jinjina kai yayi alamun "toh" duk da yayi mamakin abunda tace toh kenan meye matsalarta? ya aiyana aransa yana nufan side din nashi, sai duk suka bara masa baya, suna zuwa kofar dakin suka tsaya domin har yanzu dariyar hadi da kukan na tashi.

ko dar be jiba ya shige dakin, hannu yasa ya rike kugunsa, ganin yanda gaba daya ta sanja masa kamanin daki, tamkar dakin mahaukata, kallonta yayi yaga gaba daya gashinta ya kara hargitsewa ya dawo gaban fuskarta duka wanda hakan yasake rufe face dinta.

cikin tafiyar sa ta burgewa yakarasa wajenta hadi da karbe wani kwalben turarensa  data fasa, g jini ahannunta da alama ta caka wa kanta, tana jin ya karbe ta fasa wani ihu hadi da bubbuga hanunsa sai ta dau pillow ta shiga dukkansa dashi, hannunta ya damko kana cikin husky voice dinsa yace "will keep the hell out shout"
kamar kuwa taji tayi shiru din, sai kuma ta fara kyakyale dariya har da kifewa kan gadonsa, wasu allurori ya hada mata  yayimata babu jimawa kuwa  bacci yadauketa, take ya fahimci matsalarta, duk da shi karatunsa ba bangaren kwakwalwa yayi taba, zai yiwa abokinsa musaddiq magana ya zo duba aihinin matsalan domin ya tabattar...

kallonsu mummy yayi yayinda ya hango tausayinta a idanunsu, domin kwantar musu da hankali yace "kada ku damu mum nayimata allura xata dau lokaci bata farka ba"
"toh son, bazaka ci abincin ba?"
"no mum sai dare"
"ok ka kula da kanka please, ko hanan ta gyara maka dakin, tunda bakason masu aiki suyi maka"
"noo mum, i will do it my self tnx" yafadi haka yana bata peck (sumbata) a kumatu.
murmushi tayi kana suka bar wajen

bayan ya cire rigar suit dinsa, ta cikin data kasance fari ya tattare hannun, nan ya shiga aiki, komai data hargitse ya mayar da ita muhallinsa yayinda wadanda suka fashe ya zubar a waste bin( kwandon shara) kana ya share dakin ya goge take dakin ya dawo hayyacinsa, wanka ya shiga bayan ya gama yasa kananun kaya marasa nauyi ya dawo kan sofa, sai kuma ya mike ya bude wardrobe dinsa ya ciro rigar abrar dinnan data yayyage, ya kwanta kan sofa ya bar rigar kan fuskarshi yayinda yake shakan natural body scent dinta dake sa masa nutsuwa, tunaninta yake as usually yayinda kaunar ta ke karuwa aransa, kiran sallah magriba ne ya katse masa tunaninsa...

washegari yana off hakan yasa shi kiran doctor musaddiq abokinsa, wanda ya masa alkawarin zuwa da rana tunda yana half day ne, kamar yadda ya alkawaranta sai gashi da rana da kayan dazai mata gwaji domin daman aaban yayi masa bayanin yanayin ciwon nata, bayan ya gama duba ta, suka dawo falon kasa, nan ya shiga yi musu bayanin ciwonta tamkar dai yanda likitan nan a cyprus yayiwa hanan sai dai bambamcinsu shine, wanna karon ciwon ya sake ninka na baya... sun yi matukar tausaya mata, ga hanan datake wani tunanin na daban, domin irin  ciwon patient din ya aaban shi abrar ke fama dashi
"ya Allah kasa abrar na cikin kwaciyar hankali" tafada cikin kaunar kawarta...

"bayan sati daya"
alhaji abdur-rauf ya diro kasar nigeria domin yayi hutun daya dauka tsayin wata biyu da iyalansa domin ba karamin kewarsu yayi ba. gaba daya gidan ya kacame da murna daga masu gidan har yan aiki, domin daddy shi kowa nasa ne, har dare baki na zuwa yimasa sannu da zuwa, hakan yasa be zauna sun tattauna da iyalansa ba,...

sai washe gari daya kasance sunday suna zaune dukkansu suna hira, abun birgewa  daddy ya zauna cikin iyalansa suna ta raha da nishadi, wanda su mummy sunyi missing wanna kyakyawan halin nasa, hajiya mummy baki yaki rufuwa daddy ya dawo lolz😜
"mummynsu jiya kin fara min magana akan abokina, (aaban, domin da haka yake kiranshi tun yarinta) tukunna ma yana ina?  wai har yanzu baya shiga jama'a? anya bake ya yayo ba kuwa?" yafada cikin zolaya yana kallon mum, dariya sukayi kana mummy tace "ai daddy wanna abokin naka Allah kadai yasan inda yasamo wanna halin nashi, sanna zan so yana nan sai mu hadu muyi maganar gaba daya alright bari na kira shi"  daddy ya fada.

bangaren aaban kuwa yana zaune idanunsa a lumshe yana tunanin decent one dinshi, jin motsi yasa shi ware idanunsa abrar ya gani zaune tana  kokarin   tashi, kara rufe idanunsa  yayi yana tunanin kai ta asibitin kwakwalwa domin aduba ta duk da besan ya kalar fuskarta yake har yanzu ba, amma yaji yana da niyyar taimaka mata.

sake ware idanunsa yayi adalilin ringing din da wayarsa keyi, karawa yayi akunne bayan ya daga yaji ance "abokina kazo falo muna jiran ka yanzu"
"ok dad" ya amsa ataikace

yana zuwa ya zauna akusa da daddy yayi shiru idanunsa alumse, murmushi mai sauti daddy yayi kana yace
"mummynsu ina jinki?"
"daddy daman akan maganar auren aaban ne, yasamu matar aure, shine nakeso anema masa auranta, yarinyar dai kawar hanan ce, duk da bamu gama sanin address din su ba, amma na na yaba da hankalinta kwarai... hanan na shirin tambayar wacce kawar tata, suka ji dariya hadi da kuka na tunkarosu yayinda cikin sauri take taka benen domin saukowa gaba daya suka juyo suna kallonta banda aaban da idanunsa ke alumshe, daddy da fuskarsa ya nuna mamaki domin besan da zamanta cikin gidan ba,,, "wacece wannan" daddy ya tambaya.
nan mummy ta shiga bashi labarin komai da komai... cikin tausayawa yace "Allah ya bata lafiya, sai ya kalli abaan yace abokina da an kaita asibiti ayi aikin ko za'a dace ko?"
"eh dad abinda nake shirin yi kenan"
"toh masha Allah" daddy ya fada.
daddy yace "wacce unguwa suke, indai an san unguwar, toh sanin gidan da sauki ai, mummy zata yi magana suka ga abrar da ta yi zaman yan bori akasa ta mike hadi da  daura hannunta kan gwiwowinta kamar dai ruku'u, sai tasake dago kanta wanda hakan yasa gashinta mai uban yawa yin baya take fuskarta ya nuna, nan ta shiga bin ko wannesu da kallo sai kuma tafara zallan kuka mai ban tausayi, sai lokacin aaban ya bude idanunsa yasauke su kan beautiful face dinta kara murza idanunsa yayi domin tabbatarwa,  cikin sauri ya mike kana ya tunkareta hadi da cewa
"decent one" yayinda hanan tace " bestie abrar kallon mamaki hanan da aaban suka yiwa juna, yayinda suka jefa su mummy cikin duhu...

share pls✔
comment✔
vote✔
edit❌

gaskiya comment dinku yana kadan, idan baku kara ba zan rage typing, domin baku bani karfin guiwan typing, tunda bazai yu in dinga typing domin faranta muku ace kuma kalillan ne zasu na comment ba

noor Eemaan✍

https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now