page 12

603 30 3
                                    

*♡SIRRIN ƊAUKAKA♡*
          _Wattpad@ayshajb_

®️🌁

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
[Kungiya Domin wayar da kan mata, Farin jini writer's domin ci gaban Mata.]

         _♡F.J.W.A♡_

https://www.facebook.com/FARIN-JINI-Writers-Association-109861227874440/
      
         *Barka da Juma'a*
   Wannan Page naki ne.
    AsmeebashBashir💗💋,

Free Book
Page 12
“Nashiga uku Ummi Aure wani Auren da, dashi da babu duk d'aya? taya ummi, Gaskiya Baze Yuwu ba.." a guje nayi D'aki tare da banko musu kofa duk sunyi tsaye kuka nake kaman Raina ze fita , lnada ilimi da nasan da wannan Auren yaushe Zan Riga kula Sir Nabil. Wayyo Allah, komawa nayi kaman karaman yarinya dabas na zauna, inna kirga yatsuna ,yau shekarata ashirin da hud'u, tun innada sha hud'u aka K'ak'a bamin Wannan jangwan d'in, inda nake ajiyar kud'i naje na cire dubu tamanin na nufi falo kamar mahaukaciya har yanzun Suna tsaye, har dashi daya shigo watsa mishi kud'i nayi. "Wallahi baze Yuwu ba! Ban manta jahilcin da suka nunamin ba, ga inda ake Sona ake karramani me ze kaini cikin , ukuba, Ga kud'in ka, harda Kari na maka ka barni na rok'e ka dan girman Allah.. nakasani zakuyi zaku kassaramin Rayuwa!"

Zubewa nayi saman gwiwowina "Ka dubi girman Allah da Darajan Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi a wasallam, ka rabani da Nauyin ka, Wallahi ban tsara Tafiya da kalar ka ba, ban tsara Zama Karkashin inuwarka Ba! Ban shiryawa Matanka Nafisa Zaina da Fure ba, Haukatani zasuyi kaima basu Barka ba bare ni , Loma d'aya Kayiwa girman Allah ka sauwake min..."

Rik'e kafad'unta Arab yayi Yana murmushi "Kai Wallahi sai na karajin son kasancewa Dake , Ga jarumta inna hangowa qwayar Idonki, wannan ragwantan ba Na jarumar mace i'rin Hauwa'u Jiddah bace daure Amariyata , daure ki razana min su, daure ki kwace misu ni" cik'e da murmushi ya karasa maganar , kwacewa nayi "A'a ban isa na karb'i Muazzan ba.." kuka wiwi harda majina (kazama baranyi k'awance dake ba, Gwara Nuwaih Nah)

Kwanciya nayi cik'e da Tausayi Halima tace "Toh uncle tace bata yinka ni ka daina sata kuka" kaman zata fasa ihu ta karasa maganan. Takuwa Ummi ta mata "kubar Nan!" Ta daka musu tsawa "Amma ummi"

"Bar Nan Hanisa".
Suna barin gurin Ummi tace "Rufe min baki shashasha kawai kwashe kud'in ki bar Nan kafin na shiga jikinki" mikewa Nayi a zuciye Nayi hanyar d'aki "Dawo ki kwashe" Wallahi ko juyowa banyi ba, Haka nabarta Nan ta shiga fad'a inda take shiga ba Nan take fita ba, domin ranta yayi bala'in b'aci "Tashi ka tafi"

Sanin ranta na b'ace ne ya hanashi mata magana Haka ya tafi bayan ya tura mata kud'in data bukata ,

Koda naje d'akin Suna tsaye ganin shigowata yasa suka Nufo ni "Ku barni!" Abinda nace Kenan tare da kwanciya a kasan carpet wani i'rin kuka nake inna tuna rayuwar da nayi da Sir Nabil cikin k'ankanin lokaci da sauri na kawar da tunanin tare da yin lstigfari tuna matsayi na da  nayi, Ranan Haka mukayi kwanan bak'in ciki, domin ko abinci na kasa sakawa cikina Suma ganin banci ba, ya hanasu Cin abincin ko hirar da muke na gajeren lokaci bamuyi ba , juyi kawai nake can barci ya d'auke ni.

     Mafarki.
Zaune nake ni kad'ai a wani fili me shegen duhuwa , baka jin motsi komai sai kukan Ababen halitta sunkuyar da kaina nayi kasa wani i'rin kuka nake inna lalube can na hangi mahaifiyata da sauri nace "Ummana dan Allah ki tawo gareni zasu kassara Rayuwata" kokarin mikewa nake Amma na kasa  tashi batace komai ba, Amma daga inda nake inna hango hawaye a idanunta Sallaya ta shimfid'a ta hau sallah.
Kuka nake sosai..

Kamar kiftawar bakin Abu ta fiskata yasa ni farkawa Nan na kunna wutar d'akin shuru na zauna rik'e da kaina dake wani i'rin juyawa chan na tuna mafarkin da nayi da mahaifiyata wanda rabon da nayi mafarki da i'ta na manta, jiki a mace na nufi Band'aki tsarki nayi tare da d'auro alwala Agogon d'akin na kalla naga karfe biyu, da minti shida, Sallaya na shimfid'a na tada sallah nafila nayi raka'a hud'u cikin sujjadar Karshe na fashe da kuka inna rokon Allah. "Ya Allah ni baiwarkace Allah kafi kowa sanin sirrin dake b'oye Allah nayi tawassali da sunayenka tsarkaka Allah ka jibb'aci lamarina Allah ka kawo agaji cikin rayuwata Allah idan Akwai Alkhairi cikin tarayyata da Arab Allah ka tabbatar in kuma babu Alkhairi ubangiji ka nisanta ni dashi Kamar yanda ka nisanta sama da kasa, Allah babu wani abin bautawa sai kai, Allah ban had'aka da kowa ba, Allah dakai kad'ai na dogara Allah ka saukaka min.." Haka ta ringa kuka tana gayawa Allah damuwarta har karfe Hud'u da arba'in kafin  ta idar da sallarta tana Zaune akayi Kiran sallar farko , lokacin na karatowa ta make kafar Hanisa da Halimatu. Komawa tayi, ta gabatar da raka'a tainin fajir, kafin tayi sallar subayi,

Koda ta idar bata koma ta kwanta ba, Fitowa tayi ta hau Gyara falon Hanisa da Halima suka hau , shara tana kammalawa ta Nufi kichin ta d'ora musu abin kari kunnun tsamiya da alale tayi sannan ta soya musu dankali tana gamawa ta Gyara abinda ta b'ata wanka taje tayi karfe bakwai taji motsi ummi d'akinta ta nufa ta sameta Zaune tana duba littafin addini "lna kwana ummi" ta fad'a tana Sunkuyar da kanta kasa,

Batare data d'ago ba ta amsa mata jikinta ne ya mutu cikin sanyi murya tace "Dan Allah Ummi kiyi hakuri insha Allahu hak'an baze Kara faruwa ba" murmushi tayi "Babu komai!"

Kuka na saka ganin taki ta kalleni na rik'e hannunta "Ummina fushinki masiface a gareni Zan Miki komai bazan sake sab'awa umurninki ba dan Allah ki yafe min" kad'an ya rage hawaye be zubo Mata ba, ganin yanda Jiddah take rok'onta "Na yafe miki Allah ya yafe mana"

"Nagode Ummina insha Allahu zanci gaba da faranta miki Kamar yanda kika d'aukaki lamarina zan rik'e kaninki Zan mishi biyayya kodan na samu lahirata"

Murmushin jin dad'i Ummi tayi. "Ubangiji yayi Miki Albarka"

Da ameen na amsa kafin na fita inna share qwallar dake zubomin na amsa Mata ne Dan na faranta mata domin matar tamin komai tamkar Halimatu haka ta rik'e ni.

  Bayan kwana Goma.
Duk wannan kwanakin haka Nan nayi su, domin jina nake wani i'rin ga Halimatu da suka taso ni gaba matar uncle ko kofar Gida ban lekawa karatun islamiyar ma wata malama ummi ta d'auko min inna ji inna gani Haka zasu fita Amma banda ni, in Kuma nace Zan bisu Hanisa sai tace "Bari na Kira Miki uncle Arab ki tambayeshi ldan ya Baki izini toh" tsaki nayi "Kuyi Tafiyar ku"

Zama Halimatu tayi tare da fashewa da dariya "kai Allah ya nuna min ranar da uncle Arab ze yi shagali inga yanda zakiyi" ayarin da nake taje kaina na jefeta dashi. "Toh Allah ya shiryaki sahiba"

Hanisa tace. "Uhm in-law Wallahi kina da aiki wannan Gidan zamanshi se kin shirya" D'aure gashina nayi "Nadogara da Allah zai kawo mafita"

"Amma an cuce ki in-law uncle ya tsofe shekarar data Wuce ya Aurar da yaransa biyu MashKhura da mansura 'Yan d'akin zainaba ,  d'akin zaina Wanda uku ne duk Mata, i'tace matar uncle Arab ta biyu , yanzun saura mata Marzkhura , Fure'atu nada Biyar Sadiq  Sagir Sabilah sai'rah Sajidah , Uwar Gida Hajiya kwatakwata Nafi tanada yara biyu rak  Jamil da Jumaina Allah be bata tun daga su bata Kuma ba, a duk matar shi Fure i'tace me 'ya'ya a tak'aice yaran Uncle goma maza uku Mata bakwai , Gidan uncle ana wani Abu wai  shi K'azamin kishi , domin Wallahi mata ukun Nan Gobara ne har gwara Nafi kishinta da sauki akan na fure Zaina kuwa tace in bakayi bani guri, Da har chasu sunayi ban sani ba ko har yanzun Suna yi, in-law inna tausaya miki Sabida ke yarinya ce ,  zaki shiga cikin jigajigan Boko Nafi Dr ce, Zaina ma'aikaciyace Fure kuwa Yar kasuwace domin dukk'ansu Nan Basu cika zaman gida ba sai Juma'a da sabar da Lahadi"

Ta karsa maganarta tana zauke Numfashi "Toh amma.." taya kuke ganin zan billowa rayuwar Gidanshi nifa banson tashin hankali da hayaniya yamin nawa gurin daban, Halima tace. "Me wiyar kenan Domin ya gwammace ya had'asu Sabida gwara zamansu Guri d'aya.."
~Vote And share~
Maman Faruq

SIRRIN ƊAUKAKAWhere stories live. Discover now