Haro yace. "Sarkin ƙira kamar yadda aka saba duk shekara wannan shekararma haka zamu yi da kai ga layar nan a duk lokacin da muka shiga fafatawa idan kaga za'ayi nasara a kaina ka dinga murzata, idan kuma har anyi nasara akaina lokacin da zaka bawa abokin hammaya kambun girmamawa ka naɗa masa a hannunsa kafin a tashi daga taron wasan al'ada zai kwanta ciwo kamar yadda muka taɓa yi da Marigari Iliya Mudubi, dan wallahi da girmana ya faɗi gwara uban kowa ya rasa." Sarkin ƙira yace. "Maganar gaskiya Haro tsoro nake ji karfa asirinmu ya tonu dukda dai ba'a taɓa samun matsala ba,  amma ina gudun ɓacin rana" Haro yace. "Haba kamar ba wayayye ba ina baka kana ƙin karɓa, kasan dai bana maka ƙaramin alheri duk shekara kawai ka share haka za'a yi" Sarƙin ƙira ya amsa tare da cewa. "Amma farashin wannan shekarar ya ƙaru sai ka ninnikamin kyauta ta" Haro yace. "Wannan mai sauƙi ne"

    Sarkin ƙira tun bai gama gani ba jikinsa ya hau tsuma a tsorace yace. "Tuba nake dan Allah ka rufa mini asiri" Sabon Bawan yace. "Idan ka bi abin da zan saka ka ba.  Kaga dai ba a gaba kuka yi ba ko?" Da sauri Sarkin ƙira ya gyaɗa kai.

   Sabon Bawan yace. "To yadda na ganku ba tare da kun sani ba haka yanzu zan ganka a lokacin da na baka wannan aikin" yana gama faɗa ya huro iska daga bakinsa nan take sai ga wata farar leda me ɗaure da wani irin gwamamman rubutu a jikinta, cikin ta wani farin yashi nemai ƙamshi haɗe da sanyi, miƙawa Sarkin ƙira ya yi haɗe da cewa. "Wannan yashin nake son ka haƙa rami me zurfi a cikin gidan Sarki ka binneshi a haka, abin da nake so da kai kenan amma muddin ka saɓawa haka wallahi sai na kasheka da kisa me tsanani." Sarƙin ƙira na jin haka ya ɗago a firgice yana kallansa bayan ya karɓa yace. "Indai wannan ne ai ƙaramin aiki ne" Sabon Bawan yace."Ka adana shi sannan ka cigaba da shagali kamar komai bai faru ba." Sarkin ƙira karɓa ya yi ya sa a aljihu sannan ya ci gaba da wasa Sabon Bawa haɗe da rawa yana waƙa kamar yadda yake bisa ga al'ada ga duk wanda ya ci.

     Sarki Aminullah jin jikinsa yake wani irin sam bai so ace ba Haro ne yaci ba amma babu yadda ya iya, bayan fitar Sarkin ƙira da Sabon Bawa sai masinta suka fito suma suka shiga nuna tasu bajintar dan ganin sun faranta ran Mai Martaba.

     Kifaye masu rai suka fito da su suka zuba a ƙasa nan take Kifayen suka fara iyo a ƙasa kamar waɗanda suke cikin ruwan bayan kamar wasu mintuna sai suka ciro fatsarsu ta kamun kifi, saida suka ɗaga ta sama suna nunawa kowa babu komai a ciki sai suka sauke suka fara bazasu duk bazawa ɗaya idan mutum ɗaya daga cikin su ya yi sai ya ɗago fatsarsa cike da kifi fiye da goma a ciki kafin wani lokaci tuni sun cika fatsar su da kifaye manya da ƙanana. Sarkin masintan ya umarci a da ayi gaggawar haɗa wuta, ba'a ɗauki lokaci ba aka haɗa wuta tare da ɗora wani babban kasko aka shiga hidimar soya kifayen manyan daga ciki kuma aka dinga gasawa, wasan ba ƙaramin ƙayatarwa yake ba dan haka mutanen garin idan bikin ya ƙarato kowa da irin shirin da yake yi.

      Basu jima ba aka kamalla wasan masinta tare da gama suyar kifi suma suka tattara kayansu suka bar wajen, fitar su babu jimawa Wanzamai suma suka shigo suka fara nuna tasu bajimtar. Ɗan sarkin wanzamai me kimanin shekara goma ya fito rataye da jakar wanzamai, yana zuwa ya dire ta a tsakiyar wajen ya juya ya gaida Sarki cikin girmamawa, daga cen ɓangaren Bafaden Sarki Aminullah ya amsa da. "Sarki ya amsa an gaishe ka Ɗan sarkin wazamai" Yaron juyawa ya yi yace. "A cikin ku akwai wanda yake buƙatar aski daga nan gurin da yake?" Kallon kallo suka fea yiwa juma aka rasa wanda zai amsa har sai da ya kuma maimatawa a karo na biyu sannan wani Matashin saurayi ya ɗaga hannunsa tare da cewa. "Ga ni" Yana rufe baki Yaron ya kalli Jakarsa ya yiwa aska magana kaman wanda yake wa mutum magana, yana gama mata magana Jakar ta buɗe da kanta aska ta fita bata tsya ko'ina ba sai wajen saurayin da ya yi magana. Kafin wani lokaci tuni ta aske kan matashin, wannan abin da yaron ya yi ba ƙaramin ƙayatar da Sarki da Aminansa ya yi ba harma da mutanen wajen.

    Sarkin Aska da kansa ne ya fito ya juya ya fara kallan mutanen gurin ɗaya bayan ɗaya sannan ya bada umarnin a kawo masa babban mazubi, da sauri wani bafade ya ɗauko masa babban bokiti yana kawo masa ya zauna a gaban bokitin ya fara kwara aman jini a ciki ya jima yana abu ɗaya sannan ya cika bokitin fal da jini, gabaɗaya mutanen guri zaro ido sukayi suna kallan abinda yake faruwa, miƙewa ya yi yace a ɗauke bokitin aje a zubar dashi a wani gurin. Yana tashi ya ɗauki jakar wanzanci ya ɗagata sama sannan ya fara wulwulawa yana ajiyeta da ya buɗe sai ga Jaririya ya yafito da ita tana ta mutsuniya a cikin tsumma a wannan lokacin gurin hautsinewa ya yi da hayaniyar jama'a, a hankali Sarkin Wazaman ya taka ya miƙawa wani Dogarin Sarki yace a kaiwa Sarki Aminullah Jaririyar.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 01, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ANYA BAIWA CE?Where stories live. Discover now