Kallonsu Hanan ke yi kallon so hadi da murna, taji dadi da Abrar ta samu me sonta tsakani da Allah ba dan wani Abu daya gani a jikinta ba, ya kuma kasance yayan'ta ne ke mata wanna tsananin son, domin tasan halinsa kaf, tabbas Abrar na bukatar farinciki domin irin wandan'da suka fama da irin wanna kaddarar na bukatan abokin rayuwarsu ya kasance mai son su fisabilillah ba dan wani abu nasu ba, saboda kaucewa wulakanci, amma idan ba haka kullum suna cikin damuwa kadai'ci Wanda ze cigaba da hargitsa kwakwalwarsu, za kuma su dinga ji ajikinsu tamkar sun bambanta da sauran al'ummah duniya... Ajiyar zuciya me tafe da k'walla Hanan ta saki kana ta karasa wajansu.

"Ya Aaban"... ta kira sunanshi

"Yes little" ya fada yana dan waiwayo wa domin Sam be ji shigowarta ba.

"yaa Aaban am so happy for you, can't wait in ga ka auri bestiena"...

Murmushi ya sakar mata hadi da cewa
"soon little, soon in sha Allah"

"Murmushi farinciki itama ta sakar masa, hannun Abrar ya kamo yace " little kin tuna wanna zoben?"

Dan waro ido tayi tace "yes! ya Aaban wanda ka siyomin ne, be mun daidai ba, amma how comes ya zo hannu bestie?"...

"Good" yace kana ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba "da ring dinnan hadi rigar jikinta kinsani ke na siyo wa, amma ina yawan manta rigar a asibiti, nina sanya mata, wanda bansan dalilina na yin hakan ba, ashe matsananci sonta ne ya kama ni..."

Dariyar murna hanan keyi, ba shakka Abrar ko tace soyaayar Abrar na neman sanja ya Aaban, yau ya Aaban ke bata labari, ta fahimci duk rashin son maganarsa amma idan Abu ya shafi Abrar ya kan daure yayi magana.

"Amma ya Aaban nayi mamaki sosai ace duk shekarun nan muna tare da Abrar amma ban taba lura da ring din hannunta ba? Ikon Allah" tace tana jinjina kai sai kuma ta motsa wajen Abrar sosai kana cikin wasan tsakona ta kamo hannunta hadi da cewa "gaskiya bestie ciro min kayana da ring dinnan ai kin mora ya isa haka"...

Abrar ihu tasa ta shiga dukan hannun Hanan hadi da turo dan tsut din bakinta kai kace Hanan din yankar ta tayi, idanunsa alumshe yace " I swear Hanan kika bari hawayen decent one ya zuba ko kadan ne sai kinyi kukan kema"...

Dariya hadi da rufe baki Hanan tayi tana barin dakin, dama tsokanarsa tayi so take taji abunda ze ce.

"Haba Mummy dan Allah ya zaki yi haka? ya zaki amince da auran wanna mad girl din, bayan bakya sonta da ya Aaban, ni wallahi banason zamanta a gidanan mummy so kike muji kunya dan Allah?"... Amal ta fada cikin zuga mummy.

'Hmmm Amal ya zanyi? Duk sun kasa fahimtata, ga Aaban na shiga damuwa duk adalilinta da dalilin kin amincewata ina lura da shi sarai, you no inason farincikin dana banason damuwarsa, ga daddy'nku is angry at me, idan ba haka nayi ba, kina tunanin hankalina ze kwanta ne Amal?"....

Turo baki Amal tayi cikin jin haushi, tana kuma fatan Allah yasa Abrar ta kasa cika sharadin mummy'n ayi waje da ita...

Bangaren alhaji shettima kuwa, yana zaune yana jiran aiken daya yiwa PA dinsa, yana zaune a office din sa yana aiki kai kace mutumin kwarai ne, kwankwasa kofar aka yi, ya bada izinin shigowa ganin tahir ne PA jikinsa yasa shi cewa
" yawwa tahir ka gani ko?"
"Yes yallabai ai baya boyayyen wuri kan gado na ganshi" tahir ya fada yana Mika masa cikin girmamawa...

Har tahir ya juya ze fita sai ya juyo cikin sauri domin so yake ya sanar da alhajin Shettima'n kila yayi masa kyautar ban girma.

"Yallabai ashe ka kulle madam a daki ka manta, dana je wallahi naji bugun kofa na bude mata" ya karasa cikin washe 32 teeth's (hakoran) dinsa...

Alhaji Shettima jiyayi tamkar an buga masa guduma, kana ya tsaya cak! Daga bude file din, take idanunsa suka yi jajawur, mikewa yayi ya zagayo daidai saitin inda Tahir ke tsaye cikin wata murya dake nuni da matsanancin fushi yace "Tahir ka bude mata kace?" Ya fada yana cakuman kwallar rigar Tahir din, cikin zaro ido tahir ya ce "eh na bude mata tace kai ka rufe.... Ai Tahir be kai aya ba alhaji ya bashi wani kyakyawan naushi kana ya shiga sauke duk wani fushinsa akan tahir din, sai dan kanshi ya sake sa hadi da cewa " wallahi yau zaka bar kamfanina, tunda aikin da ba'a saka ba kake yi, ka fita na sallame ka, zan turo maka kudinka na aikin rabin watan dakayi" yana fadin haka ya dau wayarsa yana kokarin kira....

"Yallabai ka taimaka min dan Allah ka rufamin asiri, ina da iyali da ya'ya ya zanyi ga rayuwa tayi tsada, ga samun aiki da wahala, bazan kara ba ka taimakeni dan Allah!!!" Tahir yace cikin kuka me ban tausayi tamkar dan karamin yaro

Dago jajayen idanunsa yayi yana ya sauke su akan Tahir ko kad'an ya ki jin tausayin sa, duk da shi din abin tausayi ne, cikin wata murya dake nuni da yana daf da aikata komai yace "ka fita a office dina idan ba haka zan kasheka, zanyi iya kasheka TAhir, kasan asarar daka ja min kuwa? Toh kasani bazan taba iya dawo da kai ba, kai ko matsayin masu goge-goge bazaka samu a company'n SHETTIMA ba!" Ya fad'a muryansa har wani amsa amo take yayinda bakinsa ke kumfan bala'i ...

Sum sum Tahir ya juya ya fita ganin alhaji ya burkice tamkar wani sabon kamu, shi yanzu yazasu rayu da iyalansa shine damuwarsa da wanna tunanin ya bar company din....

"Hello kwaro kana jina inaso ku zagaya abuja da kewanta ku nemo.... Ai kafin ya karasa manu ya warce wayar yana cewa " alhaji da matsala fa, mun ga yarinyar nan, amma kwaro yaki amincewa ita ce da shegan mutsu bala'in sa, daga baya dai muka fito domin ganin ko ita ce mu kwamusheta, sai muka ga wayam motarsu babu alamarsu...

Cikin fushi hadi da fitar hayyaci alhaji Shettima ya buga wayarsa da bango, rigar jikinsa ya cire ya shiga fiffita da ita, duk da Ac daya cika office din amma jiyayi iska hadi da sanyi dayake shaka tayi masa kadan! Ya sani ammi ta gudu, sai kuma ya saurin cewa "a'a nasan bazata gudu ba, Rahilat na sona sosai" yar karamar wayarsa ya dauka ya kira security akan kada su bar ammi ta fita, take security ya sanar da shi "ai ta fice tun dazu alhaji"... Ihu yasa ya shiga wulli da takardun dake kan table, komai yazo ya kwabe masa alokaci daya shi yanzu ta ina ze fara neman uwar da yar.....

SHARE✔
COMMENTS✔
VOTE✔
EDIT❌

Tnx all da soyaayyar da kuke nunawa books dina, noorEemaan loves you all.💞

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now