"Ba wani sirri doctor Ina nema yardar Allah da nasarar sa akan aikin da zamuyi shine kawai"

To Allah yasa mu dace nima daga yanzu zan rinjayi in Sha Allah ba ma Sai zamuyi aiki ba,no zan rinjayi akan komai ma,nagode bari na kyale ku ku gama,Sai min ha'du a wajen aiki.

(Tunatar wa anan yana da kyau duk abinda mutum zai yi ko zai gabatar yanemi yardar ubangiji kafin yayi Sai Allah yasa masa albarka acikin abin,idan kuma ba alkhairi bane Sai Allah ya musanya masa da abinda yake alkhairi.Allah yasa mudace)
*********

Da misali wajen karfe 6 na yamma ne Aleena suna girki da Amira,gida duk ya dauki kamshi Kai kace wani hadaddan gidan cin abinci ne, Amatullah ta shigo kitchen din dauke da sallama a bakin ta har da Dan murmushin ta wani sa hani kasan yake kawai take yi,abin ya daurewa su Aleena Kai,yau ya Amatu ce da yi musu sallama haka har da murmushi don ta saba da idan har Aleena tana wajen to baka taba ganin murmushin ta balle tayi magana.idan ko za tayi magana to Sai dai habaici ko Kuma ta ciwa Aleena mutunci.
Amira ta Sha gwada kare Aleena Amman Sai Aleena ta hana ta ta Kuma hana ta fa'dawa su mini balle kuma doctor,to dole yau abin ya basu mamaki da ganin sabon abu wajen Amatullah.

Kafin su gama warwarewa daga wannan abin al'ajabin kuwa Sai ji sukayi tace yau su Aleena me she data Mana ne a gidan duk kun cika mu da kamshi haka😳😅

Cikin muryar mamaki Aleena ta ce ba fa komai bane ya Amatu,biski ne kawai da miyar taushe,Sai kuma kunun gya'da.
"A kice yau abincin gargajiya zamu ci,to ni me zan taya ku da shi?"
Kafin Aleena tayi magana Amira tace "ai kuwa kin zo a makare don mu har min gama komai ya Amatu kawai a cooler zamu zu ba"
ok to shi ke nan,ba to na je na taya mom hira tunda kin gama.har ta Kai kofa Sai ta juyo tace yauwa Aleena idan kin gama Ina son magana da ke pls,to ya Amatu in na gama zan miki magana.
.tana fita Amira tace "wallahi ban yarda da wannan saukin kan na lokaci daya ba dum yadda akayi akwai abinda take so ta kullah da ke sis Kar ki yarda da ita"Aleena day murmushi tayi kawai suka cigaba
d

a aiki.

Sunan kammalawa Aleena take yayiwa mom sallama za ta tafi,Sai mom tace kirata,tana zuwa ta durkusa kasa tace "mom gani"
Mom ta rike kunnen ta tace "
Ina jin Sai na fara Jan kunnen ki sannan zaki Ron ka jin magana ta,saunawa nace I rinka diban abinci kina tafiya da shi amman ba kya hi ko Sai na gayawa son yayi miki bulala tukunnah"

Aleena tasa dariya mom mu cibfa a kitchen nibda sis,Kuma naga na koshi shi yasa ma ban diba ba,ta fa'da a shagwabe tai wani narai narai da ido.

To na ji yanzu ki koma ki dibarwa kawata nima tunda abincin marmari akayi bana koyaushe bane.to mom an gode Allah ya saka da alkhairi,sannan ta tashi tayi hanyar kitchen tana mai jin kaunar matar nan acikin zuciyar ta.
Ita ma mom haka ta bita da kallon so, yarinyar na burge ta komai akayi mata Sai tayi godiya ko da abin Bai Kai na a gode din ba,tana Kuma Kara godewa Allah ya Aleena zata zama mata ga son din ta Ashfaq.

Ta fito daga cikin falon dauke da cooler a hannun ta guda biyu,tana Sauri ta koma gida don ta goge kayan ta da zata sa gobe bikin binta kawar su,Sai ganin Amatullah a gaban ta."tafiya za kiyi ne Aleena?ke da na ce Ina son zamuyi magana".
"Lah wallahi na manta Ina ta Sauri zan je na goge kayan mu ne kiyi hakuri ya Amatu"
Amatullah tace bakomai,Sai kuma shiru ta ratsa a tsakanin su na wajen minti daya,ita Aleena ta kagu ta tafi gashi ta tsayar da ita ta Kuma kasa ce mata komai mtsss tana wannan tunanin ne taji Amatullah tana cewa

"Dama bakomai ne ya sa nake son magana da ke ba sai don na nemi wata alfarma a wajenki Kuma ba Wanda zai iya yimin alfarma nan Sai ke"
ta Dan yi shiru sannan ta cigaba
" Don Allah don Annabi,idan kina so iyayen ki su gama da duniya lahira ki taimakamin ki barmin ya Ashfaq ya aure ni,ki hakura da shi, wallahi Ina mutukar son sa ba ka'dan ba dum na ji anyi zancen bikin ku Sai in ji zuciya kamar zata fashe kallenu ki gani haka kika sanni? Duk nabi na lalace saboda shi.nasan ke yarinya ce mai hankali da tunani mai Kuma hakuri,ki taimakamin ki yafemin duk abubuwan da na yi Miki kice kin hakura da ya Ashfaq"
Ta tsugunna wa Aleena gani gwiwowina a kasa Ina rokon ki Aleena ki tausayamin Sai Kuka ta rinka yin shi mai Sauti..

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now