"CYPRUS"
"abrar yau shirun ki yayi yawa what's the matter?"
" hanan ina kewar ammina sosai" murmushi hanan tayi tana jinjina kaunar dake tsakaninsu domin abrar batada magana sai na ammi.
"but why not ke kirata"
"banda waya, tace kuma bazan rike waya ba har sai na gama school"
jinjina kai hanan tayi kana tace
" ga wayata ki kirata idan kina da numbern off head"
cikin sauri abrar ta amsa tana murmushi itama hanan murmushi tayi ganin tasa kawarta farinciki domin sosai take son abrar.
"ammina" tafada bayan taji alamun an daga
"abrar?"
"na'am ammina ina wuni fatan kina lafiya"
" lafiya lou, ya karatu hope dai baki wasa da karatu?"
"eh bana wasa ina kewarki sosai ammina tafada cikin muryan kuka"
"murmushi mai sauti ammi tayi cikin sahihiyar kaunar yarta tace" ina kewarki nima sosai diyata, daina kuka kinji?"
jinjina tayi tayi tamkar ammin na gabanta        "amma abrar wayar waye wanna"
kallo hanan tayi kana tace "wayar kawata ce  dakinmu daya" kafin ammi ta amsa hanan tace "kaji mun yarinya wai bazaki bani wayar mu gaisa da ammi ba ko taki ce kedai" tafada tana warce wayar, girgiza kai kawai abrar tayi yayinda ammi dake jinsu ta ke murmushi, nan dai suka gaisa da ammi, linda dake gefe tana murmushi domin sosai take jin dadi idan taji su abrar na hausa "hey why are starring at us like that?" abrar ta tambayi linda tana dage girarta
"i love you guys language so much, will you teach me i mean hausi(hausa)" dariya suka sanya gaba dayan su musamman hanan da kiris take jira dama...

haka dai rayuwa ta cigaba da juya musu daga ranaku zuwa satittika, daga satittika zuwa watannin daga watannin zuwa shekara,  ayanzu haka su abrar suna level200 exams kawai ya rage sun kamalla wanda agida nigeria zasu yi hutun su linda kuma zata koma america domin yin nata hutun...

yan mata uku ne suka jero cikin shiga mai birgewa, ta hannnun dama ita ce tafi kowaccensu haske sanye take da black half gown mai spaghetti hand yayinda gashinta mai kalan sliver ke daure da band, ta hannun hagu itama farace sosai amma ta dama ta fita fari, sanye take da jumpsuit na jeans sai farar riga ta ciki, kafarta kuwa sanye yake da black cover shoe ta yane kanta da bakin veil ta sha makeup  tayi kyau ta tsakiya kuwa mai brown skin tafi ko waccensu kyau amma ita ba fara bace, itama irin shigar ta gefenta tayi wato jumpsuit, sai yanzu dana kallesu sosai naga ashe abrar, hanan, da linda ce. sun kara girma musamman abrar da take kokarin shiga 16years yanzu komai na budurwa ya gama bayyana mata cikin shekaru biyun nan tayi girma mai ban mamaki domin kirarta mai kyau ce wato cocacola shape  kallonta zaka san cewa  akwai kuruciya atare da ita domin hanan da linda sun girme mata, brown skin dinta ya kara wani kyau da sheki ga teddy a hannu wacce mahaifiyar linda ce ta siya mata awani zuwa data yi duba linda ta fita dasu shopping tace kowa ya zabi abunda yake so amma abrar abunda tafara dauka  shine teddy, daga nan sai kayan zaki dangin su chocolate da icecream.
"nikam abrar kina  badamu, kalli fa kin wani rike teddy sai kace da, kina ajiyewa a hostel mana amma ki kalli mu sha wanna wankan zaki kwabsa mana"
"hanan wallahi kin sa wa teddy na ido ina ruwana da mutane abrar ta fada tana wani murguda baki"
girgiza kai linda tayi tana murmushi duk da batasan mesuke cewa ba amma jikinta ya bata dramman dasuka saba shi sukeyi.
hadaddiyar wurin siyarda pizza da burger suka nufa domin ya aaban ya turowa hanan kudi jiya shine tace lallai sai sun fita outting da friends dinta, hadadd'un kujerun  wurin suka zauna waitress tazo ta gaishesu hadi da mika musu menu zaba musu hanan tayi, babu jimawa  aka kawo musu hanan da linda asake suke cin abinsu yayinda abrar ta kasa ci sai lemo data sha duk da babu mai kallonta domin kowa harkan gabansa yake amma ta kasa sakewa...
"ya naga bakya ci ne?"
"zan ci" inji abrar
"nikam wallahi be isheni ba bari nayi musu magana su karamin wani"
"a'a hanan zo kici nawa ni nama koshi"
"Allah baki isa ba, ki cinye duka idan bason ganin fushina kika ba" hanan tafada tana shan kunu.
"toh naji masifatu" inji abrar tana dariya
itama hanan dariya tayi, wayarta ta mikawa abrar kana ta nufi wurin masu serving mutane ...

abrar ta dauki yanka daya na pizza zata sa abaki kenan wayar hanan ya fara ringing, ras! ras!! gabanta yafadi kurawa hoton daya bayyana a screen  din  ido tayi bata ko kiftawa, "shin mutum ne wanna ko aljani?" ta fada abayyane...
har kiran ya katse bata sani ba domin gaba daya kallon hoton yadauke mata hankali wani kiran daya sake shigowa ne yasa ta dawowa tunaninta "ya Aaban" shine sunan data gani a rubuce ana haka sai da hanan ta taho dauke da plate din pizza, " gashi ana kiranki" abrar ta fada "shine baki daga ba?" abrar bata amsa ba ta mika mata wayar...
"hello ya Aaban"
" assalama alaykum" yace  mata
"rufe baki tayi da hannayenta tana zaro ido hadi da cewa " sorry ya Aaban   wa'alaikumu salaam"
"sorry for yourself, next time i won't repeat my self"
"in sha Allah yaya zan kiyaye"
"good of you, so exams dinku saura nawa?"
" uhmmm saura uku yaya i think nan da two weeks time zamu dawo nigeria, yaya i know kana missing dina shiyasa kake ta tambayana ko?"
daga bangaren Aaban tsadaddan murmushin sa ya saki kana ya katse wayar yana matukar son kanwarsa hanan, domin da ita ne kadai yake zama yayi hira baya ga iyayensa...
bayan sun gama ci suka nufi wuraren shakatawa masu yawa kana suna koma hostel agajiye....

*SOME DAYS LATER*
gaba daya sunyi shirin komawa gida, domin gobe da misalin karfe 8:00am jirginsu ze dira a nigeria, domin linda ta tafi tun jiya abunta, zaune suke abrar ta dafa musu noodles suna ci, sae dai abrar ba ci take ba tsakura take, cikin damuwa hanan " tace abrar lafiya yau gaba daya kinyi looking dull"
hannun hanan ta kamo hawaye masu zafi suka zubo mata " hanan jinake kamar kada na koma gida, jiya nayi wani mafarki dana kasa fassara shi, taba kirjina kiji yanda take bugawa" ta fada tana kamo hannun hanan zuwa kirjinta.
cikin tausayawa hanan ta sake damko hannunta tana cewa" kiyi shiru abrar duk abunda kika ga ya faru da bawa toh yana cikin kaddararsa wallau mai kyau ko akasin haka, kuma in sha Allah alkhairi zaki gani  ki cigaba da addu'a kinji"
"in sha Allah" tafada tana goge hawayenta...

"NIGERIA"
ahankali jirginsu ya sauka a airport din  Nnamdi azikwe, nan mutane suka fara fitowa, can sai ga hanan na saukowa, ga abrar agefenta cikin shigar cairo abaya peach color babu makeup a fuskarta amma sosai tayi bala'in haduwa, nan suka yi sallama da hanan tana cewa sai tazo gidan su ta gaida ammi, murmushi kadai abrar tayi tana gyada kanta kallon mutane ta fara yi ko zata ga ammi can kuwa ta hango ta tsaye jikin mota ita da alhaji shettima, tunkarosu tafara yi tana murmushi ammi na bayar mata da martani domin duk girman da abrar ta kara da kyau amma ta gane yarta, alhaji shettima kuwa sai yanzu ya shaidata kura mata ido yayi tun daga sama zuwa kasa baya ko kiftawa take wani abu ya darzu aransa.....


SHARE ✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌

NoorEemaan✍

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now