Sai da Hanan ta dawo daga rakoshi, ko zama bata yi ba tace "Allah ya shirye ki, wai ke kunya"

"Allah Hanan baki da kunya, kina gani na kika cigaba da kwanciya a jikinsa"

"Toh ya son ranki" ta fad'a tana yin fari da idanun ta.

"Tabe baki Abrar  tayi tace "A'a babu"

Dariya Hanan ta sake yi mata domin idan ta tuno irin juyin da Abrar tayi sai ta kasa rike dariyar ta.

Murguda mata baki Abrar tayi tace "wallahi in kika isheni da dariyar nan sai na koma gidana, dama kika samu zan wunin miki"

Dif Hanan ta dauke dariyar muguntar ta hadi da cewa "yeeeeeh da gaske zaki zauna har yamma?" jinjina kai Abrar tayi murmushi dauke kan fuskar ta...

Rungume ta Hanan cikin farinciki kana tace "zauna in baki story" Abrar sarkin son labari ta ce "bestie am pregnant fa, yau wata biyu kenan"

Wani tsalle murna Abrar tayi ta rungume Hanan, sai ga suka gama murnan su Abrar tace "wayyo dadi! Kice mun kusa zama Mummy's, toh Allah ya raba ki lafiya bestie na"

Cikin jindadi Hanan tace "Ameen ya Allah, ke ma Allah ya baki".

Da "Ameen" Abrar ta amsa cikin farincik'i domin bata taba damuwa ba, haka shima Aaban, saboda sun sa a ransu cewa haihuwa ta Allah ce, kuma lok'aci ne, ba kuma sun wani jima bane balle su sa K'ansu a cik'in damuwa...

Haka suka cigaba da hirar su gwanin sha'awa, sai bayan sallar azahar Aaban ya samu sararin k'iran Abrar, tana kwance a dak'in Hanan d'omin wani bacci bacci mai d'ad'i ke fizgar ta, har mamaki tak'e d'omin ita ba ma'abociyar baccin rana bace, har Hanan na tsok'anar ta wai ta samu ne, dariya k'awai tayi mata d'omin ita kam bata ji wani alama na masu cik'i a gareta ba...

Har ta fara baccin ringing d'in wayar ta ya tashe ta, idanun ta a lumshe ta yi sallama cikin zazzak'ar muryar tace
"Assalama alaykum, pure heart"
Wa'alaikumu salam, wifffffyyyy"

Yanayin yand'a ya kira sunan ya sa ta kara lumshe idanunta, "kina lafiya, yana ji muryar ki so slow hak'a?"

"Bacci" tace a tak'aice.

Ya dan yi mamak'i jin wai zata yi bacci da rana, abun da bata yi, amma a fili sai yace "have you eating?" ( kin ci abinci?)
"Yeah pure heart"
"Good girl, bari na barki ki kwanta, amma kafin nan ki fad'a min wani abu mai dadi"

"Murmushi tayi tace " toh in yi maka wak'a?"

"Yeah sure ina so" ya amsa mata yana gyara zaman sa kan k'ujeran office d'insa.

Cikin zazzak'ar muryar ta mai d'auke da amo na bacci ta fara yi masa wak'a kamar haka...

_Ehh a bayanin farko Kaine hasken da bai rabarka. A misalin farko kishina bai bari watta ta kusheka, tunda ka zama bango rabarka sai ni kadai matar ka tausayi da kulawa nice na dace na kwanta kirjinka. Ruwan gubar yanmmata ko sun shaka zasu amayoka muyi gama kar muyi baya fushi ko fada babu tsakanin mu..._

Wani lum lumshe ido Aaban ke yi, yayinda wani sanyin dadi ke ratsa kunnenwansa, saboda gardin muryar ta. Cik'in shauk'in soyaayya yace " sing more please wifffy"

Turo baki tayi tace " pure heart baccin yaci karfina fa" 

"Its ok, yi baccin ki, love you bye"

"Love you too" tace tana gyara kwanciyar ta.

*KARFE BIYAR NA YAMMA*

Zaune Abrar take ta yafa mayafin ta da alama tafiya zata yi, sai faman k'iran wayar Aaban t'ake bata shiga, cikin damuwa tace "hanan bari na tafi gida nayi girki kila aiki ne yayi masa yawa"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 21, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now