"Aabaan swerry meke damun ka this days gaba daya baka da kuzari hadi da walwala kuma ba haka na saba ganin jarumin dana ba" mummynsa ta fada tana shafa kwantacciyar sumarsa.

a hankali ya ware labbansa yace "nothing first love"

"don't tell me that son" mummyn ta fada cikin fushi.
sai kuma ta sausauta murya domin kaunar datake masa domin kaf cikin yayanta tafi ji dashi "yanzu akwai damuwar dazaka iya boye min?" ta fada cikin damuwa.

hannunta ya kamo kana yace" trust me first love babu komai kawai gajiyan aiki ne"

"ok fine i believe you my son" ta fada tana sakar masa murmushi.

shima ya kakaro murmushin ya sumbaci hannunta yace" i love you first love"

cikin farinciki mummy tace " love you too"

cikin tafiyar sa ta burgewa ya nufi site dinsa dake gidan domin baya jin zai iya zuwa hospital yau gaba baya jin dadin komai tun daga ranar daya rasata....

mummy na kokarin fita daga dakinta abrar na shigowa, tsayawa ammi tayi tana kallonta yayinda take sakar mata murmushi hadi da ware mata hannyenta alamun ta karaso gareta domin  ba karamin kewar yarta ta yi ba, cikin sauri ta rungume ammi hadi da fashewa kuka sosai har da shesheka.

"subha'nala abrar lafiya ko har yanzu jikin ne?" ammi ta tambayeta hadi da dago fuskarta sai alokacin ta lura da yanda fuskar tayi ja hadi da mugun kumburi ga kuma ramar datayi, zaro ido ammi tayi tasake cewa"innalillahi wa innah ilaihi raju'un abrar meke damunki gayawa amminki kinji" kara cukwuikuye rigar ammi tayi hadi da sake rungumarta tace

"A...m...mi mijinki ya keta mun haddi, ya mun fyade yau kwanana uku bazan inda kaina yake ba sai yau..... nan ta shiga bawa ammi labari komai data sani kafin dogon sumanta...

ammi jin maganar tayi tamkar saukar ruwan dalma akunnenta dan bubbuga kunnenta tayi domin tabattar da abunda taji tabass muryan abrar keta amsa kuwa akunnenta "mijinki ne ya min fyade ammi"...

kafadun abrar ammi ta rike da karfi                   "mekika ce abrar?"
Cikin kuka abrar ta maimaita mata komai kamar yadda tace sai ta dora dacewa "ammi mu gudu mu bar gidan nan, ammi mutafi domin zan iya mutuwa idan wani abu yasake samu na".

wani mugun tura ammi ta mata dahar ta fadi kasan tiles, cikin fushi ammi tace "ban taba tunanin cewa baki da hankali ba sai yau, anya abrar ba asibiti zan kaiki aduba min kwakwalwarki ba, yanzu kiyeyyar da kika wa alhaji har ta kai ki masa sharri, mutumin daya dauke ki tambar yarsa, mutumin daya kula da mu alokacin da muka zo garin dabamu san kowa ba, shi zaki yiwa kazafi" ammi ta karasa cikin daga murya hadi da matsanancin fushi.

Mikewa abrar tayi ta karaso gaban ammi hannunta ta rike hadi da cewa  "ammi wallahi da gaske nake, wallahi ammi na rantse da girman ubangiji daddy mijinki shine ya keta mun haddi ke duba ni ammi dan ki tabattar ko ki tambayeshi, da idona na ganshi a dakina ammi ki yarda da yarki ban da kowa aduniya sama dake ammi kitaimaka mubar gidan zuciyata zata yi bindiga" ta fada tana dora hannun ammi a kirjinta dake beating so fast.

kwace hannunta ammi tayi da karfi hadi kifa mata maruka kyakyawa har sau uku ji kake tas! tas!! tatas!!! "wallahi na kara jin kince alhaji ne yamiki fyade sai na cire bakin, yaushe kika fara karya? wato ta nan kika bullo domin mu bar gidan ko? to karyanki ya sha karya, bazaki kasheni da raina ba, kuma kafin  in kirga biyar ki bar dakin nan"

wani sabon kukan abrar tasake rushewa dashi har dashewa muryanta yayi ga makogaron ta dake mata zafi ga cikinta sai kugin yunwa yake amma duk hakan be dame ta ba, burinta ayanzu ammi da tayarda da ita
"ammi ki yarda dani, ba karya na masa ba banda kowa sama dake ammi ke kadai ce zaki iya kwatar min hakkina idan baki yarda dani ba ammi waye zae yard..."ko karasa maganar bata yiba amma ta janyota waje hadi danna key akofar. Dukan kofar abrar keyi da iya karfinta tana cewa"ammi ki yarda dani, wallahi shine"  haka ta cigaba da fada tana kuka, takai mintuna arba'in azaune abakin kofar kana ta mike tana hada hanya ta koma dakinta...

bayan barinta wajen ammi ta fashe da kuka data rasa ko na menene amma ko alama bata yarda da abunda abrar tace ba, duk da tasan abrar bata karya, amma ta amince a wanna lokaci abrar tayi karya domin bata  taba jin ko ganin hakan ba.

"1 WEEK LATER"

"alhaji shettima ne tsaye jikin kofar dakin abrar da misalin biyun dare bayan ya zubawa ammi maganin baccin nan cikin juice batare da ta sani ba, tura kofar ya dinga yi da iya karfinsa yaki buduwa alamun ta rufe kenan gashi ba shida  extra key na dakin ta, haka ya juya yana mai jin ba dadi, domin yana  son sake kasancewa da ita,  baya jin zai hakura da ita ko ta wani hali kuwa...

abrar dake zaune kan sallaya ta rushe da kuka domin tana jin duk abunda yake tama rasa abunyi, domin ko kadan  batason sake ganin sa domin shidin abun tsorone,  ga ammi bata kulata ko ta gaisheta bata amsa mata, komai ya cakude mata har tunanin guduwa take dawanna shawaran ta kwanta tana lazumi...

kamar kullum tana rufe adakinta ta rame sosai domin bata cin abincin daga ruwa sai lemo shima sai taji cikinta na murdawa alamun yunwa sannan take sha, kallon dakin tayi gaba daya ya dawo tamkar na mahaukaci, domin har yanzu abubuwan data farfarsa da wanda ta zubar kasa suna nan yanda suke haka take takawa yayinda kwalaben ke shigar kafarta amma sam bata damuwa, gashi tayi kokarin guduwa security suka hanata duk da nuna musu  tayi cewa abu zata siyo suka ki amincewa sannan suka bata tabbacin alhaji ya ce kada abarta ta fita ko da kofar wajen gate  ne, tuno hakan data yi yasa wasu hawaye masu zafin gaske suka zubo mata, " ya Allah gani ga gareka, ya Allah ka shiga tsakanin na gari da mugu"
mikewa tayi ta dauki tsintsiya ta shiga share dakin, bayan komai  ya dawo saiti adakin ta nufi toilet ta wanke sai idanunta suka sauka kan doguwar riga mai kalan sea green tsurawa rigar ido tayi, duk iya tunaninta batasan inda rigar ta fito ba, kuma ita bata da koda mai yanayin rigar ne balle tace nata ne ba, wata zuciyar tace "kika sani ko alhaji shettima ne yasa miki?" Yayinda dayar zuciyar tace " hakan bazai taba yuwa ba, mutumin daya keta min haddi, har zai iya suturta jikinki, bayan shine mutum na farko daya fara ganin sirrin jikinki bayan ammi"

gyada kanta tayi alamun gamsuwa da abunda dayar zuciyar ta raya mata, ga rigar na wani irin kamshi mai sa nutsuwa, wankewa tayi kana tayi wanka ta fito bubu gown mara nauyi tasa, sai ta haye gado ta janyo teddy dinta ta rungume da hannu daya, lumshe idanunta tayi tana tunanin makomar rayuwarta tadau tsahon lokaci tana tunanin kana ta ware idanunta ahankali take ya sauka akan diamond ring din hannunta, zaro manyan idanunta tayi cikin mamaki....

PLS SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌

ataya ni share dan Allah🙏

Noor Eemaan✍

https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Onde histórias criam vida. Descubra agora