*******
A hankali Ummy ta zare kan Nafeesah daga kan cinyarta, sannan ta share hawayen da suka gangaro kan fuskarta, gyara mata kwanciya tai sannan ta mike ta kashe mata wutar dakinta ta fito.
Falan Abba ta shiga yana zaune a tangamemen falansa yana cin kayan marmari yana kallan labarai a talabijin. Kallanta yai yace "Ta kwanta?"
Karasowa tai ta zauna tana ɗan murmushi tace "Eh!"
Ɗan shiru sukai na wasu dakiku kafin tace "Alhaji hakanan zamu barta ta cigaba da aikin nan? A duk sanda ta tafi har taje ta dawo hankalina baya taɓa kwanciya wlh."
Shiru yaɗanyi kafin yace "Shekara ɗaya muka bata tayi, yanda abin nan ke damunta har tana ganinshi kamar nauyi ne akanta, inhar ba gani tai ta sauke shi ba bazata taba kwantar da hankalinta ba, tunda mun barta saboda kwanciyar hankalinta, kema kiyi hakuri ki jirata. Nasan harda maganar mutane ke damunki sai dai inaso ki ɗinga tunawa da dalilinta nayin wannan aikin."
Kai ta ɗan daga jiki a sanyaye ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Shikenan Allah yasa hakan ne mafi alkairi, tunda dai ta samu lafiya shine fatan mu a koda yaushe in na ganta ina godiya ga Allah daya raya mana ita...." Ta karasa maganar tana share kwalla.

Yadanyi murmushi shima yace "Tunda munyi sa'a Khalifa da zai aureta yace zai jirata ta gama sai mu gode Allah."
Ta daga kai tace "shima saura shekara ya gama karatun da yake a Paris ko?"
Yace "Eh kinga dai-dai da dai-dai kenan."
A tare sukai dan murmushi.
*******
Cikin hanzari ta fito daga ɗakinta tana gyara zaman kayanta tana kwallawa Ummy kira.
Ummy ta fito daga kitchen tana kallanta, Nafeesah ta dan shagwabe fuska tace "Ummy na!"
Ɗan harararta tai tana amsawa tace "Meye kiketa wani sauri ba akwai sauran lokaci ba? Kila ma ko abincin bakici sosai ba."
Jakarta ta zugi ta nufin kitchen ta bude roba tana zuba abincin da Ummy ke yi tace "Ba lokaci Ummy banasan na dinga late nafisan na zama nice ta farkon zuwa, banaso Adnan yaga kamar bana maida hankali kan aikina."
Yanayin fuskarta ne ya canza tadan tsuke fuska tace "To in ya gani sai me? Nifa wlh sam....." kalaman Abba ne suka faɗo mata hakan yasata yin shiru, ruwa ta wuce ta ɗauko sannan ta miko mata magani fuskarta a ɗaurw tamau."
Dariyarta Nafeesah ta guntse sannan ta amshi maganin ta haɗiya ta ajiye cup din sannan ta ɗan rungume Ummyn tace "Ummy nah!"
Hannu tasa ta shafi saman fuskarta tace "Allah ya miki albarka ya rayamun ke."
Murmushi tai sannan tace "Ameen Hajiya Ummy."
Karasa ɗeban abincin tai, Barira mai aikinsu ce ta fito mata da wayarta tana cewa "Aunty wannan wayar taki sai kukan rago? ah kukan damusa? A'a kukan dai kamar na mage...."
Fizge wayarta tai tace "Barira in ma kukan alade takeyi bani sauri nake."
Dariya barira tai tace "To ki hau motarki mana? Ko kuma ki tafi dani in dinga miki aikin inyaso ke sai kiyi zamanki."
Ido tadan kifta tace "Barira wuce gashi can ana shirin Labarina a Arewa."
Ai da gudu Barira ta nufi falo tana tsale, murmushi tai sannan ta sake yiwa Ummy sallana ta fito.
Da kallo Ummy ta bita jikinta duk a sanyaye.
A harabar gidan Habu driver ya taso yana gaisheta, har waje ya rakata ta hau adaidaita sannan ya dawo ciki.
Tana isa station din motar Adnan na isowa, fitowa tai bayan yayi parking ya fito tamai salute sannan ta gaisheshi.
Komawa yai ya shiga motarsa sannan ya mata alama data shiga.
Karasawa tai ta shiga motar cikin girmamawa, bai kalleta ba yace "Me kike tunani game da case din nan? Jiya na saurari duka recordings din da kika turomin ina san naji naki ra'ayin ne."
Mamaki ne ya kamata ta dan daurw tace "Abu na farko matarnan ba ita ce tai kisa ba."
Ya ware hannayensa ya lankwashe ɗaya, tace "Banasan zargi amma gaba ɗaya matanshi ban yarda dasu ba, wanda ya kawo kara shi kadai ne nake tunanin ya fadi gaskiya."
"Good! In har zakayi bincike kowa anaso ka zargeshi wannan ya nunamin kinsan aikinki."
Ta dan sunkuyar da kai tare da ɗanyin murmushi, yace "Meyasa kike zarginsu?"
Tadanyi shiru sannan tace "Uwar gidan da matan sunyi ikirari basu san komai ba sai ihunsa da sukaji, sai dai a ɗakin Uwar gidan dana shiga bayan munsa Amarya a cell naga wannan."
Tai maganar tana cire wani dan karamin tissue a cikin jakarta, amsa yai ya bude kwalba ne a cike.
Kallanta yai da sauri yace " Irin wanda aka fada a dakin amarya?"
Ta ɗaga kai tace bansan meya faru ba sai dai ba yanda za'ai a fasa kwalba a kawoshi har cikin ɗakin da ba a kusa yake ba, sannan kayi maganar wuka wanda duk yanda na duba ba yanda za'ai ta fita ta ɗauko wuka, nayi tunanin ko zuwa tai dashi kamar yanda kake zargi sai dai bayan na fito na koma na nemi a bani ruwa insha inda naga irin karamar wukar dake jikinshi a kitchen din wanda ba shakka kenan daga gidan wukar take."
Adnan ya jinjina kai yace " Well done! Sai dai wanda ya kawo kara shima ya kamata ki sashi a list din zargi, meyasa kike tunanin bashi da laifi?"
Tace "Baya gidan sanda akai."
Kai yadan girgiza yace "A matsayinshi na yaran gida namiji ana biki meyasa baici abinci sanda kowa yake ci ba? Sannan daga jin ihu sai ya shiga ɗakin amarya?"
Shiru tai alamar nazari yacigaba " Sannan wani biki ne ake yinshi ace babu ko alamu daya nuna ana biki? Gida tsaf kamar ba wanda akai taro a ranar ba? Masu aikin su fa? Yaransu dake gidan fa?"
Nafeesah tai shiru, yace "Muktar zai nemeki akan yanaso yasan duk wani abu danakeyi akan case din nan, inaso ki bashi hadin kai ki kuma amshi kudin da suka ce zasu baki ki ajiye, ki tabbatar ya yarda dake akan abinda yakesan ki aikata."
Bata tambayi dalili ba ta mai alamar girmamawa sannan tace "Okay ACP!"
Wayarsa ya ɗauko ya mika mata, amsa tai tana kallansa.
Sa numberki, sannan kiyi dialing, nan ta saka tai dialing ta mika masa, amsa yai yace "A number ta kisa sunan mace."
Kallansa tao shikam wayarta yake kallo, a hankali ta rubuta Yusrah!
Kallan sunan yai take yanayinsa ya fara neman canzawa ya kalleta yace "Canza kisa wani."
Kallansa tai sannan ta canza tasa "Khadijah."
Shima ya rubuta Musbahu akan numberta sannan yace "Zaki iya shiga."
Fitowa tai ta nufi ciki, sai data shiga sannan ya fito daga mota ya nufi ciki shima.

*****
Ayusher Ce🏌🏻‍♀️

BINCIKEN SIRRIWhere stories live. Discover now