(10)

44 6 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(10)

_______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Dan tsokaci

Wannan littafin me suna Sauyin rayuwa yayi duba ne akan muhimman abubuwan da suke faruwa a rayuwar mu ta yau da kullum.kamar yadda sauyi kan iya zowa Dan Adam a ko Wani lokaci na rayuwa,daga kunci zuwa Jin dadi,ko Kuma daga Jin dadi zuwa akasin sa.

Baya ga haka ya sake tabo Wani bangaren Wanda ya shafi rayuwar mata da yawa a boye,kamar yadda mata da yawa suke rayuwar rashin soyyayya a gidajen su Kuma shine reality.

Bugu da Kari ya sake cin karo da littafai da dama Wanda ya kasance duk heroes din cikin littafin mafi akasari suna rayuwa cikin wadata da kulawa ta Miji.

Shin wayyanan labarai da muke karanta wa Muna daukan su a matsayin su na labarai ko Kuma Muna daukan su a matsayin  zahiri?

Toh a gaskiya zance na littafi ba duka bane zahiri,musamman rayuwar gidan Aure.

ku bari ma na fada muku gaskiya Muna yi ne dan kayatar wa da nishadantar wa saboda in ba'a kawata muku characters din labari ma ba lallai bane ku karanta .

Nidai shawara ta daku shine ,in Kun karanta ku ruga kokarin daukan gyaran da ya kamata da shawarwarin da mukan bayar tare da tantance sakon ma da labari yake son isarwa .

Ba wai fa Dan ba'a soyyayya a gidan Aure bane.A'a! Kar a Kaini gaba Amman kam wannan labarun na soyayyar Hausa ko English novel da wasunmu ke kukan basa samu daga mazajen su dama duk tatsuniyar gizo ce.

A wannan novel me suna Sauyin rayuwa abubuwa sunci karo da abubuwan da aka Saba gani.

A next page zan zo muku da gajeran labarin da wata ta bani akan kanta Kuma duk a saboda labarin soyayyar littafi .

✨✨✨✨✨✨✨✨
💞💞💞💞💞💞💞💞
✨✨✨✨✨✨✨✨

Bayan Abida ta dawo haka ta ci gaba da rainon Yan Yaran ta su biyu gwanin sha'awa.

Gefe guda Kuma ta sake gane yadda zata ruga kauce wa duk Wani abunda tasan ze iya kawo sabani a tsakanin ta da Baban Abul.se dai fa a banza.

Yarinyar ta taci sunan Zahra ,gashi tun ba'ai Nisa ba nonon uwar ta ya amshe ta sosai tayi kyau gwanin burge wa.

💞💞✨✨✨💞💞

Lokaci ne na zafi ga tsananin rashin wuta da ake yi,ita Kuma Zahra a rayuwar ta bata son zafi.

Aka yi rashin sa'a rana ce ta juma'a kunsan yadda dama juma'ah take

Baban Abul yana nan a gida dama se lokacin sallar juma'ah yake tashi yayi wanka ya fita ,shine fa Zahra take ta canyara ihu wai ita zafi.

Abul yana bacci shi ba abunda ya dame shi,lokacin yana da 3 years ne.

Ba yadda Abida batayi ba dan ta samu ta rarrashi Zahra,amman yarinyar nan taki shiru tsakanin da Allah kamar wadda ake kwashe wa yayan hanji.

Abida har se da ta sake yi wa Zahra wanka tunda dama da safe suke wankan su su,amma duk da haka a banza ba tayi shiru ba.

A dakin Baban Abul kuwa yana bacci,ga yarinya ta hana shi bacci da Uban kukan ta .

A cewar shi wai an barta se kuka take yi saboda a dame shi.

Haka ya sa ya daka Wani wawan tsalle cikin bacin rai da fusata yayo waje .

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now