Da yake saura two weeks se suka dikufa yi mata lesson a gida bayan na makarantar su da ake musu.

Saturday ta kama ranar da za'ai exams din.exams din da ta hada Yara sa'oin su Saudatu da Wanda suka Fi su da shekara daya haka.

Yara ne daga makaranta mabanbanta wanda aka zabo su a cikin sauran dalibai Wanda suka kasance zakakuran ciki Wanda baza'ai asarar daukan nauyin su ba.

Abida ita ta Kai Saudatu gun exams din Wanda office ne na scholarship board .

Se da Baban Abul ya shaka musu bakin cikin shi kafin suka fito.dama Abida ta shiga watan haihuwar ta .

Da Allah ya taimake tana da karfin zuciya ,haka a amu ta Kai proff tayi jarabawar ta tana ta murna tana gaya wa Maman ta ko daya Bata fadi ba.

Murna suka dingi yi inda aka ce musu anan zasu zo su duba Sakamako sati biyu a gaba.

Da wannan suka dawo gida murna ma agun Yan uwan ba'a cewa komai da proff take gaya musu ko Daya bata fadi ba

Sati biyun da aka Basu suzo su duba result yayi dai dai da ranar da za'a yi wa Abida C's..

Hakan yadan daga mata hankali Amman tace babu komi Allah ze kawo yadda za'ai.

A dan tsakanin tana ta dan yawan tuna wa Baban Abul maganar C's ,Dan haka ba abun da yake se jaraba da masifa matukar aka ce yana gidan.

Gashi Yara sunyi hutun makaranta,se ya zamana kullum suna yi masa Dan abu kadan ze fara jaraba yana babatu .ko fa ba laifi bane in gaya muku se ya maida shi laifi ta hau fadace fadace.

Memakon hutun da akayi ya zama musu dadi se hutun duk yabi ya gundure su se Allah Allah suke a koma makaranta.

✨✨✨💞💞✨✨✨

Zaune take cikin kaguwa a layin asibitin  har kawo sanda layin ya zo kanta.

Mace ce har mace me jini jikin ta wadda take a team din da zasu wa Abida C's.ta Santa dama sosai tunda kusan duk haihuwa tana gamuwa da matar .

Dr Farida Abdullahi kenan.cikin fara'ah take cewa Abida" ba komai Abida,wata ranar se labari,ki Kara hakuri akan yadda kike yi kinji,batun C's Kuma na Kara Miki 3 days kamar yadda kika bukata.zanyi batun dasu doctor Mu'azzam Dan Kinga ya kama Tuesday team din su ke aiki.."

Abida ce tace "kar na katse ki Aunty Farida,Amman don Allah a mayar 4 days wallahi mafi son team dinki don Allah"

Dariya tayi ganin yadda Abidan ta marairaice saboda tafi son Farida ta mata aikin"

Cewa Dr tayi "wannan shi yafi komai sauki Abida,Allah ya Bada sa'a ,Amman kizo akan time kinsan Kuna da yawa ranar"

Cewa Abida tayi "Insha Allah zan zo da wuri Aunty Farida nagode nagode Allah ya Saka da alheri."

Sallama sukai da juna Abida ta tafi cikin farin ciki da Jin dadin turawa Hashim aniyar shi da tayi.

Kawai fa daga tace dan Allah ya daure ya je dubo result din proff shine yake ta zage zage ,wai shi an Raina shi an maida shi Dan aike ya dungi zabga rashin Albarka.

Murmushi tayi ta tafi gida ,dama ce Mai tayi ance tazo ranar shine fa ta samu ya bari da kyar ta fito.

Ranar da da zasu dubo result da safe ,da yake karfen nasara bayada tabbas.haka tazo tayi ta kokarin tashin motar Amman motar nan Taki tashi.

Ba sarki se Allah suka dauki kafa har titi suka samu Adaidaita sahu ,gashi Abida ta tsani wannan gwamutsen da ake a Adaidaita sahu maza da mata.

Cikin sa'a Wanda suka tare ba kowa ,ta gaya Mai inda zasu yace mata dari biyu.

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now