★★★

 
   Bugun kofar su Haydar ne ya sa shi bude ido daga kwance,yana tashi ya bud'e musu sunyi cirko cirko "Yaya kud'in makaranta".

  Suka fad'a sun shirya cikin uniform ya juya wallet dinsa ya duba Yana zaro 500 ya mika musu tare da musu Allah kiyaye.

  
    Komowa yayi ya zauna duba agogo yayi 10am ya daga gira da mamaki don bai cika yin bacci haka dayawa ba.Toilet ya shiga yayi wanka ya fito ya shirya cikin jean blue da riga grey t shirt ya dakko waya ya fito.A kasa ya iske Hassana "Je ki gyaran d'aki na".

     Amsawa tayi ba taso ba ba yadda zatayi ,ta rasa wani irin lalaci Yaya yake ji dashi yana yin duk wani aikin gida ya iya sai dai ba abinda yake masa wuya irin gyara katifa da share d'aki ,amma girki da shirya yara kuma bai bashi wuya.

     A parlor ya iske Umman ya gaisheta ta amsa "Abincin gidannan ya kusa karewa kuwa ,Abeed Bai da lafiya ina son kai shi asibiti".

  "Me yake damunsa?"Ya tambaya tace "Ina tunanin dai malaria ce amai yake da zazzabi".

     
"Allah bashi lafy".Ya fad'a tare da zaro dubu biyu ya mika mata ta amsa tana jujjuyata tayi zaton dubu uku ne "Anjima zan gani ,idan na dan samu wank abu sai na taho da kayan abincin".Ya fad'a sannan ya fice daga gidan  , matsalolin goma da ashirin sun tsaya masa a rai ga matsalar gidannan ga jiya da daddare Rasheeda kanwarsa ta kirasa take fad'ar tata matsalar za ai ma yaronta aiki a ciki.

   'Allah ka kawo min daukii ya furta a zuciyarsa.

  Cafe ya wuce kai tsaye ,dukda abokin nasa yasan rashin maganarsa sai  dai yau ya kula tunda ya kafa idonsa a system bai dauke ba kala baya cewa ana ta hira a gun.

"Mutumin me ya faru ne yau naga ka dauke wuta?"Abokin nasa ya tambaya.

Jingina Mukhtar yayi da kujera "Shafiu bazaka gane bane abubuwa sun tarar min aka na rantse".

  "Toh ya za ai sai hakuri ka daina d'orawa kanka damuwa ka dinga ajje ta a gida ,wanann rayuwa mutum ba zai kashe kansa ba fa mutumina".

  Murmushin ya'ke yayi kawai don sam abinda shafiun yake fad'a bazai yiwu ba,maida kallonsa yayi ga system din yana karasa project din wata da yake yiwa.

 
  *****

   Kwanan Ammy uku a asibiti aka sallameta ko da suka dawo gida ,tunanin yadda zata sanar wa da Ummi take zuwansu India ,ba ta sani ba Baba ya fad'a mata sai dai bai sanar mata da ciwon da ke damunta ba duk ta bayar ulcer din ce.

    Damuwarta daya shine ba da yarinyar zasu tafi ba ,Umar da Hafiz sun sanar dasu sai dai dukansu basu da labarin ciwon da ke damunta.Ana e gobe tafiyansu suka zauna dukansu hudun a parlor sunyi hira wacce suka dade basuyi ba har ma Ummi take jin ina zasu dawwama a haka don rabon da a hadu sun jima, don ma ba su Umar sai to 11 Baba ya ce ta je kowa ya kwanta sabida around 9am washegari jirginsu zai tashi.

 
    Tun da sallahr asubah yau Ummi ba a koma bacci ba dukda cewa weekend ce ,sai ta ya Ammy shiryawa take motsi kadan tace Ammy zanyi kewarki sai kawai ta ce nima.Bata lura da hawayen da yake kwaranya idanun Ammyn ba gabadaya ta tsorata da ciwon ,a yanzu haka wani bleeding take yi.Har airport sai da ta raka su ta dubi Ammy "Allah Kara sauki Ammy nasan me magunguna kawai za a baki ku dawo don dai Baba ya matsa anan ma zaa iya baki maganinki dole sai dai ya sani kewarki , shikenan ai Allah kiyaye hanya yasa ki dawo da wuri".

  "Ameen ,Khadija ki kula da kanki kinji ,be a good girl kamar yadda na sanki banda bari bari a dinga Jin magana Kuma Ake zuwa makaranta exam is approaching two weeks ya rage ko?

Kai ta girgiza "4 Ammy da saura ai".

"Tohm fatan Alkairi a rayuwa yayi albarka I love you daughter "

Ta kare kalmar tana rau rau duk irin dauriyarta Ummi ta kwabe fuska tana so tayi kuka Baba ya kira Nasiru "Zo ku wuce ai anyi rakiya yayi haka ,Anty sa a sai mun dawo ko?"

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now