PAGE 77-78

19 4 1
                                    

                  ♻️♻️HAJNA ♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNA

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
PAGE 77-78
**********************

Da rana Aisha ta dafa abinci rana kamar yadda momy ta bada umurni, Hajna kuwa bata fito ba, dan kunya duk ta gama rufe ta, gani take bazata sake bari ta haɗa ido da Farween ko wani daga ahalinshi ba, a ɗayan ɓangaren kuma haushin Farween ta ke ji, saboda Halia. Sai misalin ƙarfe 4:00 ta fito, ta yi sa'a Farween yana compound ɗin gidan, dan haka ta yi saurin shigewa kitchen.

    Tunanin abunda za ta dafa ta ke yi, kafin daga baya ta yanke hukuncin dafa macaroni da hanta, dan haka ta buɗe fridge ta ɗauko kayan miya da ɗanyar hanta, wanke kayan miyan tayi sannan ta wanke hanta, kayan miyan ta jajjaga a turmi, sannan ta zuba a cikin tukunya, bayan ta tanadi duk abunda ta ke buƙatar a gabanta, sannan ta fara dafa abincin, kasancewar macaroni ne yasa bata ɗauki lokaci ba ta gama, tun kafin ta gama ƙamshin abincin ya gauraye ko ina na gidan, Aisha da fitowar ta kenan, duk ta ƙagara Hajna ta gama abincin ta ci .

    Pepper soup ɗin naman rago tayi, wanda ƙasusuwa su ka fi yawa, shi ma ɗin tun a ido zaka tabbatar ya yi daɗi, komai na kitchen ɗin ta gyara, sannan ta fito da abinci ta jera a dinning, lokacin ƙarfe 5:30, ɗaki ta koma ta cire kayan jikinta, dan duk zafin kitchen ya ishe ta, wanka tayi sannan ta shirya cikin wata doguwar rigar atampha, tayi matuƙar yin kyau.

A ɓangaren Farween kuwa video call yake yi da Halia, sai labari ta ke ba shi yana dariya, da alama akwai shaƙuwa me ƙarfi tsakanin shi da Halia, “yauwa baby ki shirya zan zo gobe mu taho tare da ke ", zare ido tayi “ina za mu?", “sayar da ke zan yi gurin buzaye, su je da ke niger kowa ya huta", turo baki ta yi, tace “ai da kai da kanka zaka je ka karɓo ni ", “haka kike gani, idan fa na canza sabuwar baby", Halia tace “ko wacece ita bazata kai ni ji da kai ba, ni dai ƙyale ni ma" ta faɗa tana juyar da fuska, dariya ya fara yi, dan yadda ta yi ya ba shi dariya, “au ni na ɗauka ai baza ki yi fushi ba " ya faɗa, juyowa tayi tace “to nayi a rarrashe ni", murmushi yayi yace “am sorry baby ", “ni bazan haƙura ba sai idan bazaka canza baby ba" murmushi yayi yace “I promise u bazan canza baby ba, kece baby har abada ", “to shikenan, idan ka yi baby ba zamu sake magana ba", gaɗa kai yayi alamar ya yadda, “to ina zaka kai ni", “gurin Aunty Farwa zamu zo fa ", “Ohhhh god, wai da gaske" ta tambaya cikin farin ciki, Farween yace “eh ba wasa ba", ɓata rai tayi dan ta san Farween zai iya cewa su fita amma ganin tana zumuɗi sai ya fasa, kallonta yayi yace “ki fara shiri, insha Allah zaki zo ", yanzu da yace insha Allah, sai ta ɗan yadda, dan haka sai ta saki rai su ka cigaba da labari da shi, sai da aka kira magrib sannan ya mata sallama.

   Arwala yayi ya nufi masallaci gurin sallah, tunda ya fito hankalinshi na kan Hajna, ko kaɗan baya so ya ga ranta ya ɓaci, cikin gida ya shigo inda ya samu Aunty Farwa zaune da alama itama bata daɗe da dawowa ba, duk da dai ta canza kayan jikinta, “har kin dawo kenan ", aunty Farwa tace “tun 6 na dawo, ai na wuce ka kana ta waya", rassss! Gaban Hajna ya faɗi, dan jikinta ya bata Halia ce, amma sai ta dake, “Aisha ɗauko mishi abinci "Aunty Farwa ta faɗa, “a'a ni Hajna zata kawo min" ya faɗa, Aisha da ke ƙoƙari tashi tace “ka hutar da ni ", Hajna bata ce komai, tashi tayi ta kawo mishi, kamar ko yaushe, yau ma santi ya ke yi, tun Hajna na haɗe rai har ta fara dariya, wani bin har da riƙe ciki, shi kuwa sakin baki yayi yana kallon ikon Allah, gurin a gurin shi be ga abun dariya ba, amma kalli yadda Hajna ke yi, har da riƙe ciki, jin ana kallon ta yasa tayi saurin dakatawa, nan take suka haɗa ido da shi, da ƙyar ta samu ta ja dogon numfashi, sannan tace “aunty Farwa ni zan shiga daga ciki, saboda zan yi karatu, ina so da anyi isha'i na kwanta ", Aunty Farwa tace “to shikenan ki kula kinji", tashi tayi ta wuce, har tana haɗe ƙafa.

Girgiza kai kawai Farween yayi yace “Hajnata", ni kuwa nace Hajno ba Hajna ba. Yana gama cin abinci ya wuce masallaci dan an kira sallah, sallah yayi, sannan ya dawo ya kwanta, dan gobe so ya ke ya wuce tun bayan asuba.

Kiran fari kawai aka yi Farween ya tashi yayi wanka, sannan ya shirya cikin riga da wando, sannan ya fita, masallaci ya shiga ya bi jam'in sallah sannan ya wuce airport, dan yana zuwa zai juyo, so ya ke 9:00 ta mishi cikin Lagos.

Aisha ko barci ta ta sha bata tashi ba sai ƙarfe  8:30, dan yau da ƙyar ta samu ta yi asuba, cake  aunty Farwa ta musu baking suka haɗa da tea, Hajna ta fara gamawa dan ita ba wani cin abinci take yi ba, Aunty Farwa tace “je ki tada min Farween sarkin kwaɗayi yau anyi favorite snack ɗin shi "Aisha tayi ƙasa da murya tace “Mommy baya nan fa", “to ina ya je " Aunty Farwa ta tambaya, Aisha tace “ya je ɗauko Aunty Halia ne", “da gaske? "Aunty Farwa ta tambaya, Aisha tace “eh, saboda Aunty Hajna ne, ita da Uncle Farween ne su ke son juna, amma tana fushi da shi saboda Aunty Halia", “shi ne dan shirme ya je ya ɗauko ta, lallai Farween ", Aisha tace “ni ce fa nace ya zo da ita, saboda zata fi fahimta", shiru aunty Farwa tayi, ita bata ga abun wahalar da kai nan ba, miye na zuwa ɗauko ta, ko da baki ai za'a iya ma mutum baya ni kuma ya fahimta.

Suna zaune Farween ya shigo riƙe da hannu wata yarinya da a ƙalla zata girmi Hajna da shekara ɗaya ko kuma su zo tsara da juna, kanta a ƙasa dan ita bata cika ɗaga kai ba idan tana tafiya, da gudu Aisha ta zo ta rungume ta, “oyoyo my best aunty I miss u bad "Aisha ta faɗa, Aunty Farwa ta ƙaraso tace “har ka taho da Halia ɗin ko" gaɗa kai yayi dan yasan Aisha har ta faɗa mata, Hajna da ke shirin barin gurin ba tare da ta kalli ko ɗayan su ba ya ke kallo, zata wuce yace “Halia ga auntyn ki, je ki mata magana ", da sauri ta tari gaban Hajna, murmushi ta mata tace “ki kalle ni ko sau ɗaya ne", Hajna da bata yi niyyar kallonta ba ta ɗago  ta kalle, kamar ta da Aunty Farwa kamar an tsaga kara, bambanci kawai ita Halia fara ce, Aunty Farwa kuma ba fara ba ce sosai, Aunty Farwa tace “yanzu sai ka mata bayani da kanka ", Halia tace “ni zan yi", Auny Farwa tace “to ƴar a yi, jikan na saba, maza ki faɗa mata ", Hajna kuwa kallon su ta ke yi da mamaki.

“ yaya Farween ya bani labarin komai da komai a hanya, to ni ba budurwar shi bace, hasali ma an kusa aure na, ni ƙanwar shi ce, kawai dai shi kamar aboki ne a gurina", Hajna da idonta ya ciko da ƙwalla da sauri ta wuce ɗaki tana kuka, me tayi ne haka, bata ma tsaya ta tambayi Farween wacece Halia ba, amma ta hau fushi.

A ɓangaren Farween yace “Aisha ki bi ta dan Allah ki rarrashe ta " bata yi musu ba ta wuce, Aunty Farwa tace “ Halia ki ji daɗinki, da badan Hajna ba ke da gidan nan sai sallah, ko kuma in kin yi aure mijinki ya dinga bari kina zuwa", Halia tace “wallahi ", Farween yace “to minene amfanin yawo ke da aka sa ma ranar aure", Aunty Farwa tace “ina ruwanka to ba mijinta ya yadda ba ", Farween yace “oho dai, ki fara shirin tafiya gobe kinji ni ai", Aunty Farwa tace “ka yi kaɗan kuma, dan yadda ka biya buƙatarka haka mu ma yanzu za ka saka mana na mujiya har mu gama ", dariya Halia tace “ai nasan inda zan ɓullo, in be yi a hankali ba ina nan har bayan biki", Farween yace “ki mutu a nan in kin iya, mara ji kawai ".

Anan zan dasa aya............ ✍️

Ku min afuwa, daga yau zan je hutu har bayan sallah saboda aiki ya min yawa, gashi muna shirye-shiryen biki, bana so ina raba hankali, ina buƙatar natsuwa gurin rubutu, dan haka sallah da sati insha Allah zaku jini, taku har abada Queen Nasmerh.

Karku manta kuyi following Wattpad account ɗina, sannan ku bibiye littafaina tun daga kan Ayisherh har zuwa SAQAR SO.

Haɗin guiwar Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️♻️♻️♻️💃🏻💃🏻

♻️♻️♻️HAJNA ♻️♻️♻️Where stories live. Discover now