"Amma MY dan naga abu nan wajenka inaso bani da matsayi da zaka mallakamun wannan abun matsayina na wacce zaka aura,tafaɗa tana kafesa da ido dan son jin amsa da ze bata.
Be bata amsa ba asalima bashi da niyar sake ce mata komai dan yana ganin yayima kokarin tsayawa yin dogon magana.

"Shikenan ta faɗa tana gyara fuskarta tada ɓaci da ruwan hawaye mikewa tsaye tayi tana kallonsa ok ina bukatar pieces ɗari daga nan zuwa gobe warhaka nakeso kasan idan kuɗine ba matsalata bane,wani shu'umin murmushi yasake mata wanda takasa gane ma'anarsa yana ɗage mata kafaɗa yace"anyway zaki iya zuwa kisami mai kayan sai kuyi magana da ita dan ni kaina saida kikazo nasan da kayan an danko yadinda akai amfani dashi bama dashi anan company....saurin katseshi tayi tana cewa kace kawai bazaka saka baki wannan ƴar matsiyaciyar ta bani kayan ba kenan,to wallahi kasani ko ta halin yayane sai na mallaki wannan kayan fuuuu tafice a fusace tayi hanyan barmasa office ɗin tana mai daddanna wayanta danson dialing Number ɗin daddynta dan ita fa dole saita mallaki wannan rigar dan tunda mummynta ta haifeta bata taɓa nagani abu tanaso rasaba dan haka wannan ma tagani tanaso kuma dole ta mallaka dan ta nan ne kaɗai take ganin zata nunama ƴar matsiyatar nan bambanci dake tsakaninta da ita.

ALH BADAMASI

Zubewa yayi gaban mai babban riga duk yaruɗe yana bada hakuri kan dan Allah a rusa batun auren Ahmad da wata bayan wanda ake saka ran yinsa,yanda yaruɗen kadai ze tabbatar maka ba cikin hayyacinsa yake ba kamande bawa da shugaban sa wajen ƙin tsaba umurni.
  "Shikenan zauna ai kabari ko gaisawane mayi ko yayansa yakubu yafaɗi haka kaman bega yanda kanin nasa yaruɗe ba,sai sannan ya maida hankalinsa ga waƴanda suke zazzaune a falon take wani irin kunya ta lulluɓesa dan rabon daya yaje garinsu ziyara koya kirasu ta wayane yaji lafiyan harya manta.
  Ƙasa yayi da kansa mai babban riga yasoma gaisarwa sannan yaya yakubu da yaya bara'atu nafi'u da ma'ruf shima suka gaisheshi ruwa mai sanyi da juice mai sanyi Ammi ta gabatar masa beyi musu ba yakuwa sha sosai fiye da rabi sannan ya ajiye kallonsa Malam mai babban riga yayi ya gyara zaman sa dayau yace"badamasi³sau nawa nakira sunan ka?

"Sau uku baffa ya amsa masa,gyaɗa kansa yayi ya cigaba da cewa yaushe rabonka da zuwa dubomu ko waya?
  Shiru yayi yakasa amsa masa da tambayan sai hakuri dayaci gaba da badawa"a'a riƙe hakurin ka ai mutum idan Allah ya ɗaukakashi gani yake ƴan uwa da abokan arziki da basuda shi ba ajin sa ba yanxu ya wuce sanin.

Kagode Allah daya baka mace tagari mai son zumunci badan ita ba da mun daɗe da mancewa da munada wani ɗa,amma Allah yabaka mace wacce take tsaye kai da fata dan ganin wannan zumuncin namu be ruguje ba,dan duk wani abu kama daga bikin aure suna ko mutuwa tana zuwa wani bin da yaran baki ɗaya wani bin kuma takanyi mana aike ko suje da ƴan uwata bata taɓa wofintar da duk wani abu namu ba,ko wannan zuwan muzone dominta da ɗanmu Ahmadu bawai saboda kai nayi tattaki daga kazaure zuwa nan kano ba,sai ya dan tsahirta.
  "Aure kuma anɗaura bamu da hurumin raba abunda Allah ya hada dan bamusan abunda Allah yaɓoye cikinta na alheri ba,yaya yakubu ne ke wannan magana.

"Ai wallahi kaman yanda matar uban gidan naka take kurin sunfi karfin kishiya to mu kuma zamu nuna mata cewa sunnan ma'aiki mukebi, faɗin(Allah subuhanahu wata alah)cewa ku aura daga biyu uku hudu idan ko bazaku iyayin adalci ba ku auri ɗaya,to danmu adaline da yardan Allah aurene anyi ba fashi saide idan mutum ze mutu dan baƙin ciki ya mutu.

Wannan magana ta yaya bara'atu kaman ta watsa masa tafashesshen ruwa haka yake jinsa,shi kaɗai yasan irin tashin hankali dayake shirin fuskanta dakuma tarin kalubabe dake tunkarosa.

Shide Alh badamasi banda hakuri ba abunda yake badawa saida nafi'u kaninsa da ma'aruf suka saka baki wajen bawa mai babban riga hakuri da yaya yakubu sannan ya hakura ƙarshe nasiha yashiga yimasa mai ratsa jiki cikin hikima da wayo dakuma dabara irin tasu ta manya,kwarai jikin Alh badamasi yayi laushi dajin yanda mai babban riga yake yi masa  nasiha kalma bisa kalma harafi bisa harafi ba wani hargowa ko ɗaga hankali,karshe yasake jaddada masa da kula da zumunci sannan ya daura da cewa masa"karka shiga hurumin da banaka ba,bamusan abunda Allah yaɓoye na alheri cikin wannan auren ba dan haka karmuzama masu ɓata abunda Allah yahaɗa Allah yayi muku albarka ma'arufa kikara hakuri kuma koshi beje kaimana ziyara ba ke karki bar wannan zumunci Allah yanason masu sada zumunci da masu yawan yin alheri.
   "Ina shaa Allah malam bazamu taɓa barin kuba aikune madubin dubawan mu baki ɗaya,sannan dan Allah malam ina neman alfarma abar su Inna delu suzo mana wannan karon ranan asabar kaman yanda aka saka shine ranan ɗaurin auren Ahmad da basma sannan kuma tarewar ita ɗayan ma.

Murmushi yayi irin tasu ta manya yace"ai ma'arufa kinfi karfi haka duk ma zasu zo harma da waƴanda baki nema ba,ai koni banzo ba yakuba zasu dawo dasauran yan uwa,ai kosu waƴanda suke masa ganin bashi da ƴan uwa zasu ganema idonsu shiɗin dan dangine gaba da baya dan ya wofinta dasu na.

Mutum idan ba rashin hankali ba kana tsaye da kafafunka mutum yazo rana tsaƙa yaraɓeka amma yace shine wanda ze juyaka katsaya kana rawan jiki baka da kataɓus akan komai sai yanda akai dakai,shide Alh badamasi kansa a kasa fatansa kawai kowa yatafi yabarsu yasamu zazzagema Ammi jakar tsaɓa kanta.

ALHAJI SUNUSi

Lokacin da Basma ke kiran wayan sa shikuma daidai sannan yana wani ɗaki yana ganawa da shugaban su bayan sun gama aikata masha'arsu(wa'iyazu billah Allah yakiyashe mu)dan neman duniyarsa goge jikin sa yayi da wani farin kwalle shima Alhaji sunusi yagoge duburansa a tare suka jefa kwallen tsumman cikin wani tukunyar kasa dake gabansu wuta naci aciki,rufe idon su sukai suna karanta wani dalamirai na tsafi can wutan ta tashi sama kaman an zuba mata fetur ciki a tare suka zabura cike da fargaba shugaban ya dubi Alha sunusi yace"matsala ta samu andaura auren surukinka da wata yarinya muddin wannan yarinyar tana cikin rayuwar sa bazamu taɓa samun yanda yamuke so ba,dan zata lalata mana komai namune akwai inuwan dake bibiyarta haryanzu bankai ga gane inuwar na waye ba.

INUWA INUWA INUWA kawai yashiga maimaitawa kaman wani zararre sabon kamu yana cewa shugaba kode inuwar Ishak da nafi ke bibiyar rayuwata yake son hanani kaiwa ga nasara bayan nasan duk wani sharaɗin dodo nacika harfa mamata ka kwanta da ita tsawon kwana arba'in haka nabaka budurcin ƴata ɗaya tilo nabaku jinin ɗana abun kaunata haryau uwarsa batasan baya duniya ba,ya zauce sai surutai yake"nutsu ka saurara wani murya ne yaratsa inda suke"yi maza kasamo mana jinin budurcin wannan amaryar surukinnaka a daren da aka kaimasa ita,idan karasa darenta na farko kanada dama harzu daren kwana uku dazatayi a ɗakin mijin ta maza tafi kuma cikin dare dodo yanason kakawo masa ƴarka na tsawon kwana uku dan cikan burin ka na har abada.


Alkalami🖊️
Yafi takobi⚔️

ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now