jin kanta zai fara ciwo, yasa ta lumshe idanunta yayinda wasu zafafan hawaye suka shiga zubo mata, tana kuma tunanin ko ina take yanzu? A hankali sautin kukan ta ya fara fitowa fili, yayinda idanunta ke a lumshe...

cikin damuwa yace "decent one, kiyi shiru, ciwon ki baya bukatar kuka please"...

saukar muryan sa ya sa ta ware idanun ta, hannun ta dake cikin nasa ta fincike tace  "who are you? waye kai? ko shine ya turo ka ka karasa rayuwata? ai ga ni gabanka ka yi yadda kakeso dani"... ta karasa tana fashewa da wani mugun kuka mai matukar ratsa zuciya.

ko kadan bai ji dadin kalaman ta ba, amma sam bai ga laifin ta ba, domin ta ga rayuwa wanda kafin tabon ya bar zuciyar ta za a dau tsahon lokaci...

"Decent one i will explain everything, zan yi miki bayanin komai, amma ki kwanatar da hankalin ki, maganar na bukatar nutsuwa"...

cikin kuka ta katse shi tace "ni banason sanin komai, ka gayamin kai waye? ina nake? "....

runtse ido yayi da karfi kana ya waresu yace "kina india mumbai, wani zaro ido tayi cikin mamaki abinda yace, mamaki bai gama kama ta ba sai da ta ji yace
"kuma ni mijinki ne"...

gaban ta ya bada wani mahaukacin bugawa, duk da babu karfi a jikin ta hakan bai hana ta mikewa ba, tana masa wani duba daya kasa tantancewa, kuka tasa, kana tasa dariya hadi da tafa hannuwanta, kai tsaye zaka san cewa kukan da dariya ne na matsananci damuwa... "kana cikin tunaninka kuwa? kada ka yaudareni, domin babu mutumin da zai auri ragowan mijin am... ta kasa karasawa dalilin wani mugun kuka daya taho mata...

sumbar kansa ya hargitsa da hannunsa hadi da cije labbansa da karfi domin kukan ta yafi komai dagula masa lissafa, hannunta ya sake kokarin rike wa taki bashi daman hakan, bai takura mata yace "ya kamata ki nutsu haka, nasan cewa kin manta rayuwan da muka yi a baya, a sakamakon memory'n ki da ya dawo, shiyasa nakeson ki bani dama, nayi miki bayani"... ya fada cikin lallashi.

shiru tayi babu amsa sai kukanta daya cigaba da tashi wanda hakan bai kamata ba saboda lalurar ta...

ganin  bata son bashi dama, ga kuma kuka n da take yi yasa shi mikewa ya bar dakin, office din doctor Irfan yaje yace masa ta farka kuma memoryn ta ya dawo, murna sosai doctor'n yayi ya kuma ba shi tabbacin cewa zuwa gobe ko jibi za'a basu sallama, jinjina masa kawai Aaban ya iya yi hadi da bashi hannu suka yi musabaha, wajen hospital din ya fita da motar Irfan, kasancewar ya san garin sosai duk da an kwana biyu rabon sa da mumbai din, wani hadadde'n restaurant ya je ya yi mata take away na lafiyayyen abinci, domin shi kam baya jin zai iya sa komai a cikin sa saboda halin damuwar da yake ciki....

kamar yadda ya tafi ya barta haka ya dawo ya same ta, gaban gadon ya karasa yace " decent one, tashi ki ci abinci"

idanunta da suka yi jajir ta kafa masa kana cikin kuka tace "bana ci, ni ka mayar da ni inda ka dauko ni, ban san waye kai ba"...

"huci mai zafin gaske ya furzar, yama rasa tunanin da ya dace yayi, domin ta hargitsa masa tunaninsa duka, kalma mafi ciwo da ta ce bata san shi ba...

Cikin son danne bacin ransa yace "Am sorry, zan miki bayanin komai matukar kika bani hadin kai, amma yanzu ki ci abincin"...

"Nace maka bana ci, ka rabu da ni, ka tafi!" ta fada cikin kuka mai karfi  har da majina (Awwwnnn dirty Abrar😜)

sanin cewa yawan kukan da damuwan zai iya ja mata wata matsalan, hakan ya sa shi barin hospital din, sarai yana juyo ta tana cewa "Ni kadawo ka fadamin ta ya ya na zama matar ka"... amma ko juyowa bai yi ba ya tafi abun sa

tana cikin hakan doctor Irfan ya shigo ganin halin da take ciki ya sa shi yi mata allura domin tasamu hutu a brain dinta

bangaren Aaban kuwa hotel din da suka sauka ya nufa, haka ya zauna a hotel din cikin matsanancin damuwa duk da yanda idanun sa ke kwadayin sake tozali da kyakyyawar fuskarta...

Sai ranar da za a sallameta ya koma hospital din, domin yafada wa doctor Irfan ana kai mata abincin, direct office din doctor Irfan ya je, bayan sun gaisa da taba hira irin na abokai,  sai ya basu sallama, godiya Aaban yayi wa Irfan ya fito.

dakin da take ya nufa, tana zaune kan gadon tayi tagumi, har ranshi bai ji dadin ganin ta a wanna yanayin ba, gaban gadon ya karasa hadi da riko hannuwanta yace "decent one, ya jikin ki?"
jinjina masa kai tayi alamun amsawa yayinda hawayen suka biyo baya... domin sai bayan tafiyar sa tayi tunanin cewa bata yi masa adalci ba, domin mutum da ya kawo ta asibiti bai cancanci irin kalaman da ta gaya masa ba, domin bai yin  kalan mugunta ba sam, kallon breakfast din da aka kawo mata yayi alamun bata ma ci ba, "sauko kiyi breakfast" ya fada cikin muryansa ta ainihin  Aaban da baya daukan raini...

sum sum haka ta sauka kasan carpet din, debo abincin yayi ya nufi bakinta yayinda fuskar sa ke daure alamun ba wasa, kallon sa tayi, sai kuma tayi saurin dauke idanunta tana bude dan tsut din bakinta...

ba laifi ta ci abinci sosai, daya kara debo abincin zai bata ta girgiza masa kai hadi da juya akalan spoon din zuwa bakinsa, har ransa yaji dadin yanda ta nuna kulawa wa cikinsa,   hakan yasa yaci ba don yana jin yunwa ba, sai dan ya faranta mata...

bayan sun gama ya ce ta tashi su koma masaukin su, domin an bata sallama, nan idanunta suka yi rau rau alamun tana daf da sakin kuka... "mu tafi nace" ya sake fada... kuka ta fashe da shi tana cewa "dan Allah ka gayamin waye kai? ta ya ya zan bi ka bayan ban san ko kai waye ba"...

"I will explain, but for now dai mu tafi"...

ba musu ta bi shi a baya suka bar hospital din... bayan sun isa hotel din, ya ajiye wayoyin sa kan gado ya nufi toilet wanka yayi ya fito daure da towel a jikinsa, tana ganinsa a haka tayi saurin yin kasa da kanta, abin dariya kuma sai kawai tasa kuka tana cewa, "Dan Allah kayi hakuri, wani abu ya sake samun mutuncina zan mutu!!!"

Dariya ta bashi sosai, domin sarai ya fahimci inda ta dosa, amma san bai yi dariyan ba domin dariya ba dabi'ar sa bace... kananun kaya yasa, kana yace ta tashi itama tayi wanka tace; tayi wanka a  asibiti, bai takura mata ya kyaleta...

"Idanun sa a lumshe yana tunanin ta inda zai fara gaya mata komai yaji saukan muryanta, tace
"please ka gayamin dan Allah!"
ware idanun sa yayi yace "ta ya ya zan gaya miki kin cika min kunne da kukan ki"

saurin hadiye kukan tayi tace "na daina"

numfashi yasauke hadi da kafe ta da idanun sa masu kyau yace" A ranar 20/6/2015  da misalin karfen ukun dare na tarar dake yashe a kasa a dai dai bakin gate din hospital dina, cikin mayuwancin hali..... nan ya shiga gaya mata komai da komai, idan nace komai ina nufin komai har izuwa ranar da ta dawo da memory'n ta...  sai dai bai gaya mata cewa shi din yayan Hanan bane, ya bar hakan a matsayin suprise, numfashi ya sauke na maganar da yayi domin rabonsa da magana mai tsayi haka ba zai iya tuna wa ba...

Kuka mai dauke da abubuwa daban-daban Abrar ke yi, domin tabbas kwanan watan daya fada shine ranar da alhaji Shettima ya soma yi mata fyade, da kuma yake  bata labarin, ita ma sai komai ya shiga dawo mata daki -daki....

wani kima, mutumci, darajan sa duk suka darsu a ranta cikin yan mintuna, yayinda ta bashi wani kyakyyawan masauki a zuciyarta...

Daman a rayuwa zata auru? akwai wanda zai iya auran ragowan mijin ammin ta, duk da ya san cewa ita din bata tare da budurcin ta? hakika bai cancanci butulci ko rashin da'a daga gareta ba, kuka tasa yayinda tayi saurin fadawa jikinsa tace
"am so sorry please,   ka yafe min a bisa kalamai na a gareka"...

kara rungumeta da kyau yayi ganin ta fahimce shi, sosai damuwa ke barin zuciyarsa, a daliin fahimtarsa da ta yi "na yafe miki, domin nasan cewa halin matsanancin damuwar da  kike ciki yasa kika yi haka, domin ke mai tarbiyya ce shiyasa kika dace da suna decent one, i love you so much"...

kukan tasa hadi da cewa "i love you too, Pure heart" tabass babu sunan da ya dace dashi face wanna, domin shi din na daban ne cikin dubban samari...

murmushi Aaban ya saki yayinda sanyayyar hawaye ya biyo kuncinsa, har ranshi yaji dadin karbuwan daya samu daga gareta, cikin wani shaukin sonta yace "Wiffy please ki maimaita" murmushi tayi yayinda ta maimaita pure heart din cikin muryan kukan da bai gama sakin ta ba...

mikewa yayi ya daga ta cak sama, yayinda ya shiga juyi da da ita a tsakiyar dakin, rike shi ta yi da kyau tana dariya sai da ya gaji dan kansa suka zube kan gado suna mayar da numfashi yayinda fuskarsu ke kallon na juna, hannunsu sarke dana juna....

SHARE SBD ALLAH✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌❌

Noor✍

https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now