SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(7)

_______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Ba'a samu yin suna ba saboda C's aka mata,Amman Mommy taci alwashin yin sunan daga baya Koda yar walima haka.

Se da Abida ta kwana biyar sannan aka Basu sallama dama ta gaya masa zata wuce wankan gida ,Me Doki yayi tsallen badake ya dire yace ba da yawun sa ba,ba inda zataje sedai ta zauna a gidan ta tayi ko wankan daji ne bana gida ba ma.

Kamar wasa karamar magana ta zama gaske, Abida dai kuka take saboda gaba daya zaman gidan Hashim ya ishe ta ,gida ba yanci ba soyayya ga dan iskan kullen masifa,ka tattare yarinya yar gata ka Hana ta yawo,ka Hana makaranta haba..

Ita dai Mommy ba ta da ta cewa ,da Allah ya taimaka Hajiyar su Hashim tazo ta taradda Abida nata kuka ana rarrashin ta,a asibitin ne kan a sallame su dama ,

Hashim ya gama sheka mata rashin Albarka ya kafta mata rashin mutumci ya tafi,be duba rashin lafiyar da take ba,da yaron da ta Samar masa ya gama muszuna mata ya tafi.

yana tafiya se ga Hajiyar su,nan ta ji meke faruwa ta Kuma yi ta fada dan dama Hajiya irin masifaffun matan nan ne amman masu dattako da sanin ya kamata,ga Kuma mugun kirki..

A karshe dai Hajiya ta Bada izinin zuwan Abida gidan su tayi jegon ta ba tare da son ran me Doki ba..

ko da Abida ta koma gida taga danyen Kai,domin Hashim gaba daya dauke mata kafa yayi,ya watsar da Al'amuran ta ita da yaron ta Wanda yaci suna Abul Khair..

Sedai ya manta iyayen ta masu kudin ne sannan za'a musu gata ita da dan danta Koda shi be musu ba.

A dakin ta fa kayan su Madara ,Milo su ma'u zam zam ga su nama ne su farfesu kawai kake gani in ka shiga..ga uwar barka da ta samu kamar zata Bude shago daga Yan uwa da abokan Arziki so Koda be yi ba abun ba sosai ya dame ta ba

Tunda dama Uban ba Wani kaya ya Siya ba,yace sun cinye kudin kayan a asibiti na C's da taci sa'a ya biya.dama taci sa'a ya siyi ragon suna shine har take Wani tuno cewa be siyi kayan jariri ba?

Kan a cika wata guda mommy ta fahimci cewa akwai gyara a al'amarin  rayuwar auren Abida.

Amma se tayi shiru musamman tunda ita Abidar tana cikin walwala ita ma ta mance da tata damuwar.

Bata ma tuna cewa Hashim baya zuwa ganin su se ya ga dama ba.dan tun zuwan su har akayi wata Daya,sau hudu kachal yazo ,Shima in yazo ba wata magana me dadi,ze ga dan ya juya ya tafi.

Abubuwa dai gasu nan har kawo sanda Abida ta yi arba'in .a nan ne aka sake tada sabon balli tsakanin su da me Doki,tace Bata da lafiya baza ta iya komawa gidan ba ,mommy dai ta zuba ido taga ko Abida zata nemi taimakon ta ko shawara ,Amman shiru har yanzu.

Se ranar da Hashim yazo yace ta tabbatar ta koma gida a daren ranar da suka samu kwana 45 a gidan,shine bayan ta dawo dakin ta tayi ta faman rusa kuka kamar wacce aka wa mutuwa.

A lokacin ne Mommy ta shigo ta sameta ta rungume ta tana bata baki akan hakuri da rayuwa ,sannan ta nemi Jin dalilin kukan na Abida ,dake Abidan ma yar duniya ce se tace wa mommy wai haka nan ne take Jin kuka na zuwa mata ..a farko mommy se tayi zaton ko irin koke koken nan ne na sabbin iyaye da wasu matan kanyi in sun haihu ana ce mishi post natal depression ko..

A hikiman ce mommy ta dubi yar ta ido cikin ido,ta mata nasiha me ratsa jiki sannan ta sake cewa "Ko Hashim ne yake Miki abunda yake saka ki kuka?"

A nan Abida ta sake cewa ba ruwan shi,Amman cike da yarinta se tace "cewa yayi mu koma gida yau,ni Kuma bana son tafiya "

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now