3

23 1 0
                                    

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

Karamci Writers Associations.
(Karamci shi ne tushen mu'amala tagari).

Vote@wattpad khairi_muhd.

_Mugun Miji_
    ( _Rayuwar Aurena_ )

Yan kasuwa ga babbar dama a gareku,ku zo ku tallata hajarku ko group dinku na kasuwanci a cikin farashi mai rahusa. Ku tuntubi wannan number 👇👇👇👇👇
09065856251. Domin more wa garabasar ta ku.

                 _3_

"Yanzu Dear, wannan matar da yaran nata ya za ayi dasu? Kin yarda da ita ne? Just look at her yarinya ce sosai ga yara why are they hare a wannan lokacin kuma cikin yanayi na ruwa?."

"Hmm! Wallahi Hub ina ganin abubuwa a cikin idanuwan yarinyar she's to young duk yadda aka yi ta samu matsala ne da mijin amma in ba haka ba saboda me zata fito a wannan lokacin ga yara."

"Na san ki da taimako da tausayi ki taimaka mata zan yi taya ki da duk wani  iya karfina ta bani tausayi kawai ina ganinta kamar Aminatu na."

"In sha Allah, ina son ta saba damu tukuna sai na fad'a maka yadda muka yi da ita."

"Shi kenan."

*

"Dakin babba ne sosai ni da yarana mun sake a cikin dakin tamkar dai gidanmu. Na jinjinawa kokarin masu gidan da suka taimaka mana da wurin zama a lokacin da bamu da mataimaki sai Allah. Tabbas akwai wani abu da nayi wanda yake da kyau da yasa nima Allah Ya aiko min da masu taimakona da yarana.

Yau na yarda da karin maganar nan da Hausawa kan yi "Duk wanda ya dauki namiji uba to tabbas zai mutu maraya." Yau gani dai ina da mijin amma baya tare dani ina da gidan ban isa in zauna a cikin shi ba ina da iyaye amma ban isa naje wurinsu ba saboda wani dalili da ni ja jawowa kaina ina da yayyu rututu amma babu wanda zan iya tunkara da damuwata duk saboda na yarda da shi na bashi amanar kaina da rayuwata i gave up all for him and to be with him. Ban taba yarda da cewa dafin cin amana na da zafi ba sai a yau da na shiga cikin sa ina zaune da mijina shekaru shidda ashe fuska biyu gare shi ya gama da rayuwata ya cuce ni ya rabani da komai......kuka ya kwace min na tashi da sauri na shige bandaki bazan iya jure wannan trauma din ba bazan taba mantawa da shi ba a rayuwata ba ko da na manta da shi yarana bazasu sa na manta dashi ba. Na tuna da maganar yayata Adda Asma'u da ta ce min "imili me yasa bazaki bi abinda muke so ba? Me yasa za ki biyewa son zuciyarki a koda yaushe Abbu yana fifita ki a kan dukaninmu saboda yafi son ki da kowa amma me yasa yau sau daya baza ki iya bin abin da yake so ba kar ki zo kina dana sani a lokacin da baki da komai ba ki da kowa da za ki runguma u re still young ki cigaba da karatunki me kika sani?...." Kukan na cigaba da yi ina ma zan iya dawo da hannun agogo baya da na gyara kuskuren da na tafka.

Sai da na gama cin kukana tsab sannan na fita daga cikin bandakin na dauki sallaya na tada sallah don kuwa ita ce kadai abin da zan iya yi dan kore damuwar da take damuna.

*

Washe Gari!.

Tun farar safiya da na tashi na gama gyara ko ina nayi shara, na gyara dakina na kunna turaren wuta na dorawa yarana ruwan wanka seda ya tafasa na tashe su suka yi nayi musu wankan na gyarasu na sa musu kayan makarantarsu.

Na dafa musu ragowar taliyar da na ajiye musu rabin leda ce daman na zuba musu man kullin da be kai cokali daya ba na sa musu dunkulen maggi suka ci na rakasu .

Bini_bini sai na duba agogo karfe goma nake son tayi sai na ga ma kamar ranar bata yin sauri kamar kullum.

Tara da rabi na yi ko na shiga bandaki na yi wanka na bude adaka ta na dauko atampa mai kyan cikin kayana da wani mayafi milk na saka na kulle dakin da mukuli na fita kan goma na karasa gidan Hajiyar nan kuwa ban sha wuya ba maigadin yau ya bar ni na shiga.

Sai da na danna kararrawar jikin kofar sau hudu sannan aka zo aka bude min wata matashiyar yarinya ce ta fito jikinta da tufaffi mai kyau.

"Ki shigo ciki." Na bita na shiga ciki. Wani dan loko ta nuna min " ki zauna a ciki Madam bata tashi daga barci ba amma ta ce min ki shiga ki dama mata kunun tsamiya ki soya mata kosai akwai garin wake mai dauke da sinadirin komai kawai damawa za ki yi ki zuba a flask ki ban zan kai wa Hajiya Babba."

Gyada mata kaina nayi kawai sai na ayyanawa kaina kenan na samu aikin wani sanyin farin ciki ne ya lullubeni na furta "Alhamdulilahi " a fili.

Saida na gyara ko ina yadda nake so sannan nayi yadda ta gaya min na had'a a gu daya na fita na kirata.

Ta dauka ta kuma yi min Umarni da in bita.

Mun fita daga wannan sashen ta wata karamar kofa da bazaka taba zata akwai hanya a wurin ba lallai kam kudi suna in da suke.

Tashin farko hancina wani irin fitinanan dadaddan kamshi ya dauko min har sai da na lumshe idanuwana saboda dadin kamshin a hancina.

Ban taba ganin falo mai girma da kyan wannan ba, ya kawatu da kayan alatu fes da shi kujerun ma abin kallo ne ban sani ba ko dan ni ban da su ba ne ko dan ban saba ganin irin su ba ne oho amma koma dai meye wannan falon ya hadu dan ya fi wancan ma haduwa.

Ga faskareren tv da wani showglass na turaruka masu yawa ban san lokacin da na kama habata ba.

A kan wani dinning ta dora tire din abincin sannan ta shiga wani daki ta rufo ni kuma tsugunawa nayi a gefen kujera na yi luff ina shakar ni'imar kamshi.

Kusan minti goma da shigar wannan yarinyar ta fito a bayanta wata dattijuwar mata ce cikin shiga ta alfarma hannayenta zubba biyu a hannun damanta na gwal ne masu kyan ado na hagu kuma guda daya yan matsakaita haka ma kunnenta.

Abin hancin ta ma na gwal ne sutturar jikinta bazan iya fadar adadin kudinsu ba amma tabbas tsadaddu ne na gaske.

Zaunawa tayi fuskarta dauke da fara'a sossai. Fara ce tana da jiki amma jiki irin na hutun nan kyayawa ce sosai da gani shuwa arab ce hakoranta tas farare ga hakorin gwal na makka a jiki.

"Barka da Safiya Hajiya Babba."

"Barkanmu ya kike ya yara?."

"Alhamdulilahi Hajiya."

"Kece kika yi min abinci jiya?."

"Eh nice Hajiya."

"Gaskiya naji dadin wannan girkin naki dan kika min dan wayanan babu abin da suka iya duk taron yuyune ba abin da suka iya har dumamawa nayi naci har yanzu ban ci abinci ba ina jiran dadadan abincin ki ashe kece nagode! Nagode! Nagode sosai na jima ban ci abin kirki "ba saboda ina kyankyamin wancan kukun arne matar gidan kuma yar hutu ce bata son aiki.

*Littafin Mugun Miji na kudi ne. Ki biya naira dari biyun ki kacal ki samu shiga group din paid novel.*

*Za ki iya biyan kudin ki ta wannan account din.*

👇👇👇👇👇👇👇👇.

*2098372249*.
*Uba*.
*Sani Ummulkhairi panisau.*

*Ko kuma ki turo katin waya na mtn ta wannan layin.*

👇👇👇👇👇👇👇👇
07042058317.

*Za ki turo shaidar biya ta wannan layin.*

*09065856251.*

MUGUN MIJI. (LABARIN AYSHATUL_IMILI).Where stories live. Discover now