Kwance tashi ba wuya a wurin Allah abrar tana da shekaru goma 13 a duniya yanzu tun bata gane cewa yan'uwa babban ta basu sonta har ta gane domin abayyane suka nuna mata tsana banda zulaihat wacce aure ya rabasu a yanzu, abin burgewa kuwa abrar ta sauke qur'ani a wanna kananun shekarun na ta, haka zalika tana ss2 abangaren boko. A yau sajeed ze dawo daga china domin yanzu harka ta kara buda masa, abrar sai zumudi take abbi ze dawo, duk inda tayi rahilat na bin ta da kallo cikin kaunarta domin komai na ta ta dauko tamkar photocopy har ma ta zartata a kyau da kyawun fata abu daya ta dauko na mahaifinta gashinsu mai uban yawa na buzaye.

bayan wata biyu sajeed ya fara rashin lfy wanda be dau lokaci ba, Allah ya karbi ransa, ranar sun shiga tashin hankali domin sun rasa babban jigo mai kula da dukkanin al'amuransu.

Bayan wata biyar da kasuwar sajeed wanda rahilat ta gama takaban ta, sauran kwana uku araba musu gado, ummi ta kori rahilat cikin dare, babu irin rokon da bata yi ba, har ma da abrar rokon ummi take, amma haka ta kore su babu tausayi, suna kuka haka suka dau yan kayansu tare da kudadden da sajeed ke bar mata bata kashewa wanda ummi batasan da su ba. Gaba daya rahilat ta rasa ina suka nufa ga dare yayi, a tasha suka kwana washegari da asuba tunanin komawa cameroon ya zo mata, da zuwansu can suka ga gidan raheenat arufe wani gefen ma ya rushe alamun anjima ba mutum a ciki, gashi ba wasu gidaje kusa da gida balle ta tambaya ko suna ina, haka suka bar kauyen tana kuka domin bata sani ba ko yayarta da mijinta na raye ko a mace???

da fitowarsu cikin gari ta rasa ina suka nufa domin dare yayi, gaba daya tsoron komawa nijer take domin bata san sharrin da ummi ke dashi akan su ba, tunanin mai zurfi ta shiga can ta yanke shawaran barin kasar zuwa NIGERIA domin sanda sajeed ke raya yana yawan bata labarin kasar tana kuma sha'awar zuwa din, take taji mutuwar mijinta ya dawo mata sabo hawaye masu zafi suka saukar mata kwanansu uku a hanya suka iso domin da rabi da rabi ta dinga hawa abun hawa saboda kudin ya kai mata domin bataso su shiga halin matsi idan sun je kasar da basu san kowa ba. Tarihinsu a taikace kenan

*ABUJA*
A unguwar maraba dake abuja suka sauka domin nan sai sun fi samun saukin rayuwa domin a unguwar akwai masu karamin karfi ba laifi, da taimakon wata mata dasuka hadu a tashar abuja tasamu hayar daki daya a dubu arba'in da biyar.

washegari suka je kasuwa ta siyi leda dakin, labule, babban roban zuba ruwa, kwanunka, tukunya, cokula da dan abinda ba'a rasa ba a daki. Ragowar kudin ahannunta idan aka canza su zuwa kudin nigeria ze kai dubu dari, tunanin wani sana'a ya kamata su fara take domin kada kudin su kare a siyan abubuwa sun shiga halin kunci maganar abrar ya katse mata tunani

"Ammi ki siyamin nama in ci tun da abbi ya barmu na daina ci" abrar ta fada da hausarta wacce bata kama bakinta ba sosai kasancewar ba'a fi yi mata hausa ba, daga yaren cameroon sai buzanci, amma duk da haka hausar tayi dadi a muryanta mai gardi.

hawaye ne suka ciko idanun ammi domin kalaman diyarta ya sa ta tuno gwarzon mijinta, tabass shi ya saba mata da cin nama domin shima ma'abocin son nama ne sosai.

"abrar idan muka cigaba da siye-siye a haka kina tunanin kudin ze kai wani lokaci ba tare da ya kare ba?"
turo baki tayi batare da tace komai ba, murmushi ammi(rahilat) tayi cikin kaunar yar tata tace "wato ni kike turo wa karamin bakin ki nan zaki ga wanda ze siyo miki naman"
cikin sauri ta fada jikin ammi tace; kiyi hakuri ammina murmushi ammi tayi cikin canjin daya rage na siyeyyan ta bata dari biyar . "Maza je ki siyo awaje gidan nan kidawo domin nasan shi kika gani tsahon kwadayinki ya tashi" dariya abrar tayi ta fice cikin sauri domin har wani hadiyan yawu take tun kafin ma ta siyo😄

Washegari ammi ta siyo musu kayan abinci daze dade musu, kana ta yanke shawaran yin sana'ar kosai da kudin daya rage mata cikin ikon Allah ta fara kuma ba laifi tana ciniki sosai .

*BAYAN WATA UKU*
zuwa yanzu babu wanda be san ammi mai kosai da kunu ba domin har kunu take hadawa yanzu, har runfa gareta kuma tana samun riba har tana tunanin da an fara biyan kudin waec da neco zata biya wa abrar domin so take tayi karatu mai zurfi domin kula da rayuwarta koda bata raye...

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now