Abin duniya gaba ɗaya ya dami Fulani Maryama amma duk da haka ba ta gushe ba tana faɗin, " Ka taimaka mun kayimun wani abu, ni da kai kaɗai na dogara "

       Wani mugun kallo ya bi ta dashi sannan ya ce, " Baki da hankali ne a gabanki munanan abubuwa suka faru amma zaki ce na taimaka miki kinga idan kinganni a lahira kaini akai, babu uwar da zan iya taimaka miki, bincike na biyu da zan gaya miki shi ne, idan kika sa aka fitar da shi tun yana jariri to ba makawa acikin ƙasa da makwanni goma zai faɗa gurin da zai gamu da ita wannan yarinya kuma dawowarsu shi da ita bazai miki daɗi ba, dabara ta ragewa mai shiga rijiya..."

         Zufar dake goshinta ta goge sannan ta ce masa, " Marduska wai dole sai akaina wannan masifun  yarinyar zasu sauka? Kaina ya kulle fa, dan Allah ka bani mafita..." katse ta yayi da ƙarfin gaske yana cewa, " Da alama kin manta dokar kogon dutsen, azaba ta gaggawa zata iya wanzuwa agareki " sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce, " Tsafi ya dafa tuba nake bokana Sarkin bokayen duniya, ina gwanin wani ga nawa Aljani Garbunsa ya ƙara ja da zamanin ka "

     Motsa bakinsa yayi alamar jindaɗi sannan ya ɗauko wani ruwa dake cikin tukunyar ƙasa ya ɗaga shi sama da hannunsa ya fara surutunsa na tsafi, ya jima ahaka sannan ya sauko da shi ya leƙa wani tiriri ne yake fitowa, sai da ya gama kallon ƙwaryar ya ce, " Akwai wasu ɓoyayun al'amura mai tafe da sarƙaƙiya, da alama shuɗaɗɗun abubuwan baya ne zasu iya dawowa wata ƙila Tarihi ne zai kuma maimaita kansa, amma bani da tabbas harsashe ne nayi,  ƙarɓi wannan " Ya miƙa mata wata manyan layu sannan ya cigaba da bayani.

     " Ita wannan layar ki saƙaleta aɗakinki zata taimaka miki na bunnuwar wasu sirrika na ki, wannan kuma ki binneta akan ƙofar shiga gidan masarautarku, bance zata Hana faruwar komai ba sai dai wannan layar zata hana tonuwar muhimmin sirinki musamman akan wance yaran, kinfi kowa sanin dai ba jinin Aminullahi ba ne hasalima ba jinin masarautar Kano bane, to ki saƙale ta gun da kikasan bazata faɗo ba, ita wannan ta ƙofar gidan wasu aljanune zasu miki gadin bakin ƙofar don hana ta shigowa, amma banda tabbaci yaƙini nake watakila shigowar Rayzuta gidan ya sa ta faɗowa wata ƙila kuma bazata faɗo ba, kuma na lura da faɗuwar gaba a duk lokacin da zaku haɗu da ita wannan yarinyar, sai ki riƙe wannan duk lokacin da kikaji faɗuwar gaba ki dinga lura da waɗanda suke tare da ke, ni nayi iya yi na ku tashi ku bani guri "

      Jakadiya dake gefe tsumu tayi najin kalaman boka cikin zuciyarta ta ke faɗin, " Au dama Salman ba jinin Takawa bane? Lallai duk inda makirci ya je Fulani Maryama ta kai cen, babu ko tantama ɗan wajen Fulani Zulaiha shi zai zama magajin Izza, muje zuwa mahaukaci ya hau kura na tabbata akwai ranar da Ya zata ɗakin Ƙanwa, Fulani Maryama kinyi shuka a idon makwarya, lokaci na nan zuwa da kwaɓarki zatai ruwa, tafiya sannu-sannu kwana nesa. "

    Kamar Fulani Maryama tasan abinda yake ran Jakadiya aikuwa ta juyo cikin tsuke fuska ta fara mata magana, " Jakadiya duk abinda kika ji agurin nan ki tabbata da ya zama sirri banasan kowacce magana ta fito daga bakinki, bakinki ƙanin ƙafarki, kinsanni sarai kinsan wacce Fulani Maryama bani da kyau banida daɗi, idan na sake naji wata magana ta ɓilla waje to daga gareki ne, kuma insa a hallakaki ba abu ne mai wuya agurina ba "

      Jakadiya sarai ta san Fulani Maryama zatayi abinda yafi haka ma ta rissinar da kai ƙasa ta ce, "  Wane ni da wannan ɗanyen aikin ya Shugabata indai wanda ya mutu zai dawo to maganar nan zata tashi, ai duk wanda ya ƙona rumbunsa yasan inda toka take tsada, ina ni ina bayyana sirrin Uwar gijiya ta idan nai haka ai kamar na daɓawa kaina wuƙa ne "

    Fulani Maryama ɗauke kanta gefe tayi tana faɗin, " Ki tabbatar da kin kiyaye abinda kika faɗa domin ni ginshiƙin dutse ce kowa yayi karo dani shi ka faɗi, idan kunne yaji gangar jiki ta tsira " Jakadiya haɗiye yawu tayi mai ɗaci saboda jin haushin maganar Fulani, cikin zuciyarta ƙwafa tayi ta ce, " Tunkafin ahaifi uwar mai sabulu balbela ta ke da farinta, Fulani Maryama dani kike zance wallahi duk wannan wulaƙancin da kike mun akwai lokacin da zan farke miki laya. "

      " Muna godiya Ubangidana maganin kuka na dukda yau ce rana ta farko da zan fita daga kogon dutsen bada biyan dukkan buƙata ba, amma  ni mai bin umarnin ka ce akan duk abubuwan daka gindaya mun, tsafi ya dafa hatsabibancin ka ya cigaba da wanzuwar har ƙarshen zamani " Fulani Maryama ta faɗa tana karɓar layun da ya bata.

      Cikin jindaɗin kirarinta ya ce, " Taɓewa ta tabbata ga mai yin shirka kije tukwicin aikinmu na ga cikin bayin Masarautar ku kamar yanda muka saba duk lokacin da kuka ziyarce mu, zan ƙara miki tuni idan kun wayi gari da mutuwar wani bawan babu ku babu cin kayan sadakar inba haka ba zaku bishi, ku fice daga kogon dutse kuna masu ambatan sunan mu " yana gama faɗa ya ɓace daga gurin, Jakadiya da Fulani tashi suka yi suka fita, suna zuwa bakin kogon dutsen Fulani ta kuma runtse idonta tana karanta ɗalasiman tsafin, atake haske ya kuma mamaye su suka ɓace daga gurin.

        Lokacin da suka koma cikin Masarautar tuni dare ya tsala babu motsin komai sai kukan tsuntsaye da ƙananan dabobbi, Fulani karɓar Salman tayi dake hannun Jakadiya sannan ta ce mata, " Ƙuda wajen kwaɗayi akan mutum ina fatan baki manta maganar boka ba " rissunawa Jakadiya tayi ta ce, " Ina ankare ya shugaba ta "

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

ANYA BAIWA CE?Where stories live. Discover now