(tofah readers kuna ganin cewa mummy zata amince danta ya auri abrar idan taji kaddaran daya fada maka? ku dai cigaba da bin alkalamin noor dan jin yanda zata kaya a book din Mijin ammina ne sila).

bayan sun isa asibitin doctor hanan tayi masa bayanin yanda abrar keyi kwanan na nan yace sai sun zo da iyayensu zasu iya dubata, nan hanan ta nuna masa cewa iyayensa basa wanna kasar da kuma amincewarsu suka zo, ganin yanda anan tayi kallan tausayi yasa shi amincewa, amma ya gaya mata cewa za'a caje su kudi masu yawa ta nuna masa cewa basu da matsalan kudi...
bayan duk sun tanadi kayan aikinsu aka shigar da abrar wani daki yan gwaje gwajensu sukayi hadi da daukan hoton kwakwalwarta, bayan awa daya da rabi doctor ya fito yace anan ta bishi office dinsa...

Bayan ta shiga ya bata umarnin zama kallonta yayi na few seconds yace"you said the other girl is your sister right?"
Jinjina kai hanan tayi alamun "eh"
"ok sorry to ask are your parents still alives?" cikin mamaki tambayoyinsa hanan tace "of course yes!"
"You mean iyayenku na raye suka barta cikin wanna dangerous condition din. Doctor'n ya fada cikin mamaki
"Doctor please just go straight to the point" hanan ta fada cikin damuwa gyara medicated glass din idon shi yayi kana yafara magana cikin harshen turanci

"Asakamakon gwagwajen da muka yi mata mun tabattar da cewa tadauke da hawan jini, sannan kwakwalwarta yafara samun matsala domin idan aka cigaba ahaka ma'ana bata bawa kwakwalwarta hutu toh zata iya samun tabin hankali gashi ta dauko hanya, nayi matukar mamakin ganin wanna karamar yarinya cikin wannna mummunan halin domin ban taba jin karo da hakan ba duk da akwai wandanda ake haifa da irin wanna cuta amma bincike ya nuna damuwa, rashin hutu, firgice, hadi da rashin bacci sune suka haddasa nata wanda abubuwa da dama zai iya kawo shi kamar ko mutum ya ga abunda ya yi matukar firgita shi, kuma ace ya cigaba da gani ko wacce aka wa fyade ta karfi da yaji da dai sauran su ".

"innalillahi wa innah ila'ihi raju'un" hanan ta fada kamar zata saki kuka.
"amma bazata iya warkewa ba kenan doctor"?

"zata iya warkewa idan aka mata aiki amma, ba yin aiki bane solution, babban solution shine sai ta samu kwanciyar hali da bawa kanta cikakken hutu sannan aikin zai tafi yanda akeso domin bazai yu ayi aiki amma ta cigaba da dasa damuwa aranta tofah baza'a samu abunda akeso ba, dole sai tasamu mai debe mata kewa ta daina tunani dasa damuwa aranta, any way ga wasu magunguna zan rubuta miki zasu taimaka mata da yardan Allah" bayan ya gama ya mika mata takardan hadi da takardun aka dau hoton brain dinta, asanyaye hanan ta fito bayan ta siyi maganin ta biya kudin komai da komai dan kudin daya rage saura kadan domin asibitin suna da chajin kudi sosai...

tana juyowa ta ga abrar ta fito daga dakin da aka kaita, tun daga nesa hanan ke mata kallon tausayi "yanzu ace abrar mai kananun shekaru ke dauke da irin wanna cutan ita daya?" ta aiyana aranta...
bayan abrar ta karaso tace
"hey malama kallon fa" ta fada tana murguda dan mitsisin bakinta, dariya mai tafe da hawaye hanan tayi sai kuma ta riko hannunta suka fito daga asibitin

"wai hanan meyasa kika kawoni asibiti? nifa lafiya ta kalau"

hararan wasa hanan ta zabga tace"ban saniba yar rainin sense sai yanzu kika ga daman tambaya na"

dariya abrar ta yi tace" wallahi hanan har jikokin ki sun shiga uku da masifarki"
murmushi jinjina hanan tayi ko ba komai taji dadin yanda abrar tadan yi magana, hannunta takamo zuwa wajen wasu bayan dutsina gwanin sha'awa tamkar kujerar ta zama bayan sun zauna hanan tace

"jokes apart abrar mekikeso ki ja wa kanki? i know abunda ya faru dake yana da matukar ciwo amma ba yana nufin zaki cigaba da sa damuwa aranki ba, abrar damuwa bata gyara komai naji matukar tsoro lokacin da doctor ya fadi abunda yake damunki dan Allah ki kwantar da hankali wallahi bazan iya jure rasa kawa mai kyawun dabi'u kamar ki ba please ki taimaka ki rage damuwa akwai masu bukatar rayuwarki da yawa domin tana da muhimmanci agaresu, kalli result dinki cikin sauri abrar ta amshi takardun bayan ta gama karantawa sai ta kwashe da wani irin dariya ta dau wasu mintuna tana dariyan kana tayi shiru sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi tace " hanan ko daya banajin ciwon abunda doctor yace yana damuna kamar yadda nake kan jin ciwon rasa budurcina, abu mafi daraja da kowacce mace mai mutunci ke alfahari dashi matukar ta kaishi gidan mijinta, hanan ki gayamin ina abunda zan kai gidan mijin? shin wazai aure ni ahaka wazai auri ragowar mijin ammina abrar ta fada tana jijjiga hanan sannan tace ki gayamun hanan bana jin zan iya daina damuwa hanan ba laifina bane i can't just control it"

"toh zan gayawa ammi, zan gaya mata matukar zaki cigaba a haka" hanan ta tace cikin fada fada
cikin sauri abrar ta riko hannunta tace "hanan kada ki gaya mata komai dan Allah, ammina na cikin kwanciyar hankali tana matukar son mijinta, ta yarda da shi fiyeda ni shiyasa ta kasa amicewa da abunda na fada mata, ba bukatata ammi tasan abunda doctor yace yana damuna ba a'a bukatata ammi ta amincewa da cewa gaskiya na fada mata komai dadewa koda bana raye aduniyan, duk da haka ina matukar son ammina domin ita ce halitta mafi soyuwa agareni banason abunda zai daga mata hankali kimin alkawari bazaki gaya mata ba pleaseeeee" ta ja karshen maganar cikin kuka mai ban tausayi....

cikin kuka hanan tace " bazan gaya mata ba i promise you this, rungume hanan abrar tayi tace nagode miki sosai bestie hanan nagode da kaunar da kike nuna min since from the very first day we met, ina sonki fisabilillah ina kuma fatan Allah ya hada mun har a aljanna madaukakiyya"
"ameen abrar nima sonki"sun dau tsahon lokaci suna kuka kana suka koma hostel...

"welcome home aaban" mummy ta fada
"tnx mom" aaban ya amsa yana bata peck agoshi murmushi mummy tayi
tace "aaban my son na girka maka favorite dinka da hannuna, am sure you will love it"
murmushin da iyakarsa lebe yayi domin shi ba ma'abocin son abunci bane sosai, yafi ganewa su coffe, black tea, soft drink da snacks haka amma yaji dadi sosai musamman da mummy ce ta girka masa da kanta "thank you, mummy bari nayi wanka"
"ok son you re welcome"...

ya dau kusan mintuna arba'in kana ya fito sanye da ash 3quarter hadi da black jersey armless sosai kirarsa ta karfafa yasake fitowa sumar nan a kwance luf luf aaban ba dai haduwa ba, tun daga nesa mummy ke kallon shi cikin alfahari da godiya ga Allah daya bata shi, serving dinsa tayi da pounded yam hadi da egusi da ya sha su kifi banda, naman rago, gwanda, stock fish, ugu, da dai sauransu babu abunda ke tashi sai kamshi (ko ni dana leka miyar sai da na hadiyi yawu😜)
yana kai loma daya bakinsa yace "yummy you re always a good cook mom" murmushin jin dadi mummy tayi (kusan ba wanda baya so a yabe shi) da kyar dai ya cinye malmala daya saboda farinciki mummynsa kana ya dawo falo ya zauna, ayanda yake zaka yi tunanin ba shi da ko digon damuwa amma azuciya shi kadai yasan abunda ke damunshi, gyaran murya mummy tayi kana tace "son inaso muyi magana it's hightime ace yanzu ka ajiye iyali shin kana da wacce kakeso ne? idan babu nayi maka sha'awar kawar hanan abrar domin na yaba da hankalinta, jiyayi gabansa ya bada dam! adalilin sunan abrar daya ji....

kuyi hakuri dan Allah wallahi nayi typing mai yawa ya goge😰 manage this pls...

noor Eemaan✍

SHARE PLS✔
VOTE✔
COMMENT✔
EDIT❌

https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now