Page 1

575 44 1
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
'''A True Life Story'''
_Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

KARAMCI KARAMCI KARAMCI🔥🔥🔥

*Ko daga jin sunan kun san karramammu ne, kuma masu karramawa. Gidan karamci, masu abin mamaki, gidan karamci ƙungiya ce mai fitar da tsaftatattun littattafai masu ɗumbin faɗakarwa da nishaɗantarwa, a yau ƙungiya mai albarka ta cika shekara biyu da kafuwa, ina yi wa ɗaukacin members na karamci fatan alkhairi da fatan nasara a rayuwa. Allah ya ƙara mana basira da fikira ya kuma ƙara haɗa kanmu.*
_Happiest 2nd Anniversary to my forum._

_*Hip Hip Hip🎂🎂🎂*_
_Happy birthday STYLISH may this birthday be different from the rest of your birthdays in every good way. May all your fantasies come true. Have a lovely birthday.🎉🎉_

*This page goes to KARAMCI WRITERS ASSOCIATION i dedix this page to you.* *On this romantic day, may our souls come closer than ever before. I wish luck for the love and ideas we share. The magic of togetherness in the air, there is passion and there is care, that is what true love is all about Allah ya ƙara haɗa kanmu I wish that success always stay with us, in all our ways and our endeavors.*
_Ina taya mu murna cika shekara biyu da kafuwar ƙungiyarmu. Allah ya ƙara mana fikira! Ameen._

Book2
'''Page 1'''

"Me kake nufi da ka san komai?" Fauwaz ya tambaya, mamaki shimfiɗe a fuskarsa.

Zayyan kallonshi yayi sannan ya cije leɓen ƙasa. Wasu files ya ja gabansa da zummar ya cigaba da aikin da yake, Fauwaz a karo na biyu ya sake cewa "Zayyan ka sakani a duhu"
"Ai ba za ka taɓa fita daga duhu ba, muddin baka bar Amatul-ahad ba"
"Zayyan ya kamata ka gane cewa abinda kake wa yarinyar nan babu abinda zai ƙara maka face ɓacin rai, amma da ace za ka dangana ka kuma miƙa lamuranka ga Allah sai kaga ka samu da cewa a rayuwa"
Table ya buga da ƙarfi sannan ya miƙe tsaye, yana huci ya kalli Fauwaz.
"Ko waye zan iya rabuwa dashi muddin ya nemi shiga tsakanina da abinda nake yi wa Amatul-ahad, idan har ba za ka goyi bayana ba, to bana son duk wani kalamin ka, ka fitar min a office"
"Ni kake kora daga office ɗinka Zayyan?"
"Daga rayuwata ma zan iya korarka idan har ba zaka daina shiga abinda bai shafeka ba"

"Okay ba damuwa ya yi, nagode, amma ka sani ban taɓa tunanin akwai rana mai kamar ta yau da za ta zo ba, Zayyan insha Allah na daina shiga rayuwarku"

"Da yafi maka, domin ni dama ina zargi akwai wani abu tsakaninku."

Fauwaz murmushin takaici kawai yayi, ya juya da nufin barin office ɗin, Zayyan ya ce "Ka manta takardarka, please kada ka bar min ita"
Juyowa yayi ya ɗauka sannan ya fita.

******

Da sallama Islaha ta shigo ɗakin, Zaliha ta miƙe tsaye tare da faɗin "Barka da zuwa."

Da sakin fuska Islaha ta kalleta ta ce "Yauwa sannunki ya mai jiki?"

"Da sauƙi" Zaliha ta faɗa tare da ɗaukar abin sallah ta shimfiɗa a ƙasa ta zauna.

Tun zuwan su, bata taɓa ganin wanda ya zo dubasu ba bayan Fauwaz, sai Islaha da bata ma shaida ta ba.

Gefen gadon ta zauna ta kalli Amatul-ahad, jikinta yayi sanyi sosai, ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Sannu Sister, ya jikin naki?"

"Da sauƙi" Amatul-ahad ta faɗa idanunta kan Islaha, tana karantar fuskarta.

"Sister sannu, amma mene yake faruwa haka? Naga kin rame sosai."

"Bana cikin kwanciyar hankali Islaha." Amatul-ahad ta faɗa lokacin da wasu hawaye suka sauka daga kuncinta.

Itama Islaha hawaye ne suka sauka a kuncinta, amma bata goge nata ba, hannu ta saka tana gogewa Amatul-ahad hawayenta.

"Tabbas na san a wannan yanayi zan sameki, amma ina fatan za ki yafe min tsawon shekaru da nayi ina cin zarafinki."

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now