Wata irin razananniyar Kara Amatullah ta kwalla tana ihun fuskar ta,Aleena ta ta so a rikice ta juya tana kallon Amatullah ganin yadda Amatullah take ihun fuskar ta Kuma ta kasa taba fuskar ta ta sai ta hau cewa innalillahi wa inna ilaihi raji'un me ta same ki Amatullah ta yadda yar jakar ta ta ta rike Amatullah, Ashfaq kuwa da da har ya bude wajen driver seat ya sauna Yana jiran Aleena su gama da Amatullah ta taho su tafi duk haushi ya cika sai jin karar Amatullah yayi ya fito a guje sai ya hango wadannan mutane sun juya a guje ai kuwa ya bi bayan su,sai ga wata mota tayi parking a gaban su suna shiga ciki ganin sunyi masa nisa Kuma ga shi zasu gudu sai ya tsaya ya dauki wani katon dutse ya cillawa na bayan Allah ya bashi sa'a ya same shi adaidai kanshi,sai fa mutumin yayi wata irin dungurwa ya Fadi kasa ganin mutane sunyi kan su sai suka gudu suka bar wannan na karshen a kasa Kansa har ya fara jini,jin ya Dave shi har ya suma.

Su ya Ammar da Anti suka fito a guje ganin abinda ya ke faruwa don da har sun ta da motar su za su wuce gida don ba za su iya da rashin kunyar da Ashfaq ya daukowa kan shi ba kwanan nan,ya Ammar yayi sauri yayi dialing number police nan da nan kuwa sai ga su da ma basu da nisa aka dauke shi aka tafi da shi IRA Kuma Amatullah aka tafi da ita hospital.

Aleena sai kuka take yi ganin yadda fuskar Amatullah ta koma duk ta lalace kamar ba ita ba Ashfaq na rungune da ita ba ya ko jun kunyar mutane,shi dai kawai so yake ya ga ta dawo cikin nutsuwar ta Amman ina. .a zuciyar sa Yana ta tunanin suwaye sukayi wa Amatullah haka suka bata mata fuskar ta da Acid.

Lokacin da su mom suka Kara so an shiga da ita dakin tiyata.ganin dare yayi shine mom ta ce wa Ashfaq ya tafi yaje ya Kai Aleena gida saboda duk ta wani gigice ta fita hankali ta,da ta cewa mom ta bar ta ta kwana mom ta ki yarda dole a kabar mom da Anti za su kwana a wajen ta.

A hanya ba mai  cewa komai sai dai lokaci lokaci Yana juyowa ya kalle ta,ita tana tunanin mai Amatullah tayi wa mutanan nan har sukayi mata wannan aika-aikar wannan wani rashin imani ne haka.jin anyi parking ta dago kan ta duk a tunanin ta an kawo gida ne sai ta gansu a wajen wasu masu gashi nama ya kalle ta ta dauke kan ta,shi abin ma mamaki ya ke bashi kamar shi ya aikata abin nan sai wani haushi haushin shi take ji.

Yace"wai ni kam baiwar Allah Amaryar bawan Allah Ashfaq me nayi ne ki ke wani jin haushi na ai ko ni na aikata wannan abin ai sai haka ballan ta na ni ba ni ba ne ba daure fuskar ya isa haka ai ko so kike zuciya ta ta buga?"ya karashe  Yana rike daidai in da zuciyar ta sa take.sai Kuma ta ga kamar ba ta kyauta masa ba domin ba ta ga ta in da yayi laifi ba a cikin wannan abun.ta rike kunnan ta turo bakin ta sannan ta ce masa "am sorry dear"wallahi al'amarin ne ya shige ni ta bani tausayi ba kadan ba shike nan fa fuskarta tayi damage fa.ya Dan shafin gefen fuskar ta yace "dadi na da ke kina da tausayi da Imani" may be idan aka fitar da ita waje ana iya gyara mata fuskar ta amman fa ba za ta dawo daidai ba fa kamar da saboda ta Riga da ta lalace but it depend da yadda acid din ya taba fuskar ta.yanzu dai mubar wannan zancen Ina so in ga cikin pet dina ya cika kafin ta kwanta barci don na tabbata ba ki ci komai ba yau iya me zaki ci yanzu balangu ko tsire na fita na karbo Miki?

Ta danyi shuru sai Kuma ta ce" ni kaza nake son ci" ya gwalo idon sa waje kamar ya ji ta ce wani abu daban "no no no pet ki dai zabi wani abun na je na siyo Miki saboda Bai kamata ki ci kaza yanzu"tace "saboda me?"ya yi kasa kasa da muryar har da matsowa wajen fuskar ta yace saboda gobe ne ranar da ni da Kai na zan ciyar da ke kaza ki ci ki koshi da hannu na a Kuma cikin dakin mu bayan an kawo min ke kowa ya tafi,so prepare your self for tomorrow " ya wani bata unexpected kiss a chick din ta,sannan ya fita waje don ya karbo mata balangu.

Aleena kam dauke wuta tayi ta Kuma ka sa cewa komai tayi saboda kiss din ya shige har cikin kanta.har suka isa gida ta kasa dago kan ta shi Kuma ya ki ce mata komai Yana kashe motar tayi sauri bude motar caraf ya riki hannun ta "why are u in such hurry?"ita dai tayi kasa da kanta."duk wannan guje gujen daga yau ne kawai gobe e warhaka in Sha Allah muna tare zama Kuma na dun dun sai mutuwa zata rabo" ya dauko ledar ya sa mata a cikin hannun ta ya murza hannun na ta yace"gud night pet I LOVE YOU "Sannnan ya saki hannun ta a guje ta fita daga motar ta wuce cikin gidan su don ta gayawa umman ta lallai yau acikin gidan su take son ta kwana tura kyauren kawai tayi ta shiga ciki ta na murmushi Amman cikin ciyar ta fargaba ce faal a cikin ta.
Tana  shiga ciki ya life kan sa kawai akan sitiyarin motar kunyar nan ta Aleena tana daya daga cikin abinda yake Kara masa son ta a zuciyar sa.kwankwasa gilas din motar akayi ya dago Kansa don yasan ko wanene zai yi masa haka"idan ka gama soyayyar sai ka wuce ai mu tafi ko ni barci nake ji"inji Amir.

******

Washe gari da misalin Karfe 12 na rana aka daura auren su Aleena da Ashfaq,Amir da Amira tare da shaidawar dubban jama'a,abin har mamaki na rinka ji yadda aka cika  a wajen nan ba masa ka tsinkekowa ka gani yaci farar shaddar shi,yau dai kowa sai da ya shaidar dariyar Ashfaq saboda ya kasa rufe bakin sa duk in da ya wulga sai dai ka hango fararen hakoran sa Yana ta gaisawa da mutane haka ma Amir.
******

Ina labarin shalelen Alhaji da Kuma Amatullah ku biyo ni a last page in Sha Allah.......

*****
07038185042

Comment

Comment

Share,vote and follow me on my Wattpad pls.
Love you all my fans😘

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now