosai Ikilima da Ummarta su ka yi bak'inciki dan kuwa bak'inciki sa son Hindatun ta bar gidan dan sun fi so ta zauna su cigaba da nuna mata Y'AN UBANCI, haka dai su ka hak'ura da wani k'udurin na da ban. Tun da ta koma Maigatari aka sanyata a islamiya amma ba ta allo ba, sannan an sanyata a boko a in da ta fara zuwa makarantar jeka ka dawo ta cigaba daga S. S 1 nan ta cigaba da karatun ta hankali kwance ba tare da damuwa ba.
YOU ARE READING
YAN UBANCI
ActionLabari ne mai cike da cin amana butulci, abubuwan al,ajabi kaa-kala
