Shafi 1

117 7 1
                                    


YADDA NA KE SO🌺



_Da sunan Allah mai girma mai rahama mai jin 'kai_

Page 1

'Yan makaranta ne 'yan mata guda uku sun jera suna tafiya a babban farfajiyar makarantar sanye da uniform navy blue skirt da top sai farar shirt a ciki da karamin hijab V shape.Ta tsakiya ta goya jakarta ta gaba wacce ke gefenta ta bugeta kad'an a kafad'a "Ummi dubi can wancen ba brother Saumah bane?"

A fakaice ta kalli gurin ta amsa da "Shine ,ki bar kallonsa dilla kar ya raina mu".Wacce aka kira da Ummin ta furta.

Ta day'an gefen ce tayi dariya "Ummi kin shiga uku wlh fafarki ta miki yawa".

Baki ta murguda ta ce "Ni dad'i na dake Yusrah zubda da aji ,nifa banson duk abinda zai saka na kwafsa a rayuwa wlh ,d'an iskan girman kai ne dashi sabida ya ga Allah yayi shi mai kyau".

Shaheeda tace "Gashi ke kuma irin yadda ki ke so ne,kina so kina kaiwa kasuwa"

Guntun tsaki tayi "Ni kyale ni na gaji bazaki gane bane sanin kanki ne duk macen da ta ga yayan Sauma dole ta ya ba ,ga tsaho ga shi yana gyming ke kinsan bani da buri irin na ga namiji yana gym wlh darajarsa karuwa take a guna plus ya iya wanka yadda na ke so".

"Awwnnn!"Suka had'a baki gabadayansu tare da kwashewa da dariya ta ta'be baki tana harararsu ,bayan sun fito gate kamar yadda suka saba driver ya k'araso suka shiga mota ya ja su ba wani magana sukai ba a ciki har aka zo sauke Yusrah ta musu sallama sannan Shaheedah last Ummi da ya kasance direban gidansu ne unguwarsu d'aya layin biyu ne ya raba su amma Yusrah da Shaheeda layinsu d'aya sai dai tazara kafin ka k'arasa gidan.

Bayan ta rufo kofar ta leka ta window tana gargad'ar direban nasu"Kuma saura idan Baba ya dawo yau ka ce masa bana zama lesson".Ta furta tana rolling idanu ya bita da ido matashin tare da girgiza kai "Allah ya shiryaki da rashin kunya".

Gaba tayi bata ji sa ba tana wasa da jaka har ta shiga cikin gidan ta tura k'ofa tana leka parlor wani dad'i taji jun yadda ac d'akin ta ratsa ko ina take ta cizge hijab din jikinta tare da cilli dashi kan kujera ba kowa parlor ta nufi kitchen bayan ta dire jakarta a kujera.

"Mommyna kin dawo?"Matar ta fad'a wacce bazata gaza 40-45 ba gid'a kai tayi"Ammy me kika dafa mana yau don yunwa nake ji? "

Wani makalewa tayi a jikinta Ammyn ta tallafota "Coconut rice ne gashi da sauce ,Nasiru bai samon sweet potato ba fate bai samu ba mommyna".

Shagwa'be fuska tayi "Ammy haba wai shi Nasirunnan me ke damunsa kullum kika aikesa sai ya ce bai samu wani abu ba".

Plate ta jawo ta d'ibi shinkafa ta bud'e tukunyar ta zuba miyar ,rabin miyar tata gabad'aya naman kazar ta kwashe ta zuba ta rufe "Lubabatu!" Ta kwala kiran sunan mai aikinsu ba 'bata lokaci ta 'karaso jiki na rawa "Ki kawo min lemo da ruwa ina dakina".

Ta fad'a bayan ta sanya cokali "Ammy na tafi d'aki.Ta fad'a tana wucewa.

D'aki ta wuce ta turo kofar tana kunna ac ta zauna carpet tana mi'ke 'kafafu ta soma cin abinci bayan ta d'akko wayarta a locker don school dinsu basa bari a je da waya yafi sau biyar ana seizing mata sai da Babanta ya tsawata mata da kyar ta daina zuwa da ita.

Data ta kunna sakwanni suka hau shigowa ta bude IG ta na ganin ruwan like na wani hotonta da ta dora , murmushi tayi kadan ta bi comment wanda mafi yawa positive ne daga masu wooo babe kin hadu sai masu alamar fire sannan love da sauran heart iya wanda zata iya tayi like sannan ta fita ta koma whatapp kai tsaye group dinsu da Yusrah da Shaheeda ta shiga ta ga Yusrah ta turo picture wani guy ne kyakyawa zubin model komai ya tsaru a 'kasa tayi caption.

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now