PAGE 1

411 12 4
                                    




*DA BANSAN ASALINTA BA!!*


Na
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
*DA*
*HAUWA SHEHU ALIYU*
( _JEEDDAH ALIYU_)

*HOT LOVE STORY 2021*



*Page 1*

*GODIYA*
_Dukan yabo da godiya sun tabbata ga ubangijin tahallikai. Tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad ( s a w) da alayansa da Sahabansa baki d'aya. Yanda muka fara littafin nan lafiya ubangiji Allah yasa mu gamasa lafiya alfarman Annabinmu amin ya Rabbi_

*GARGA'DI*
_Wannan littafin k'irk'iraren labari ne ba mu yarda wata ko wani su juya mana labari ba, ta ko wace hanya idan ba tare da izininmu ba yin haka kuskure ne sosai dan haka a kiyayye_

*SADAUKARWA*

_Wannan littafin sadaukarwa ne ga d'anmu *MUKHTAR UBANDOMA* da kai da y'an uwanka ba ki d'aya ubangiji Allah raya mana ku amin ya Rabbi samawati wal ardi_

***"""""****

*ABUJA NIGERIA*

Mota ce k'irar Mercedes Benz 2020 ta danno kai cikin harabar wajen shakatawar.
Tamkar ma mallakin motar zai tashi sama.
Ya isa cikin wajen daidai table d'in wasu mutane ya taka birki.
suna zaune a gaban wani table samansa an d'aura masu kwallaben giya dukkan su, su uku su na sanye da kakin soja{Army uniform} ko wane ya aje bindigar sa a gefen shi.
Cikin fushi had'e da zafin zuciya ya banko k'ofar mota, ta bud'e lokaci d'aya ya fito da gangar jikinsa kamar namijin zaki, basu an kara ba yasa k'afa ya tashi da table d'in giyar dukansu saida suka zube k'asa.
'Daya daga cikinsu ne ya d'ago kai wanda ba yaro bane ba, kallo d'aya za ka yi masa ka gane ya malaki hankalin sa sai dai kashhh....! wannan wajen girma yayi gardama, cikin murya ta wanda yake cikin maye ya lumshe ido ya d'aga hannun Shi ya kaishi daidai kumcinsa ya ce "Morning sir! ashe oga kaine da kanka?"

Cikin k'arin bak'in ciki ya d'ago shi da hannu d'aya tamkar ya d'auki yaron goye Cikin fushi kamar zai wanka masa mari ya fara magana
"CPL Riskuwa what's wrong with you are you out of your mind?
An kaiku duty shine zaku bar wajen a matsayinka na ogan su ka kwasosu ka kawo su gidan giya ga bindigogin ku a k'asa,you guys how you will save urselves idan wasu suka kwashe su..."
"Oga MK wallahi yau ne kadai aka samu matsala please sir am.."
Keep your **fck*mouth shut my friend did I ask u"
"Madugu please kayi shiru kasan halin oga MK idan ba so kake ya kaimu gidan maza ba"

Captain Mk ya k'ara finciko Cpl Riskuwa ya d'aga shi ya koma direshi k'asa ya ce
"Gidan maza yanzu ko za ku koma babu fashi tunda kunce Ku yan iska ne daidai ni ke da ku wanda basu san mutuncin kansu ba, Kai Emma ba dai kaima ka biyewa wannan tsohon banza ba? zaku gane waye *CAPTAIN MUKHATAR Gwandu* tunda ku ba za ku natsu ba"
"Oga sir am sorry i don't do anything wrong, wallahi oga Riskuwa ne yace mu taho nan sir u known me idan naga star bana iya hakuri, am sorry Sir i promise you as from today bazan kara ba please Sir have mercy.....
Cikin fushi zuciya ya katse shi ta hanyar kiran sunan shi "Emma! Emma! How many times did I call ur name"
"Two times sir"
"Ok to za ku tafi inda ku kafi wayo ko Kuma kuna so in nuna mu ku my true colour?
Girgiza kanshi ya yi cikin tsananin tsoro
Ya bud'e bayan motarsa ya jifa Cpl Riskuwa da k'arfi ya fad'a.
Ya koma ya finciko Emma shima da k'arfi ya jifa shi kana ya finciko Sanusi shima ya jefa shi ya rufe qofar motar da k'arfi tamkar zai cire marfin motar.
Ya koma ya kwaso bindigogin su yasa a booth, ya za gayo ya shigo ya sakawa motar key yanda kawai ya bata wuta sai da jama'ar wajen suka tsorata.

*NATIONAL DEFENCE COLLEGE NIGERIA*
Tun daga nesa sojojin bakin get d'in barrack suka hango motar Captain MK da sauri suka mik'e tsaye suna jiran isowarsa, tun kafin ya karaso wajen suka k'ame tamkar an dasasu.
Bai Ko kalle inda suke ba kawai ya danna kan motarsa a cikin barikin direct hanyar quarter guard ya nufa.
Yanda yake gudu da motar haka ya cigaba babu tsayawa duk da kuwa da ababen hawa da ke cikin barrack d'in sai dai su, su kauce masa saboda sanin waye Captain MK.
Wani irin birki ya taka tamkar motar zata fad'i lokaci d'aya ya danna horn.
A hankali na ke tafiya cikin salon tafiya ta mai ban sha'awa da dauk'ar hankali tamkar bana son taka k'asa.
Kallo d'aya za ka yi min ka gano ina cikin kwanciyar hankali.
sanye na ke da hijab d'ina har k'asa fuska ta nad'e da nik'af hannu na d'aya d'auke da alqur'ani izzo sittin.
Na bada bayana ina tafiya kamar ban san yana yi ba...

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 12, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DA BANSAN ASALINTA BAWhere stories live. Discover now