Aleena ta sunkuyar da kan ta kasa da jin abinda ya fa'da a karshen maganar sa,don Sai maganar ta ba ta kunya,wai yara?abinda ko auren ma ba ayi ba Amman ya fara ambatar yara hmm.

"To nagode"

"Bangane kin gode ba nayi mana addua ba za ki iya cewa Amin ba lallai ma yarinyar nan"

Ta ce tao ai nace nagode hakan ma ya wadatar Kuma na fa'da a cikin zuciya ta.to ban yarda ba sai kin fa'da a fili na ji tukun na

"Wallahi ka fiya rigima,to naji nace Amin, shike nan?

Sai kawai ya d'aga mata gira a maimakon ya ce eh.murmushi kawai tayi ,cikin zuciyar ta tana Kara jin son sa da farin ciki da yiwa Allah godiya da ya bata Wanda ya ke mutukar son ta.don a d'an tsakankanin lokacin nan ta Kara tabbatar wa kan akan irin son Ashfaq ya me mata.

Daga can nesa kuwa Mom da umma ke kallon su suna dariya don duk abinda ya faru har punishment d'in da aka bawa Ashfaq yayi,duk a kan idanun su.

Mom tace"umman Aleena kin ga soyayya ko?to nima ki Dan bani labarin soyayyar ku ke da Abban su Aleena.
Sai suka kwashe da dariya dukkan su,sannan suka bar wajen.
Su kuwa wadancan masu maganar Sai Kara shiga cikin jama'a ake yi ana ta hotuna wai tarihi 😜
*****
"....Yanzu Kai Annur abinda ka za bar wa kan ka ke nan saboda Allah,me yasa ba za kayi tawakkali ba ka hakura,yarinyar nan ba fa rabon ka ba ce,don da rabon ka ce da tun farko za ka yi min biyayya ka je ka ganta ku daidai ta Amman ka ki a lokacin.saboda haka kayi hakuri Allah zai kawo ma ka wacce take alkhairi ce gareka ka ji yaro na"ta fa'da da sugar lallashi kamar tana lallashi Karin yaro

Tari ne ya ka mashi tare da rike kirjin sa daidai wajen zuciyar sa da take yi masa ciwon don ji yake kamar ya tsaga kirjin ya fito da zuciyar ta sa saboda azaba.

Da 'kyar ya bu'de baki cikin sanyi murya yace"momy wallahi zuciya ta ke ciwo kamar za ta tsaga kirjina, wallahi wallahi momy Ina son Aleena ni bansan lokacin da son ta ya shiga zuciya ta ba har ya masifar kamani haka momy....don Allah ki taimakamin na mallaki yarinyar nan, wallahi zan dai na duk abinda na keyi da bashi da kyau"
Ya wani ha'de hannun su duk ka biyun alamar roko.

Nan da nan Sai tausayin yaron na ta ya kamata tana jin kamar take ta gayawa Aminiyar ta gaskiya cewa fa Annur Yana son Aleena da gaske,Kuma tuntumi ta ke da sha'awar taga ta ha'da su.to ta tabbatar ko ma da waye za ayi bikin fasawa za ayi saboda tasan tana daraja da kima a idanun bayin Allah nan.
To Amman in tayi haka ta kyauta kuwa? Na farko ga yaron da za ayi bikin da shi ta yi masa adalci kuwa saboda ta ta son zuciyar?suma Kuma iyayen Aleena za ta mai da su kananan mutane Kuma ba tayi musu adalci ba.sai ta yanke shawarar bari kawai ta cigaba da lallaba shi akan za tayi wani abun har dai a samu ayi bikin nan,idan ya ga hak ai ya hakura ko?

"Kayi hakuri Annur in Sha Allah zan yi wani abu a Kai Amman fa ka sani matar mutum kabarin sa."
Yace to momy na gode nasan ba zaki bar yaron ki ya shiga wahala ba,to Amman zan iya zuwa na ganta...?

Da Sauri momy tace " a'a ka bari Sai na gama komai tukun na,Sai ka je wajen na ta,to Amman fa ka sani Sai kayi min alk'awarin zaka dawo daidai yadda ka ke harkokin ka Amman ban da halayyar da ba na so"

Nodding kan sa yayi yace "yes momy I promise I will change mutukar zan Sami Aleena

            

      A gefe guda Kuma tana tunanin Irin gudumuwar da za ta bawa Aminiyarta.
            
************

      Tun da yayar su Ashfaq ta iso gari ba abun da ta hau yi sai gyara Amare take in and out,don ba iya Amira ba har da Aleena take had'awa ta dauke ta tamkar Amira,haka kawai take kaunar yarinyar tun wani zuwa da tayi daga abuja,da ta zo ta ganta take son ta.lokacin da ta ji cewa Ashfaq Aleena ya ke so tayi Murna sosai da farin ciki 'kanin ta zai Sami mace gari ga kyau ga hankali ga gidan su suna da dattako.

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now