Hajia ce ta fara magana"insha Allahu za,a gyara kamar yadda ka bukata kuma naji dadin wannan nasiha daka mana. Allah ja da kwana"ta fada a zahiri a ranta kuma tana raya tabbas ya gama zubar mata da girma a idon aysha,kuma ita bazata taba karbarta a matsayin suruka ba.

"insha Allah daddy zaka samemu masu aiki da abinda ka fada"cewar ya abdullahi a ladabce.

"daddy tabbas nasiharka ta taba min zuciya lallai kafin a samu mahaifin da zai zaunar da iyalansa yana fadakar dasu domin gyara rayuwarsu,domin su dace duniya da lahira za,a tona,in Allah ya yarda zaka samemu masu aiki da maganarka.Kabeer ya fada yana kallon daddy.

"daddy munji nasiharka kuma muna godiya sannan zaka samemu masu kiyayewa"cewar ummulkhairi.

"daddy mun gode kwarai da nasiharka garemu"jamila tace a takaice.falon ne yayi tsit kamar ba kowa.

"Yata ke bazaki ce komai ba"daddy ya fada yana mai kallon aysha da kanta ke duke har loakcin.dago kanta tayi  tayi sannan ta fata bayani.

"daddy hakika ina alfahri da kai a matsayin uba kuma suruki a wurina ,sannan kuma wannan nasiha da kuma fadakarwa sunyi tasiri sosai a zuciyata,babu abinda zance sai dai ina maka ftn alkairi a dukkan lamuran rayuwarka,ina kuma addu,a ubangiji ya maka jagoranci ya baka rai da lpia yasa kayi kyakkyawan karshe ya kuma maka sakamako da gidan aljanna"tana kaiwa nan tayi shiru.daddy kwa tunda ta fata magana yayi tsai yana kallonta yana kuma yaba kaifin basira da iya magana da kyawawan lafuzza da ayshan keyi wanda gaba daya cikinsu babu wani wanda yayi magana makamanciyar tata.har hajiyar ma.ita kuma hajia da jamila dama ummulkairi sai binta suke da harara a inda ya abdullahi da kb suke ta jijjiga kai suna murmushi alamar ayshan ta burgesu.

"ah alal hakika nayi matukar farinciki da abubuwan da kuka fada Allah mana jagoranci gabaki daya"daddy yace tare da rufe taro da addu,a dan dama yayi hakane sbd aysha da bata taba koda zuwa gidan surukan nata ba ,da kuma hajia dake nuna batasonta dan kasancewarta ba yar kowa ba ma,ana basu da abin duniya.daga haka kowa ya musu sallama ya fito aka bar daddy da hajia suna tattaunawa.ummulkairi part din hajia ta wuce ranta bace ganin kb da aysha sun jera suna ta magana suna murmushi ,hakama ya abdullahi da jamila data wani manne masa kamar zata koma cikinsa wai ita a dole zata nunawa aysha ita wayayyiya ce.haka sukayi sallama kowa ya shiga motarsa mai gadi ya bude musu get suka fice kowa ya kama hanyar gidansa.

A haka rayuwa taci gaba da kasancewa cikin farinciki da kwanciyar hankali a tsakanin kb da aysha a haka har suka shafa watanni shida da aure.a lokacin ne kuma aysha ta fara rashin lpia ana zuwa asibiti gwajin farko aka gano tana dauke da cikin wata guda sosai kb yayi murna da samun cikin,sai dai cikin yazo da laulayi sosai wanda haka yasa kulawar da aysha ke bawa kb ta ragu domin yawancin kullum bata da lpia wannan ne yasa kb ya koma soyayya da yan matansa dumu dumu wanda daman ya dai ragene amma koda sukayi aure da ayshan bai fasa ba yana boye matane kawai.

  soyayyar da yakeyi da yanmatansa tasa ya daina baiwa aysha kulawa ,idan ya dawo daga kasuwa yayi wanka yayi kwalliyarsa ya fice sai kuma kwanciya zai dawo dan abincinta ma bai fiye ciba ya gwammace idan ya fita ya dauki budurwarsa suje su ci abinci mai rai da lpia mai tsada.wannan halayen da kb ya fara fito dasu sune suka sanya aysha cikin tsananin damuwa domin ya daina kulata ta kowace fuska,idan ya dawo ta masa sannu da zuwa sai kawai ya daga mata hannu ya fice ya barta a wurin.in ta tambayeshi ko ta masa laifine sai yace shi ba wani abu data masa kawai ya gajine ta barshi  ya huta,kai gaba daya rayuwar ta sauya har dai aysha ta fara tunanin ko dai cikinne bayaso,dan yanzu ko mu,amalar aure sai ya dau lokaci baiyi da ita ba.amma a haka ko zai kai karfe nawa bai dawo ba sai ta jira dawowarsa kuma koda ya dawo ba wani kulata yake ba,wani lokacin ma ita ke kwanciya a jikinsa domin suna hawa gado yake juya mata baya sai dai ita ta rungumoshi saboda sosai cikin ke sanyata jin shawa,a amma haka zaiyi biris da ita kamar bai jita ba haka zata hakura ta kwanta a jikinsa wai ko ta danji sanyi sanyi da saukin abinda take ji.

GIDAN MIJINAWhere stories live. Discover now